Yau Allah ya karbi Rayuwar Sahal Usman Adam

April, 27 @14:42

Yan uwa haryanzu dai ina bukatar addu arku na rabu da zazzabi yanzu kuma olsa mai zafice takamani ina cikin wani hali idan kuma ciwan bana tashi bane to Allah yasa muyi kyakykyawan karshe – Sahal Usman Adam

Muna da son zuciya

Ra’ayin Hassan Sani Gidan Fulani

Lokacin da ja’afar ja’afar yake tata tsiyarsa akan faifan video dukda cewa karya ce dan Allah kaf fadin kano da nigeria waye yafito yabashi hakuri, kokuma yace ayi musu sulhu? Kowa murna yake za’akama tirqeqen 6arawo, karshe ma da majalisa tace zatai bincike cewa akayi wai ba huruminta bane, akwai wani lauya daga tsallaken kano dakuma wani dan jarida daga nan kano babu irin budirin da basuyi ba wajen rura wutar wannan al’amari,

Amma yanzu ko kunya babu sune a gaba gaba wajen nuna rashin jindadinsu dangane da bincike da ake cewa za’ayi akan na cikin birni, haka suma dayawa daga masu murnar faifan video yanzu kuma sune suke adawa da bincike na cikin birnin.
Bamu saniba ko saboda shi tasa satar musulma ce???

Duk Wannan Lokacin Babu Wanda Ya Ja Hankalin Sarki?

Ra’ayin Sharhabil Ismail
Lokacin da Sanusi lamido Sanusi II Yake yin taro da baffa Bichi da kwankwaso akan yadda za’a kifar da Ganduje da Buhari da Kuma APC ba ku tsawatar wa Sanusi lamido Sanusi ba
Sanusi lamido Sanusi ya kasance jagoran kamfen din Atiku, kwankwaso, Abba Kabir Yusuf da PDP a Arewacin Nigeria.
Domin fadawansa sun shaidawa fadar shugaban kasa cewar, shi sarki da kansa ya dinga raba kudin kayar da APC, Buhari da Ganduje, Kuma ya tattara wasu manyan Yan kasuwar jihar Kano cewa su tabbatar an Kada APC , har sarki da baffa Bichi suka samo wani shiri Wanda aka dinga aikatawa agidan baffa Bichi cikin BUK, Duk a wancan lokacin babu Wanda ya ja hankalin Sanusi lamido Sanusi daga halayen sa duk da cewa ya zama Sarki ta karkacecciyar hanya.@Dotsa

Allahu Akbar!

6/6/2014 – 6/6/2019

Marigayi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya cika shekaru biyar (5) da komawa ga mahaliccinmu.

Muna addu’a Allah SWT ya jaddada rahama a gareshi ya kyautata bayanshi.

An soke hawan Nassarawa

Sanarwar da muka samu daga ofishin kwamishinan ayyuka na masamman ta bakin babban sakataren ofishin cewa an soke hawan Nassarawa da aka saba yi a kowace rana ta uku da gudanar da bukukuwan sallah sakamakon wasu ayyuka muhimmai da suka taso.

Allah yabamu lafiya da zama lafiya.

Breaking news …

Maigirma zababben Sanatan Kano ta tsakiya Dr Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano yana hakurkurtar da magoya bayansa ba sai sunje Abuja wajen rantsuwa ba duba da inda yanayi yake ba kowa ake bari ya shiga wajen rantsuwar ba, ba budadden waje bane kamar yadda aka yi rantsuwar Shugaban kasa dana Gwamnoni, wanda yake kallo a TV sai yafi wanda yaje wajen ganin komai . Don haka yace ayi addu’a idan ya dawo azo taya murna.

Sardaunan Kano a Masallacin Eid

Sardaunan Kano, Sanata Ibrahim Shrkarau CON ke karbar gaisuwa daga dan takarar gwmnan Kano na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata na shekarar 2019 Abba Kabir Yusuf a filin masallacin eid.

Allah ya karbi ibadar mu ya maimaita mana ta badin badada cikin koshin lafiya.

Kafircin Kwankwasawa A Fili Matukar Basu Tuba ba

Mutumin da tun sanyin safiya ya zagi sunnah ta Manzo (SAW) ta hanyar zagin gemu da malaman addini na sunnah, ya gangaro ya baci Manzo (SAW) ya sake gangarowa ya tuhumi Allah (SWT) dalilin yin halittarSa ta sauro, kuda da kyankyaso, amma haka mabiyansa suka take masa baya a zuwan daidai yakeyi.

Akwai wani abu da zai aibata kayi mamaki?
Ko akwai wani yaronsa dazai baka mamakin goya masa baya wajen aiwatar da wata sabuwar tabargazar da yayi?

Ku gaggauta tuba ga Allah (SWT) kafin lokaci ya kure muku

Ganduje ya amince da sake nada Usman da Shehu

Maigirma zababban gwamnan Kano bayan karbar rantsuwar kama aiki ya amince da sake nada Alhaji Usman Alhaji a matsayin sakataran gwamnati da Shehu Mu’azu a matsayin babban akanta na Jiha.

HIRAR KWANKWASO TA JIYA AKWAI AYAR TAMBAYA..

Ya kamata hukuma tayi bincike domin tantance wasu daga kalaman kwankwaso, domin a hirarsa ta jiya akwai inda yace “daga cikin ‘yan iskan da gwamnati tashigo dasu daga wasu garuruwa sukayi ta’addancin za6en gama har yanzu sunanan basu fita daga kano ba, a yanzu sune suke kidnapping mutane a kano”

Wannan kalami a mahanga ta tsaro ba karamin abu bane, don haka inna kira da gwamnati da hukumomin tsaro lallai sudauki kwakkwaran matakin da ya dace, musamman shi wanda yayi wannan furuci akwai yiwuwar yasan wani abu a harkar kidnapping dinnan, don haka hukuma gakinan gashi, sakaci ba naki bane,

Allah yabamu lafiya da zama lafiya a jihohinmu da kasarmu baki daya..

SHEKARAU A FADAR SHUGABAN KASA

A ranar Talata da ta gabata, zababben sanata daga Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau, ya halarci bude baki na azumi a fadar shugaban kasa a Abuja.

Mallam Shekarau yana cikin tawagar Majalisar Koli ta addinin Musulunci, Nigeria Supreme Council of Islamic Affairs, a takaice NSCIA, wacce ke karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Saad da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyace su.

A wannan hoton wanda aka dauke a dakin tarbar baki na shugaban kasa, mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II na Kano ne, tare da shehin malami Farfesa Shehu Ahmed Galadanci da Mallam Muzammil Sani Hanga, a tsakiyarsu kuma Mallam Shekarau ne.

An dade da sanya Mallam Shekarau a cikin wannan majalisa ta koli ta NSCIA wacce ta hada sarakai da manyan malamai, saboda hidimar da ya yi ga addinin Musulunci abin misali a duk fadin Najeriya

Cin Mutuncin Masarautar Kano

Shekaru 5 kenan cif mutane marasa daraja suka ci mutuncin Masarautar Kano.

A irin wannan rana 30th May,2014 Marigayi Maimartaba Sarkin Kano ya nada Limamin waje a matsayin wazirin kano Gwamnatin Wannan lokaci ta tura takarda da kausasan kalamai tana umartar Marigayi ya warware Wannan Sarauta. Wannan shine rashin mutunchi na farko da akayi wa Maimartaba a tsawon shekaru fiye da 50 da yayi yana mulkin Kano.

Allah ya jikan sa ya gafarta masa. Ya Allah ka kara nesanta mutane marasa daraja daga jagoranci a kano.

GASKIYA AKWAI MATSALA!

Daga Umar Faruq Muhammad

Ina matukar takaici da Mamakin irin Usulubin da Tsohon Sanata Kwankwaso ke bi wajen Furta kalamai ga masu sauraren sa.

Idan mukayi la’akari zamu fahimci cewa Kwankwaso yana dora magoya bayan sa ne a gwadaben siyasar Kiyayya da cin Mutuncin abokan hamayyar sa.

In mukayi duba na tsanaki zamu ga yadda Kwankwasawa ke kausasa harshe ga duk wanda yasabawa tunanin siyasar Jagoran su, hakan yanada nasaba da yadda Madugun yake Dora su a duk sanda zaiyi zance kan abokan Hamayyar sa.

Magana ta gaskiya babu Kamala irin ta Bahaushe balle koyarwar Addini a irin tsarin kausasa harshe da Madugun ke bi.

Lamarin yana koyarda Fitsara tare da rashin kunya ga yara ‘Yan kasa da shekaru 30, kai harma da wadanda suka haura wadannan shekarun.

Kiri-kiri zakaga Yaro yagayawa sa’an Kakansa kalmar da ko sa’an sa a tarbiyyance cin mutunci ne yafada masa.

Sukuma Yan Jarida yakamata su dauki matakin gyara, ko dai su dinga ankarar da Kwankwaso game da hakkin tausasa harshe ko kuma su dena Live program dashi.

Siyasa ba Kiyayya bace ko gaba, amma shi kullum a haka yake dora Magoya bayan sa.

Labarai cikin hotuna

Alhamdulillah Masha Allah!

Laraba 29/5/2019

An rantsar da zababban gwamnan Kano tare da mataimakinsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Dr Nasir Yusuf Gawuna kamar yadda zakugani cikin hotuna.

Allah yayi riko da hannayenku, yabaku ikon sauke nayin da ya mataya a wuyanku zuwa shekaru hudu masu zuwa, Allah yasa damu za’ayi

Oyoyo Baba

Asabar
20 Ga Ramadan
BARKA DA SAUKA BABANMU
Mai Girma Zababben Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Ya dawo daga Kasar Saudiya bayan kammala Ibadar Umarah .
Allah ya amshi Ibadah .

ABUBUWA 5 MASU MUHIMMANCI A 10 KARSHE NA RAMADAN

Assalamu alaikum warahmatullah wabaraktuhu ! Kashi 2 bisa 3 na kwanakin Azumi sun wuce, Muslmai yanzu suna cikin kwanakin 9 ko 10 karshe na Azumin bana shekara ta 1440 bayan Hijira, ya danganata da kwanakin da watan zai yi, 29 ko 30. Kwana 10 karshe na wannan wata mai tsarki yana da muhummanci sosai da sosai.

Hakan na nuni ga cewa duk Muslmin da ya gudanar da Azumin sa cikin kiyaye dukkanin ka’idodin da aka gindaya mai to ya kamata ya zage damtse domin ya ribaci gagarumar riba a wadannan kawanki 10 na karshe.

Daya daga cikin dalilan da yasa aka fi bada Muhimmanci a kan goman karshe shine daren Lailatul Qadari ta kan fado ne a cikin wadannan kwanaki na watan Ramadana.

1:-Ka kara kaimi a karanta Al-Qur’ani:-

*Idan ya kasance Musulmi ya kan karanta shafi 10 zuwa 30 na Qur’ani mai tsraki ne a kowane rana, toh ya dage ya kara daga shafi 30 zuwa 80 har ma 100. Dalili kuwa shine gwargwadon karatunsa gwargwadon ladan sa. Bugu da kari ma, a wadannan kwanaki 10 ne aka saukar da Al-Qur’ani.

2- Sallah Tahajjud:-

*Sallar Tahajjudi wata Sallace da akeyinta a tsakiyar dare idan an farka barci, ya kamata aba wannan Sallar muhimmanci. Idan da kana yin raka’o’I hudu ne a Tahajjud, to ka dage ka ninka shi zuwa 8 ko sama da haka. Kada a manta, ita Sallar Tahajjud ana yin ta ne
biyu biyu kamar 2, 4, 6, 8, 10. 12, haka dai.

3-Yawaita Addu’a:-

*Musulmi ya dage da yawaita yi da kuma maimaita Addu’ar da Annabi ya umarci Musulmai su yi, itace
“Allahumma Innaka Afuwwun, Tuhibbul Afwa, Fa’afu Anna”
Addu’ar tana nufin “Ya Allah, Kai ne mai
gafara, Kana kaunar yin gafara, Ka gafarta
mini”. Ana so Musulmi ya yawaita maimaita wannan Addu’an Safe, Rana da Daddare.

4-I’itikafi:-

*I’itikafi na nufin tarewa a Masallaci na tsawon wasu kwanaki da nufin bautan Allah sosai da sosai. An so idan ma za’a samu dama, toh a kwashe gaba daya kwanaki 9 ko 10 duka a cikin Masallaci. Amma idan misali hidimar yau da gobe ba zasu bari Mutum ya tare gaba daya kwanaki 10, toh zai iya raya dararen
wadannan kwanakin.

5-Sadaka:-

*Sadaka ta kunshi ciyar da Miskinai da masu karamin karfi, bayar ma Mutane kyautan kudi, ko kuma ka kashe kudi wurin yi ma Addini hidima, kamar gyaran Masallaci da sauran su.

Allah yasa mu dace ya karbi ibadun mu baki Daya.

Ibrahim Shekarau
(Sardaunan Kano)

Kowa Ya Tsuke Bakinsa

Zuwa ga duk wani hadimin Sanata Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano da majalisar Mundubawa dake mazabar Panshekara karkashin Ibrahim Ali

Ina kira ga kowa ya tsuke bakinsa 😷 bisa yanayin da muke ciki a mazabar ta Panshekara, mun saurari korafe-korafen ku, dangane da tafiyar siyasar mu, kowa yayi hakuri da irin yadda muka tsinci kanmu kafin lokacin da Allah zaisa mu taka tsandauri.

Allah ya albarkaci wannan tafiya, ya karawa Sardauna lafiya, Allah ya karbi ibadunmu, yasa mudace da rahamarSa a wannan watan na Ramadan mai albarka.
Allah ya kara mana lafiya da zaman lafiya.
Nagode.

Signed:
Ibrahim Ali
Coordinator na Sanata Ibrahim Shekarau 2019 mazabar Panshekara kuma Sardaunan Panshekara

SAKON JAJE GA H.E NASIR MUHAMMAD SORON

SAKON JAJE DA DUBIYA GA H.E NASIR MUHAMMAD SORON DINKI DAGA #S4S.

A madadin jagorori da Exco #S4S na jiha karkashin Abdullahi Ahmad Tadada da dukkannin Co-ordinators na kananan hukumomi da kuma membobinta muke amfani da wannan dama domin mika sakon jaje da dubiya ga H.E Nasir Muhammad Soron Dinki da iyalansa da kuma dukkannin masoyansa bisa hadarin mota da ya samu a kan hanyarsa ta Abuja zuwa Kano.

Da fatan Allah (S.W.A) ya kiyaye afkuwar hakan a nan gaba. Wayanda su kaji raunuka kuma Allah ya basu lafiya yasa kaffara ne. Allah ya kara kiyaye mu daga dukkannin wani sharri. Allah ya kara mana lafiya da zaman lafiya. Allah kuma ya kar6i dukkannin ibadunmu, yasa muna daga cikin wayanda Allah yake yantawa a wannan wata mai albarka.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S,
19/5/2019.

Sakon Ta’aziyya

Amadadin jama,ar Gwale da dukkanin Shugabanni da Coordinators na Jiha na S4S munayiwa maigirma jagorar mu kuma shugaban Shekarau 4 Senator

Abdullahi Ashamed Tadada

Ta,aziyar rasuwan Dan kanwar shi. Da Allah yakarbi abunshi bayan yasha fama da jinya Allah yajikanshi da rahama yabawa yan’uwa da iyaye juriyar wanan rashin dasukai

Idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani ga Lambar wayar shugaban S4S na jiha domin masu bukatar ta,aziya gareshi
08036030497

Yusuf Ibrahim mandawari coordinator S4S Gwale. Social media

Hukumar Hisbah Ta Damke Gandaye A Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gandaye 80 a gurare daban-daban a birnin Kano da kewaye sakamakon cin abinci da rana a wannan lokaci na azumi.

Kamar yadda kakakin hukumar Mallam Adamu Yahaya ya bayyana wa manema labarai cewa, dukkanin wadanda hukumar ta damke musulmi ne babu wanda ba musulmi ba, saboda sune azumi ya wajaba a kansu.

Gandayen sunyi wa hukumar bayanin cewa, wasunsu rashin lafiya ne dalilinsu na cin abinci da rana a cikin azumi, inda wasu ke cewa, rashin ganin wata ne ya jawo basuyi azumin ba.

Tuni hukumar ta sakesu sakamakon wannan shine karon farko da ta samesu da laifi tare da gargadin kada su bari a kamasu karo na biyu, duk wanda aka sake kamawa cikinku zata mikashi gaban alkali manta sabo.

AKWAI ALFANU CIKIN KARIN MASARAUTU

Fahimtar Al-Ikhwany

Jihar Kano Jiha ce datake da Kananan Hukumomi 44, daga cikin 44n nan guda 8 ne kadai suke cikin Kwaryar Birni,Guda 36 kuwa suna Karkara.

Idan mukayi Nazari zamuga Gwamnonin da Kano tayi tun daga 99 zuwa 2019 manyan Ayyukan su sukan tsaya ne a Iya Kananan Hukumomin da basu wuce 4 zuwa 5 ba cikin 8 din dake Birni.

Duk da ina cikin Mutanen dasuke da ra’ayin cigaba da kasancewar Masarautar Kano a waje daya hakan bazai sa in kasa hango Alfanun karuwar Masarautun ba.

A Fahimtata karuwar Masarautu (emirates) zai taimaka wajen Jan hankalin kowanne Gwamna wajen raba manyan Ayyuka a kowacce Masarauta, hakan zai taimaka sosai wajen bunkasar bangarori biyar na Masarautun Kano.

Idan muka Kalli Kazaure a tsohuwar Kano dakuma Kazaure a Jigawa zamu gamsu cewa Kazaure tasamu bunkasa sakamakon Ayyuka da Gwamnonin Jigawa ke rabawa Emirates Jihar.

In sha Allahu nan da Shekaru 10 sai kaga Bichi, Gaya, Rano da Karaye sun samu habaka sakamakon zamowar su manyan Masarautu.

An Sami Raguwar Hada-Hada A Fadar Mai Martaba Sarki Sunusi II

Fadar mai martaba Sarki Sunusi Lamido Sunusi II dake kwaryar birnin Kano ta sami raguwar hada-hadar zirga zirgar jama’a da motoci da ma fadawa kamar yadda wata jarida ta ruwaito.

Wannan baya rasa nasaba da kara kirkiro wasu sabbin masarautu guda hudu da gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tayi, kamar yadda labarai suka tabbatar, dayawa daga hadiman masarautar sunyi gudun hijira zuwa wajen sabon Sarkin Bichi mai martaba Aminu Ado Bayero.

Shima kansa Sarki Sunusi Lamido Sunusi II tun bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi an fahimci ya ja bakinsa ya tsuke duk da kokarin da manema labarai ke yi na ganawa dashi domin jin ta bakinsa.

Sakon Ta’aziyya Ga Musa Sanka

SAKON TA’AZIYYA GA DAN’UWA ABOKIN GWAGWARMAYA MUSA SANKA DAGA #S4S.

A madadin jagororin #S4S da shugabanninta na jiha karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada da kuma sauran dukkannin membobinta muke mika sakon ta’aziyyarmu ga dan’uwa abokin gwagwarmaya Musa Sanka bisa rasuwar mahaifiyarsa wadda Allah ya yiwa rasuwa a yau Litinin a jihar Kaduna.

Da fata da kuma addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata ya yafe mata kurakuranta ya sada ta da Annabin Rahama (S.A.W). Allah ya jikan dukkannin sauran yan’uwa musulmi da suka rigamu gidan gaskiya tin daga lokacin Annabi Adamu (A.S) zuwa yanzu. Mu kuma idan tamu tazo yasa mu cika da imani.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S,
13/5/2019.

Sauka Lafiya Sardauna

A daidai lokacin da ya fito daga fadarsa ta Mundubawa akan hanyarsa ta filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano inda zai nufi kasa mai tsarki domin gudanar da aikin umarah.

Zababben Sanatan Kano ta tsakiya Mallam Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano, kamar kowane lokaci idan zai fita yakan tsaya domin yin addu’a ta neman kiyayewar Allah SWT.

Muna rokon Allah ya sauke ka lafiya Baba, ya dawo dakai gidanka lafiya.

Majalisar Dokoki Ta Jihar Kano Tayi Zaman Gaggawa

Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano Zatayi Dokar Fadada Masarautar Kano Inda Zata Maida Tsarin Sarakunan Yanka.

Wasu Lauyoyi Sunnemi Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano Datayi Dokar Dawo da Darajar Sarakunan yanka Na Jahar Wanda Kowanne Sarki Dajarsa Daya Da Sarkin Kano.

Masarautun Sune Kamar Haka.

Masarautar Rano
Masarautar Gaya
Masarautar Karaye
Masarautar Bichi .

Azamanta Na Yau Yan Majalisun Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Wanan Al’amari.

Kuma Nan Take Majalisa Ta Kafa Kwamitin Dazai Kawo Mata Rahoto A Gobe 7/5/2019.

6/5/2019
Hon Hassan Cikinza Rano
SSA Speaker KNHA.

Za’a yiwa hukumar Hisbah garanbawul – Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano zata yiwa hukumar Hisbah garanbawul inji Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje yace, kamata yayi hukumar ta Hisbah tayi aiki akan jagorancin hukunce-hukuncen Qura’an da Sunnah kamar yadda aka kafata bawai jagoranci akan ra’ayin wasu mutane ba.

Wannan ya biyo bayan kokarin yin dokokin da zasu shafi tafiyar da iyali a wannan Jihar ta Kano, dokokin da zasu yi tasarrufi wajen kulawa da iyali, tafiyar da auratayya tsakanin ma’aurata, rabon gado, hakkin miji akan matarsa da hakkin mace akan mijinta ko da bayan rabuwarsu.

SAKON BARKA DA SHIGOWAR AZUMIN WATAN RAMADAN MAI ALBARKA DAGA #S4S.

A madadin jagororin tafiyar #S4S da shugabanninta na jiha dana kananan hukumomi da membobinta muke amfani da wannan dama domin mika sakon murnar shigowar Azumin watan Ramadan ga dukkannin yan’uwa musulmi . Da fatan Allah yasa mu dace yasa muna daga cikin wayanda Allah yake yantawa a wannan wata mai albarka. Allah ya jikan iyayenmu da kakanninmu da dukkannin yan’uwa musulmi da suka rigamu gidan gaskiya tin daga lokacin Annabi Adamu (A.S) zuwa yanzu. Allah kuma ya kara mana lafiya da zaman lafiya a kasarmu da sauran kasashen yan’uwa musulmi na duniya.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S,
05/5/2019.

Marasa kishin Najeriya na neman kawo cikas ga bikin sake rantsar da Buhari -Inji Sojoji

Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya ta bayyana cewa akwai marasa kishin Najeriya da ke kulle-kullen tuggu tare da wasu ’yan kasashen waje, domin su kawo cikas ga bikin sake rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 Ga Mayu.

Sanarwar ta ce su na kokarin yin haka ne domin su gurgunta tafarkin dimokradiyya a Najeriya.

Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Sagir Musa ne ya bayyana wannan kakkausan bayani a cikin wata takardar da ya fitar ga manema labarai, jiya Asabar.

Musa ya ci gaba da cewa, “wasu marasa kishin kasar nan na shirin su kawo rudani ta hanyar tuggu da kuma kirkiro matsalar tsaro, musamman a cikinnkasar nan kuma wannan bangaren yanki na Afrika ta Yamma.”

Ya kuma kara da cewa wadannan tsiraru na ci gaba da kokarin ganin sun ingiza Boko Haram da mahara sun dumbuza musu kudade da saura kayan da suke bukata.

“Irin munanan kalaman da ke fitowa daga bakunan su, ya nuna suna bada goyon baya ne a fakaice ga mabarnata.

“Misali, wata kwakkwarar majiya ta nuna cewa wasu tsiraru na kulla mummunar alaka da Boko Haram, yayin da wasu kuma kiri-kiri su na kirkirar karairayi ga jami’an tsaro, da nufin haifar da rudani tsakanin sojoji da fararen hula da kuma gwamnati.

“Sannan kuma suna kashe guiwar jami’an tsaro ta hanyar kirkirar labaran karairayi.” Inji Sagir Musa.

Daga nan sai ya ja kunnen su kuma yayi tsokaci a kan cewa idan ba’a daina ba, to abin ba zai yi wa duk wani mai yin haka din dadi ba.

“Akwai kuma wasu daga kasashen waje da ke aiki ba ji ba gani domin haifar da rashin jituwa a tsakanin sojojin Gamayyar Kasa-da-kasa, wato MNJTF, da nufin samar da kafar yadda ISWAP da kuma reshen su na Boko Haram su sake samun gindin zama.

Yayin da ya ce sojoji ba za mu mika kai borin wasu tsirarun batagari ya hau kansu ba, ya kuma ce sojojin Najeriya suna goyon bayan kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen ganin an dakile ta’addanci gaba daya a kasar nan.

A karshe ya ce sojojin Najeriya a ko da yaushe suna masu biyayya ga mulkin dimokradiyya da kuma Gwamnatin Najeriya.

Sun kuma maida hankali domin ganin sun kakkabe ’yan ta’adda da magoya bayan su gaba daya.

Gwamna Ganduje Zai Aurar Da Mata 1,500

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR zata aurar da mata 1,500 a yau Asabar 4/5/2019 inda aka zabosu daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

A cewar mai yada labarai da yawun gwamna Ganduje Abba Anwar za’a bawa kowane ango kayan sawa na shadda da sadakin #20,000 ita kuma amarya za’a yi mata dukkanin kayan daki wadanda suka hada da gado, katifa, kujeru, ledar daki da wajen aje kayayyakin sawa da sauransu.

Ana sa ran gwamnati zata kashe Kudi kimanin naira miliyan talatin (#30m) domin gudanar da wannan hidima.

Sanarwar Nesanta Kai

Wannan shafi yana nesanta kansa daga buga duk wani nau’in labari da yawun Maigirma Sanata Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano, haka nan duk wata hulda da aka kulla ko akeyi da wannan shafi bata da wata alaka ta kai tsaye da yawun sa.

Wannan shafi dai kawai wata kafar sadarwa ce da take goyon bayan sa da tallata manufofin sa da ayyukan sa harma da wasu ayyukan da mukaga sun cancanta mu tallata, matukar basu sabawa dokar kasa ba, bazasu zubarwa da Maigirma Sanata Ibrahim Shekarau mutunci ba, haka bazasu zubarwa da masu buga labaran mutunci ba, kuma bazasu zubarwa da sauran al’ummah mutunci ba.

Don haka a kiyaye!

Mai bugawa
Ibrahim Ali Ahmad
(Na’Allah Raheemeeb)

Design a site like this with WordPress.com
Get started