Sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim shekarau ya shirya taron bita ga ƴan social media na gidan sa domin faɗar da su yadda zasu rika tallata sanatan da kuma yadda zasu gujewa yada labaran ƙarya .
Yayin taron sanata Shekarau ya bukaci mahalatta taron da su guji ya da labaran karya koda akan yan hammayya ne ,domin yin karya yana zubar da kimar dan adam.
” ku guji yin kalaman ɓatanci akan kowa saboda duk abun da kayi kai ma za’a yi maka , idan ka ɓata gwani wani, shi wanda ka ɓata gwaninsa shi ma zai ɓata naka gwani ka ga kenan an yi ba’ai ba.” Inji Sanata Shekarau
Sanatan yace kusan shekara guda kenan yana son shirya irin wannan bitar saboda yan social media su dai na yada labaran karya dana ɓatanci domin dai-daita al’amuran.
“Nasan wasun ku zasu yi tunanin an shirya wannan taron ne domin abun da yake faruwa a cikin jam’iyyar mu, to ina so ku wannan taron bashi da alaƙa da wannan matsalar waccan daban wannan daban kuma idan lokacin waccan yayi zamu magana akai.” inji Shekarau
An dai gayyato masana da dama wajen taron domin fadakar da mahalarta taron cikin su har da Daraktan yada labaran sanatan Malam Sule Ya’u Sule.
An haifi Mallam Ibrahim Shekarau ne a ranar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 1955 a unguwar Kurmawa da ke cikin kwaryar birnin Kano.
Mahaifinsa sunansa Alh Sulaiman Usman Giginyu, a gidan su Mallam Ibrahim Shekarau, shine dan Auta, yana da yayye guda uku, daya namiji, biyu mata.
Mahaifin Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, jami’in tsaro ne, yayi aikin dan sanda na tsawon shekaru 35 a tsarin aikin ‘yan doka da aka fara yi tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, ya yi ritaya a shekarar 1965, Allah ya karbi abinsa a shekarar 1979.
A bisa dalilin aikin ‘yan doka, mahaifin Sen Ibrahim Shekarau, Alh Sulaiman Usman ya shaku da marigayi sarkin Kano Alh (Dr) Ado Bayero, a lokacin yana matsayin wakilin ‘yan doka a gaba dayan lardin Kano, kafin a nada shi Sarki.
Amincin mahaifin sa da marigayi sarkin Kano ya sanya Mallam Ibrahim Shekarau ya maida marigayi sarkin Kano Dr Ado Bayero a matsayin Uba a gareshi.
Sen Ibrahim Shekarau ya sami kulawa da cikakkiyar tarbiyyar musulunci daga iyayen sa ba tare da sangartawa da iyayen yanzu ke wa ‘ya’yansu ba, yayi karatun allo tun yana karami har Allah ya azurta shi da sauke Alkurani mai girma.
Yayi karatun firamare a gidan makama daga shekarar 1961 zuwa 1967, daga nan ya shiga makarantar Aminu Kano Commercial College a shekarar 1968 zuwa 1972, ya shiga makarantar jami’ar Ahmadu Bello Zaria daga shekarar 1973 zuwa 1977 inda ya karanci ilimin lissafi hade da tarbiyyar koyarwa.
Sardaunan Kano yayi aikin bautar kasa a karamar hukumar Ekiti dake jihar Imo a wata makarantar mai suna Madonna Boys High School a shekarar 1977 zuwa 1978, yana dawowa gida a ka daukeshi aikin koyarwa inda aka turashi Government Technical College Wudil, bayan shekara daya aka bashi matsayin Senior Master. A shekarar 1979 zuwa 1980 aka yi masa mukamin firinsifal a Government Day Junior Secondary School Hadejia a lokacin yana da shekara 25 da haihuwa.
Bayan shekara uku da yi masa firinsifal sai aka turashi Government College Birnin Kudu, an dawo dashi GSS Gwammaja a shekarar 1986 inda ya share shekara biyu yana tarbiyantar da makarantar GSS Gwammaja.
A shekarar 1988 zuwa 1992 aka turashi zuwa babbar makarantar Rumfa College, wannan makarantar itace a wancan lokaci ake kira Middle School kuma ta kyankyashe daliban Ilimi da su ka mulki Najeriya, kamar irin su Janar Murtala Muhammad, Janar Sani Abacha da Sarkin Kano Ado Bayero.
Mallam Ibrahim Shekarau jajirtaccan mutum ne, kasancewarsa shugaba, wato firinsifal a makarantun Wudi, Hadejia, Birnin Kudu, Gwammaja da Rumfa, bai taba ajiye alli ba, da shi ake shiga aji domin koyawa yara karatu inda yake daukar darussan lissafi da turanci sannan ya gudanar da ayyukan mulki na makarantun.
A shekarar 1993 zuwa 1994 aka nada shi mataimakin darakta a ma’aikatar Ilimi da ke Gidan Murtala, kafin kace kwabo an nada shi a matsayin babban sakatare a lokaci yana da shekara 39 kacal da haihuwa. A shekarar 1994 din dai aka maida shi babban sakatare a ma’aikatar ruwa har zuwa shekarar 1997 inda ka sake dawo da shi ma’aikatar Ilimi karo na biyu a matsayin babban sakataren.
Daga wannan shekara ne sai aka yi masa mai dungurungun, aka kawoshi cibiyar gudanar da gwamnati, wato ofishin sakataren gwamnati, a matsayin babban sakatare mai lura da gudanarwa da sauran aikace-aikace daga shekarar 1997 zuwa 2000. Wannan shine makurar aiki ga duk ma’aikacin gwamnati, Mallam Ibrahim Shekarau ya kure aikin gwamnati bayan shekara 23 da fara aiki.
An dauke Mallam Ibrahim Shekarau daga ofishin sakataren gwamnati wato Cabinet Office zuwa hukumar daukar ma’aikata a matsayin babban sakatare a shekarar 2000, a wannan shekarar ne dai kwatsam sai gwamnatin Kwankwaso ta rage masa matsayi ta dawo dashi malamin aji a sashin koyar da lissafi na makarantar share fagen shiga jami’a ta Kano wato CAS har zuwa 2001
A wannan shekarar 2001 ne Sardaunan Kano ya ajiye aiki bayan ya shafe kusan shekara 30 a aikin gwamnatin, nan take aka dauke shi aiki a Dantata Organisation a matsayin Principal Private Secretary na Alh Aminu Dantata, inda anan ma bai shekara ba ya ajiye aikin kuma ya shiga harkokin siyasa.
Sen Ibrahim Shekarau ya dare kujerar gwamnan Kano karo na farko daga shekarar 2003 zuwa 2007 ya sake dare kujerar gwamnan karo na biyu daga shekarar 2007 zuwa 2011. Mallam Ibrahim Shekarau ya zama Ministan Ilimi a shekarar 2014, yanzu kuma Sanatan Kano ta tsakiya mai ci.
Ga tashoshi masu yada ingantattu kuma sahihan labaran Sen Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) a kasa domin samun labarai da dumi-dumi har ma da wadanda suka shude baku riskesu ba kamar haka;
Sen Ibrahim Shekarau Media, Taskar Masoya Sardaunan Kano, Tsalle Daya
Godiya mai yawa ga DG MIS New Media, Mallam Bello Muhammad Sharada bisa bada ingantattaun bayanai domin shirye-shiryen wadannan tashoshi da sauran masu taimaka mana a wannan directorate, muna taya maigirma Distinguished Senator Mallam Ibrahim Shekarau murna bisa cimma wadannan Shekarau masu albarka.
Allah ya kara lafiya da zaman lafiya, Allah ya kara daukaka, ya karo shekaru masu albarka cikin nutsuwa, lafiya, kwanciyar hankali da imani
Ibrahim Ali Ahmad (Na’Allah Raheemeeb) MIS Director Research and Documentation
Mai girma Sanatan Kano ta tsakiya ya sauka a kasar Tanzania tare da tawagarsa lafiya domin gudanar da wata ziyarar aiki, sun sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Julius Nyerere Darussalam, Tanzania.
Sanata Ibrahim Shekarau ya sami tarbar wakilin Najeriya a Kasar Tanzania Ambassador Hamisu Umar Takalmawa, muna fata Allah ya dawo da su gida lafiya.
LITININ 25 ga watan Oktoba 2021 uwar jam’iyyarmu ta APC ta kasa ta karbi cikakken rahoton kwamitin zabe da aka gudanar na shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano.
An gabatar da wannan zaben shugabanni su 36, a ranar Asabat 16 ga watan Oktoba 2021 a Kano karkashin jagorancin Farfesa Muhammad Sani Bello (Mainan Zazzau) da ‘yan kwamitinsa.
Shugaban kwamitin zaben ya mika rahoton ne ga sakataren mulki na jam’iyya, wanda ya karba, sannan ya buga hatimin APC ya saka hannu. A cikin rahoton kwamitin, Farfesa Sani Bello ya bayyana Ambassada Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin wanda ya lashe wannan zaben da ya jagoranta. Haka kuma Hon. Balarabe Wakili a matsayin sakatare, sai Alhaji Awwalu Ibrahim DanZabuwa a matsayin ma’ajin jamiyya.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da: Barista Halliru Danga Maigari, lauyan jam’iyya na jiha da Basiru Yusuf Shuwaki a matsayin shugaban Matasa, Haruna Muhammad Insha Allahu shi kuma kakakin jam’iyyar APC a Kano. Haka an zabi Aisha Hassan shugabar mata da Abubakar Muhammad Gwarmai a matsayin sakataren kudi na jiha.
Idan za a iya tunawa a sati biyu da ya gabata Babban kwamitin riko na kasa na jam’iyyar APC a bisa umarnin Gwamna Mai Mala Buni ya kafa wani kwamiti mai karfi karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nassarawa domin ya daidaita takaddama da sabani a tsakanin ‘ya’yan APC a jihohin Najeriya, tun kafin a gudanar da zabe. Kwamitin bai fara aikinsa ba aka shiga zabukan wanda Allah ya baiwa Alhaji Ahmadu Haruna Zago a Kano
Siyasarmu addininmu, addininmu siyasarmu, a ta bakin Sanata Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano yayin sake fasalin Majalisar Gudanarwa ta Shura a fadarsa ta Mundubawa ranar Lahadi 4 ga watan Yuli, 2021
Sanata Shekarau yace; na sake dawowa kan dandamalin magana domin karyata wata jita-jita da ke yawo a farfajiyar kafafen sada zumunta, wato social media, inda ake cewa wai zanbar siyasa.
Alamu sun nuna cewa masu yada wannan jita-jita ko dai basu san waye Ibrahim Shekarau ba kokuma sun jahilci siyasarmu kokuma dai suna yi ne domin son zuciyarsu, kuma daga alama sun fito ne daga gidajen masu hamayya da siyasar mu.
Duk wanda yasan menene siyasa, yasan cewa mu’amala ce da hidimtawa al’ummah shine siyasa, kuma shima addinin Allah mu’amala ne da hidimtawa al’ummah, duk wanda ke da sabanin haka, ya jahilci menene siyasa.
Shi kuma rike madafun Iko, daya ne daga rukunnan siyasa, wata kaddarace daga mahalicci, dukkanin mu anan da muke rike da madafun Iko ba wai domin munfi kowa bane, kaddararmu ce, haka Allah ya kaddara mana a tafarkin siyasa.
Amma duk wanda ke tinanin Ibrahim Shekarau zai bar siyasa, kamar yana tinanin zanbar addinin Allah ne, hakan kuma ba mai yiwuwa bane, don haka muna nan a cikin siyasa daram-dam har sai mai riska ta riskemu.
Ba wai mun fito siyasa domin a mutu ko ayi rai ba ne, amma mun fito domin kar a tauye mana yanci, ba zamu zalinci kowa ba, haka kuma ba zamu linke hannayen mu mu zura Ido a zaluncemu ba.
Za muyi kokari wajen zabo mutanen kirki, wadanda za su hidimtawa al’ummah haka kuma za mu kiyaye dokoki, za mu kare akwatuñan mu domin kar a zalincemu.
Mai Girma Malam Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, Tsohon Gwamnan Kano, kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, yana gayyatar Masoya da Magoya baya zuwa wajen kaddamar da Shugabanni na Majalisarsa ta Shawara, wato SHEKARAU SHURA MAJALIS.
Wadda aka FADADA daga matakin Jiha zuwa Shiyoyi Uku (3) na Kano, da Kananan Hukumomi Arba’in da Hudu (44), da Mazabu dari Hudu da Tamanin da Hudu (484).
Za a yi wannan Taro ne a Ranar Lahadi mai zuwa. 4 ga watan Yuli, 2021.
Za a yi Taron da karfe 10 na Safe, a Fadar Mundubawa, Gidan Mai Girma Sardaunan Kano.
Sanarwa daga
Shekarau New Media Communication
A Madadin Dokta Umar Musa Mustapha, Maimansaleta, Shugaban Majalisar Shura ta Jiha.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai Nake Gabatar Muku da Dan Takara ta, Kuma zabin Matasa Hon. Abdullahi Ahmad Tadada A matsayin Shugaban Matasa na Jam’iyar APC ta Jahar Kano (APC Kano State Youth Leader).
A Sanina da Hon. Abdullahi Ahmad Tadada Mutunne Jajirtacce wanda Kullin burinsa Yaciyar da Matasa gaba ta kowane Fanni.
Kuma ya kware a fannin Siyasa dana Zaman takewa, Duba da irin Kungiyoyin da ya Shugabanta ko yakasance acikinsu, hakan yasa yasamu Kwarewa ta gogayya da mutane mabambanta aciki da wajan Jahar Kano.
Duk inda kazaga Ba abinda mutane suke face fatan Alheri ga Hon. Tadada
Duk mai neman Cigaban Jam’iyarmu ta APC yakamata yabawa Hon. Tadada Kuri’arsa Dan Samun Change Alheri A Jahar Kano.
Siyasa ita ce tsanin shugabanci, amma ba kowane kwashi-kwaraf za a rika tura wa su rike madafun iko ba tun daga kansila har zuwa shugaban kasa
Jam’iyyun siyasa, sune ginshikin samar da gwamnati, amma suna hannun da bai kamata ba, kuma sun katange wadanda suka cancanta.
Gyara da samun shugabanni na kwarai dole ya fara daga daidaikun mutane. Wajibi ne a yi ganganmin kiran mutane su shiga jamiyya, su nemi mulki, don kafa al’umma ta gari.
Amma kuma ba za a taba gina al’umma ba sai an koma tafarki da tsarin A Daidaita Sahu. Na dade da fahimtar haka, shi ne ya sanya na kirkiro shirin A DAIDAITA SAHU a Kano lokacin da na samu ragamar jama’ar jihar Kano.
Shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump ya umarci magoya bayansa su hargitsa majalisar dokokin Amurka, don a hana tabbatar da zaben Joe Biden, a zauren majalisa.
Magoya bayan Donald Trump sun dauki “tabarya da muciya, sun haura katanga, sun shiga zauren majalisa ko a Mutu ko A yi rai, kuma har mace guda da ta dauki muciya ta mutu,” an dakatar da zaman majalisa na awanni.
Duk duniya ta yi Allah wadarai da wannan rashin lissafi na Donald Trump. A cikin Amurka ‘yan majalisar kasa sun yi ittifaki a yi gaggawar sauke Trump daga shugaban kasa. ‘Yan kasuwa da manyan masu masana’antu sun ce a kore shi.
Jam’iyyar sa ma ta Republican ta ce ya zama dan ta’adda. Tun tsakiyar dare masu rike da mukami a gwamnatin Trump suke sauka da ritaya.
Lallai mu fahimta kalmomi da shugabanni suke amfani da su ga magoya baya suna da tasirin habaka zaman lafiya da haifar da tashin hankali, sai mu hankalta.
Sen Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) had inspected road works he awarded at Aminu Kano Teaching Hospital AKTH intended to ease the hardship in movements of patients and the staff of the hospital around the premises.
This, has been one of the achievements that Senator Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau had so far brought in the year 2020 that touches the life of people of Kano and beyond.
Distinguished Senator Kano Central Senatorial District Mallam (Dr) Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) inaugurated 6 man Technical Committee on (Constituency Projects).
Members of the Committee as follow : Murtala Yusuf Abdullahi – Chairman Alh.Salisu Indabawa – Member Engr.Bashir I.Bashir – Member Engr. Salisu Magaji – Member Engr. Munir Ahmad Gwarzo – Member Engr. Dayyabu Tijjani – Member/Secretary.
Matukar malam shekarau bai fice daga jikin ganduje ba tofa babu shi ba motsi a siyasar Kano sannan babu wani mutum dazai sake fitowa takara daga mundubawa koda ta kansila saboda yasan ma bazai samu ba.
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce Shugaba Buhari na Najeriya ya karya dokar Najeriya sakamakon ƙin sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya da wa’adinsu ya ƙare tun tuni.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, ya bayyana cewa a kundin tsarin mulkin Najeriya, idan ma’aikaci ya kai shekara 60 da haihuwa ko kuma shekara 35 yana aiki, dole ne ya yi ritaya.
“Shugaban ƙasa bai da ikon ya ƙara wani abu kan abin da doka ta ce,” a cewar Malam Shekarau.
A cikin makon nan ne Majalisar Dattawan Najeriya ta sake buƙatar shugaban ƙasar ya sallami manyan hafsoshin ƙasar, buƙatar ita ce ta biyu cikin watanni shida.
Haka kuma majalisar ta aika goron gayyata ga shugaban ƙasar, shugaban kuma ya karɓi goron.
Sanata Shekarau ɗan jam’iyyar APC ne, daga jihar Kano, jihar da ta fi kowace ruwan ƙuri’u ga Shugaba Buhari.
A madadin jagorori, shugabanni na jiha da kananan hukumomi da mambobi da Sen Ibrahim Shekarau MEDIA da dukkanin masoya Senator Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano.
Kungiyar s4s.home.blogShekarau for Senator Campaign Team.
Muna taya Shugaban mu, jagoran mu na siyasa kuma abin alfaharin mu, Senator Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano murnar cika shekaru 65 da haihuwa.
Babbar kotun daukaka kara ta tarayya dake Kano, a zamanta da tayi a ranar Talata 20/10/2020 ta kori karar da hukumar kula da cin hanci da karbar rashawa EFCC ta shigar inda take tuhumar tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da laifin karbar kudin zaben 2015
Kamar yadda kotu ta bayyana, ta kori karar ne sakamakon gazawar da EFCC tayi na gabatar da cikakkiyar shaida da zata tabbatar an aikata laifin da suke tuhuma.
Daga karshe, gaskiya ta yi halinta, Allah mun gode.
Yanzu, da misalin karfe 8:44 na safiyar Lahadi 11/10/2020 na sami sako daga Director social media a ofishin Sen Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) Mall Bello Muhammad Sharada kamar yadda zaku gani a kasa :-
Aslm Alaikum Sir, Alhamdulillah Ina godiya GA Allah An yi aiki. Ranar Alhamis An yi nasara. Allah ya karbi tawassulinku
Ina godiya gareka da duk abokan arziki. Allah ne kawai zai biyaka.
Ina magana, ina tafiya, Ina cin abinci, Ina hayyacina, ina salla, Ina gane kowa da komai Ina jin sauki. Allah ya amsa duk adduarka.
Ina rokon Allah ya karbi duk ayyukan alheri da kake yi kuma ya baka aljannar Firdaws al’a’ala. Ya tsare gabanka da bayanka, ya tsare duk iyalinka. Allah ya baka nasara akan duk lamarinka.
Ina samun kula a dakin amenity 2 male surgery a AKTH
Bello Muhammad Sharada
A madadina da iyalina da kuma kafafan yada labarai na zamani, mallakina da kuma mallakin kungiyoyin da muke jagoranci, masu alaka da Distinguished Sen Ibrahim Shekarau CON, muna fatan Allah ya karawa Mall Bello Muhammad Sharada lafiya, Allah yasa jinyar da yayi, ta zama kaffara a gareshi.
Daga karshe, duk mai son ya kai masa ziyarar gaisuwa zai iya samunsa a Amenity 2 male surgery a AKTH muna rokon Allah yasa ya fito da karfinsa na gwagwarmaya da tunkarar kalubalen rayuwa fiye da yadda aka sanshi a baya.
Nagode
Ibrahim Ali Ahmad
(Na’Allah Raheemeeb) mawallafin blog da jaridun online kamar haka:-
Wannan gidan yada labarai mai suna a sama na addu’a ga daya daga cikin abokin hulda kuma Director Social Media a fadar Distinguished Sen Ibrahim Shekarau, wato Mallam Bello Muhammad Sharada, wanda ke fama da rashin lafiya kuma za’a yi masa aiki, Allah ya bashi lafiya ya sa kaffara, Allah ya bada sa’a ayi aiki cikin nasara.
Daga karshe, muna addu’a Allah yaba dukkanin musulmi da basu da lafiya sauki da rangwame.
We rejoice and celebrate with the President and the entire Nigerians on this occasion, we pray that Almighty God see us through our entire calamity and Nigeria prosper.
A Safiyar Litinin 21/9/2020. Mai Girma Sardauna Kano Kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau, Ya Ziyarci Masarautar Zazzau, Domin Yin Ta’aziyyar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh Dr Shehu Idris.
Haka Kuma Ya Gabatar Da Ta’aziyyar Sa Ga Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero Da Dukkan Sarakunan Najeriya. Hada Da Al’ummar Masarautar Zazzau.
Mai Girma Sardaunan Kano, Ya Bayyana Marigayin Mai Martaba Sarkin Zazzau, A Matsayin Uba, Shugaba Abun Koyi, Kuma Dattijo, Jajirtacce.
Yayi Addu’ar Allah Ya Jikansa, Ya Gafarta masa, Yasa Aljanna Makomarsa, Ya Bamu Hakurin Rashin Sa.
Distinguished Sen Ibrahim Shekarau in continuation of his best, making consultations with the Northern communities in Edo State all in preparations of the gubernatorial election.
The Northern Nigeria communities lived there endorsed the APC aspirant and were urged by the Distinguished Sen Ibrahim Shekarau CON not to end the endorsement on the table but follow it by action.
He urges them to bring out their various community members on election day to cast their votes to APC.
H.E Most Distinguished Senator Dr Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano (CON) on Friday in a meeting with Northern communities led by Sarkin Hausawan Benin City Edo State Alhaji Adamu Isah Dutse and other leaders of Northern Citizens who are living in Edo State.
A Yau Juma’a Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Kuma Sardaunan Kano Mal Dr Ibrahim Shekarau Ya Tattaunawa Da Kungiyoyi Al’ummar Arewa Mazauna Jihar Edo. Karkashin Shugaban Alh Adamu Isa Dutse Da Sauran Shugabanin Arewa Mazauna Jihar Edo.
Allah Ya Taimaki Sardauna, Jagora Abun Koyi. Duk Wannan A Shirye Shiryen Zaben Gwamnan Jihar Edo Da Za’a Gudanar Ranar Asabar 19/9/2020.
Muna Addu’ar Allah Ya Bawa Jam’iyar A. P. C Nasara.
A Shirye Shiryen Zaben Gwamnan Jihar Edo Da Ake Shirin Gudanarwa a ranar 19/9/2020. Wanda Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR Shine Shugaban Yakin Ciyo Zaben.
Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Kuma Sardaunan Kano Mal Dr Ibrahim Shekarau, Tuni Yayi Gaba Wajen Taya Mai Girma Gwamnan Kano Wannan Aiki, Domin Samun Nasarar Zaben.
A Jiya Mai Girma Sardaunan Kano Kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau, Ya Zauna Da Kwamatin Koli Na Addinin Musulunci Reshen Jihar Edo, Domin Neman Goyon Bayansu A Zabi Jam’iyar A.P.C.
A Ci Gaba Da Shirye shiryen Tunkarar Zaben, Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Kuma Sardaunan Kano Mal Dr Ibrahim Shekarau, Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Jam’iyar A.P.C Na Kasa Comrade Adams Oshomole, A Gidansa.
Muna Addu’ar Allah Ya Taimaki Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR, Allah Ya Taimaki Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Kuma Sardaunan Kano Mal Dr Ibrahim Shekarau.
And they were not divided until after the knowledge came unto them, through rivalry among themselves; and had it not been for a Word that had already gone forth from thy Lord for an appointed term, it surely had been judged between them. And those who were made to inherit the Scripture after them are verily in hopeless doubt concerning it.
The Islamic New Year, also called the Hijri New Year or Arabic New Year, is the day that marks the beginning of a new Hijri year, and is the day on which the year count is incremented. The first day of the Islamic year is observed by Muslims on the first day of the month of Muharram.
Happy Islamic new year 1442AH to all Muslim brothers, sisters followers all over the world.
Ina mana barka da riskar wannan wata mai alfarma. Allah SWT ya sadamu da dukkan alkhairan dake cikin wannan wata, Ya kuma karemu daga dukkan sharri.
Allah Ya bamu ikon yin aiki na gari a cikinsa wanda zai zamo sanadin samun yardar Allah, Rahma, gafara da dukkan alkhairai na duniya da lahira.
Allah Ya sa watan ya zama sanadin kawo karshen wannan annobar da ta addabi duniya baki daya. Allah ya kara mana lafiya da zama lafiya, Ya kuma azurtamu da ganin wadansu watannin Ramadan masu yawa.
You must be logged in to post a comment.