Mutumin da tun sanyin safiya ya zagi sunnah ta Manzo (SAW) ta hanyar zagin gemu da malaman addini na sunnah, ya gangaro ya baci Manzo (SAW) ya sake gangarowa ya tuhumi Allah (SWT) dalilin yin halittarSa ta sauro, kuda da kyankyaso, amma haka mabiyansa suka take masa baya a zuwan daidai yakeyi. Akwai wani abuContinue reading “Kafircin Kwankwasawa A Fili Matukar Basu Tuba ba”
Monthly Archives: May 2019
Ganduje ya amince da sake nada Usman da Shehu
Maigirma zababban gwamnan Kano bayan karbar rantsuwar kama aiki ya amince da sake nada Alhaji Usman Alhaji a matsayin sakataran gwamnati da Shehu Mu’azu a matsayin babban akanta na Jiha.
HIRAR KWANKWASO TA JIYA AKWAI AYAR TAMBAYA..
Ya kamata hukuma tayi bincike domin tantance wasu daga kalaman kwankwaso, domin a hirarsa ta jiya akwai inda yace “daga cikin ‘yan iskan da gwamnati tashigo dasu daga wasu garuruwa sukayi ta’addancin za6en gama har yanzu sunanan basu fita daga kano ba, a yanzu sune suke kidnapping mutane a kano” Wannan kalami a mahanga taContinue reading “HIRAR KWANKWASO TA JIYA AKWAI AYAR TAMBAYA..”
SHEKARAU A FADAR SHUGABAN KASA
A ranar Talata da ta gabata, zababben sanata daga Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau, ya halarci bude baki na azumi a fadar shugaban kasa a Abuja. Mallam Shekarau yana cikin tawagar Majalisar Koli ta addinin Musulunci, Nigeria Supreme Council of Islamic Affairs, a takaice NSCIA, wacce ke karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad SaadContinue reading “SHEKARAU A FADAR SHUGABAN KASA”
Cin Mutuncin Masarautar Kano
Shekaru 5 kenan cif mutane marasa daraja suka ci mutuncin Masarautar Kano. A irin wannan rana 30th May,2014 Marigayi Maimartaba Sarkin Kano ya nada Limamin waje a matsayin wazirin kano Gwamnatin Wannan lokaci ta tura takarda da kausasan kalamai tana umartar Marigayi ya warware Wannan Sarauta. Wannan shine rashin mutunchi na farko da akayi waContinue reading “Cin Mutuncin Masarautar Kano”
GASKIYA AKWAI MATSALA!
Daga Umar Faruq Muhammad Ina matukar takaici da Mamakin irin Usulubin da Tsohon Sanata Kwankwaso ke bi wajen Furta kalamai ga masu sauraren sa. Idan mukayi la’akari zamu fahimci cewa Kwankwaso yana dora magoya bayan sa ne a gwadaben siyasar Kiyayya da cin Mutuncin abokan hamayyar sa. In mukayi duba na tsanaki zamu ga yaddaContinue reading “GASKIYA AKWAI MATSALA!”
Labarai cikin hotuna
Alhamdulillah Masha Allah! Laraba 29/5/2019 An rantsar da zababban gwamnan Kano tare da mataimakinsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Dr Nasir Yusuf Gawuna kamar yadda zakugani cikin hotuna. Allah yayi riko da hannayenku, yabaku ikon sauke nayin da ya mataya a wuyanku zuwa shekaru hudu masu zuwa, Allah yasa damu za’ayi
Oyoyo Baba
Asabar20 Ga RamadanBARKA DA SAUKA BABANMUMai Girma Zababben Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Ya dawo daga Kasar Saudiya bayan kammala Ibadar Umarah .Allah ya amshi Ibadah .
ABUBUWA 5 MASU MUHIMMANCI A 10 KARSHE NA RAMADAN
Assalamu alaikum warahmatullah wabaraktuhu ! Kashi 2 bisa 3 na kwanakin Azumi sun wuce, Muslmai yanzu suna cikin kwanakin 9 ko 10 karshe na Azumin bana shekara ta 1440 bayan Hijira, ya danganata da kwanakin da watan zai yi, 29 ko 30. Kwana 10 karshe na wannan wata mai tsarki yana da muhummanci sosai daContinue reading “ABUBUWA 5 MASU MUHIMMANCI A 10 KARSHE NA RAMADAN”
Kowa Ya Tsuke Bakinsa
Zuwa ga duk wani hadimin Sanata Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano da majalisar Mundubawa dake mazabar Panshekara karkashin Ibrahim Ali Ina kira ga kowa ya tsuke bakinsa 😷 bisa yanayin da muke ciki a mazabar ta Panshekara, mun saurari korafe-korafen ku, dangane da tafiyar siyasar mu, kowa yayi hakuri da irin yadda muka tsinci kanmuContinue reading “Kowa Ya Tsuke Bakinsa”
SAKON JAJE GA H.E NASIR MUHAMMAD SORON
SAKON JAJE DA DUBIYA GA H.E NASIR MUHAMMAD SORON DINKI DAGA #S4S. A madadin jagorori da Exco #S4S na jiha karkashin Abdullahi Ahmad Tadada da dukkannin Co-ordinators na kananan hukumomi da kuma membobinta muke amfani da wannan dama domin mika sakon jaje da dubiya ga H.E Nasir Muhammad Soron Dinki da iyalansa da kuma dukkanninContinue reading “SAKON JAJE GA H.E NASIR MUHAMMAD SORON”
Sakon Ta’aziyya
Amadadin jama,ar Gwale da dukkanin Shugabanni da Coordinators na Jiha na S4S munayiwa maigirma jagorar mu kuma shugaban Shekarau 4 Senator Abdullahi Ashamed Tadada Ta,aziyar rasuwan Dan kanwar shi. Da Allah yakarbi abunshi bayan yasha fama da jinya Allah yajikanshi da rahama yabawa yan’uwa da iyaye juriyar wanan rashin dasukai Idan tamu tazo Allah yasaContinue reading “Sakon Ta’aziyya”
Hukumar Hisbah Ta Damke Gandaye A Kano
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gandaye 80 a gurare daban-daban a birnin Kano da kewaye sakamakon cin abinci da rana a wannan lokaci na azumi. Kamar yadda kakakin hukumar Mallam Adamu Yahaya ya bayyana wa manema labarai cewa, dukkanin wadanda hukumar ta damke musulmi ne babu wanda ba musulmi ba, saboda sune azumiContinue reading “Hukumar Hisbah Ta Damke Gandaye A Kano”
AKWAI ALFANU CIKIN KARIN MASARAUTU
Fahimtar Al-Ikhwany Jihar Kano Jiha ce datake da Kananan Hukumomi 44, daga cikin 44n nan guda 8 ne kadai suke cikin Kwaryar Birni,Guda 36 kuwa suna Karkara. Idan mukayi Nazari zamuga Gwamnonin da Kano tayi tun daga 99 zuwa 2019 manyan Ayyukan su sukan tsaya ne a Iya Kananan Hukumomin da basu wuce 4 zuwaContinue reading “AKWAI ALFANU CIKIN KARIN MASARAUTU”
An Sami Raguwar Hada-Hada A Fadar Mai Martaba Sarki Sunusi II
Fadar mai martaba Sarki Sunusi Lamido Sunusi II dake kwaryar birnin Kano ta sami raguwar hada-hadar zirga zirgar jama’a da motoci da ma fadawa kamar yadda wata jarida ta ruwaito. Wannan baya rasa nasaba da kara kirkiro wasu sabbin masarautu guda hudu da gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tayi, kamar yadda labarai sukaContinue reading “An Sami Raguwar Hada-Hada A Fadar Mai Martaba Sarki Sunusi II”
Sakon Ta’aziyya Ga Musa Sanka
SAKON TA’AZIYYA GA DAN’UWA ABOKIN GWAGWARMAYA MUSA SANKA DAGA #S4S. A madadin jagororin #S4S da shugabanninta na jiha karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada da kuma sauran dukkannin membobinta muke mika sakon ta’aziyyarmu ga dan’uwa abokin gwagwarmaya Musa Sanka bisa rasuwar mahaifiyarsa wadda Allah ya yiwa rasuwa a yau Litinin a jihar Kaduna. Da fata daContinue reading “Sakon Ta’aziyya Ga Musa Sanka”
Sauka Lafiya Sardauna
A daidai lokacin da ya fito daga fadarsa ta Mundubawa akan hanyarsa ta filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano inda zai nufi kasa mai tsarki domin gudanar da aikin umarah. Zababben Sanatan Kano ta tsakiya Mallam Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano, kamar kowane lokaci idan zai fita yakan tsaya domin yinContinue reading “Sauka Lafiya Sardauna”
Majalisar Dokoki Ta Jihar Kano Tayi Zaman Gaggawa
Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano Zatayi Dokar Fadada Masarautar Kano Inda Zata Maida Tsarin Sarakunan Yanka. Wasu Lauyoyi Sunnemi Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano Datayi Dokar Dawo da Darajar Sarakunan yanka Na Jahar Wanda Kowanne Sarki Dajarsa Daya Da Sarkin Kano. Masarautun Sune Kamar Haka. Masarautar Rano Masarautar Gaya Masarautar Karaye Masarautar Bichi . AzamantaContinue reading “Majalisar Dokoki Ta Jihar Kano Tayi Zaman Gaggawa”
Za’a yiwa hukumar Hisbah garanbawul – Ganduje
Gwamnatin Jihar Kano zata yiwa hukumar Hisbah garanbawul inji Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Ganduje yace, kamata yayi hukumar ta Hisbah tayi aiki akan jagorancin hukunce-hukuncen Qura’an da Sunnah kamar yadda aka kafata bawai jagoranci akan ra’ayin wasu mutane ba. Wannan ya biyo bayan kokarin yin dokokin da zasu shafi tafiyar da iyali a wannanContinue reading “Za’a yiwa hukumar Hisbah garanbawul – Ganduje”
SAKON BARKA DA SHIGOWAR AZUMIN WATAN RAMADAN MAI ALBARKA DAGA #S4S.
A madadin jagororin tafiyar #S4S da shugabanninta na jiha dana kananan hukumomi da membobinta muke amfani da wannan dama domin mika sakon murnar shigowar Azumin watan Ramadan ga dukkannin yan’uwa musulmi . Da fatan Allah yasa mu dace yasa muna daga cikin wayanda Allah yake yantawa a wannan wata mai albarka. Allah ya jikan iyayenmuContinue reading “SAKON BARKA DA SHIGOWAR AZUMIN WATAN RAMADAN MAI ALBARKA DAGA #S4S.”
Marasa kishin Najeriya na neman kawo cikas ga bikin sake rantsar da Buhari -Inji Sojoji
Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya ta bayyana cewa akwai marasa kishin Najeriya da ke kulle-kullen tuggu tare da wasu ’yan kasashen waje, domin su kawo cikas ga bikin sake rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 Ga Mayu. Sanarwar ta ce su na kokarin yin haka ne domin su gurgunta tafarkin dimokradiyya a Najeriya. KakakinContinue reading “Marasa kishin Najeriya na neman kawo cikas ga bikin sake rantsar da Buhari -Inji Sojoji”
Gwamna Ganduje Zai Aurar Da Mata 1,500
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR zata aurar da mata 1,500 a yau Asabar 4/5/2019 inda aka zabosu daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano. A cewar mai yada labarai da yawun gwamna Ganduje Abba Anwar za’a bawa kowane ango kayan sawa na shadda da sadakin #20,000 ita kuma amarya za’aContinue reading “Gwamna Ganduje Zai Aurar Da Mata 1,500”
Sanarwar Nesanta Kai
Wannan shafi yana nesanta kansa daga buga duk wani nau’in labari da yawun Maigirma Sanata Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano, haka nan duk wata hulda da aka kulla ko akeyi da wannan shafi bata da wata alaka ta kai tsaye da yawun sa. Wannan shafi dai kawai wata kafar sadarwa ce da take goyon bayanContinue reading “Sanarwar Nesanta Kai”
Kai Tsaye Daga Fadar Mundubawa
Kungiyar Benue youth Initiative sun karrama zabbaben gwamnan kano Karo 2 Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon gwamna Kano karo 2 kuma zabbaben sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau yanzu haka a fadar mundubawa.
Jihar Kano Ta Sauke Manyan Sakatarori A Kowacce Ma’aikatar Jihar
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje a cigaba da tsaftace ayyukan gwamnati da kara karkashin aikin da ma’aikata, ta sauke dukkanin manyan sakatarori na kowace ma’aikata (Perm Sec) Wannan ya fito daga bakin shugaban ma’aikata na Jihar Kano Auwalu Na’iya, inda zasu mika ragamar aiki ga babban darakta na kowacce ma’aikata dagaContinue reading “Jihar Kano Ta Sauke Manyan Sakatarori A Kowacce Ma’aikatar Jihar”
Labarai Daga Fadar Mundubawa
Maigirma gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon Mataimakin gwamna Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da sauran jami’an gwamnati sun ziyarci Maigirma Zababben sanatan Kano ta tsakiya Distinguish Senator Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano a fadarsa ta mundubawa yanzu haka.
Sanata Ibrahim Shekarau Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Hada Hannu Da Buhari A Cigar Da Najeriya Gaba
Zababben Sanatan Kano ta tsakiya a zaben da ya gabata Sen. Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano ya bukaci wadanda suka fadi zabe su ajiye banbance-banbancensu su hada hannau da shugaba Buhari domin cigar da Najeriya gaba. Sanata Ibrahim Shekarau yace, duk da kalubale da soke-soke da gwamnatin Buhari take samu, wannan bai hana samar daContinue reading “Sanata Ibrahim Shekarau Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Hada Hannu Da Buhari A Cigar Da Najeriya Gaba”
Shedar Karatun HND Da Bsc A Hukumar Ma’aikatan Jihar Kano Daidai Take
Maigirma gwamna Abdullahi Umar Ganduje a bikin zagayowar ranar ma’aikata ta 2019 yace, daga yanzu babu banbanci tsakanin masu rike da takarar shedar karatu ta HND da Bsc a kowane fannin aiki a Jihar Kano. Ko shakka babu, kwakwalwar Maigirma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje nesa take da sauran, ma’aikatan Jihar Kano suna godiya.
MA’AIKATA SUNE GINSHIKIN GUDANAR DA MULKI
Gaisuwa Ta Musamman Gareku Ma’aikata Yau rana ce da aka ware domin duk jinsin ma’aikata. Rana ce ta duniya, wacce manufarta shi ne a nuna muhimmancin gudunmawa da ma’aikata suke bayarwa wajen gudanar da mulki don inganta rayuwar al’umma Ina taya ku murnar shagulgulan zagayowar wannan rana, wacce ta zo daidai da lokacin da majalisarContinue reading “MA’AIKATA SUNE GINSHIKIN GUDANAR DA MULKI”

You must be logged in to post a comment.