

Kungiyar Benue youth Initiative sun karrama zabbaben gwamnan kano Karo 2 Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon gwamna Kano karo 2 kuma zabbaben sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau yanzu haka a fadar mundubawa.
s4s.home.blog


Kungiyar Benue youth Initiative sun karrama zabbaben gwamnan kano Karo 2 Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon gwamna Kano karo 2 kuma zabbaben sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau yanzu haka a fadar mundubawa.

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje a cigaba da tsaftace ayyukan gwamnati da kara karkashin aikin da ma’aikata, ta sauke dukkanin manyan sakatarori na kowace ma’aikata (Perm Sec)
Wannan ya fito daga bakin shugaban ma’aikata na Jihar Kano Auwalu Na’iya, inda zasu mika ragamar aiki ga babban darakta na kowacce ma’aikata daga nan zuwa 8/5/2019
Sanarwar tace duk wani darakta da yake akan matakin albashi na 16-17 harma su wadanda aka sauke zasu iya sake neman komawa matukar sun cika sharuddan da gwamnati ta zayyana musu.




Maigirma gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon Mataimakin gwamna Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da sauran jami’an gwamnati sun ziyarci Maigirma Zababben sanatan Kano ta tsakiya Distinguish Senator Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano a fadarsa ta mundubawa yanzu haka.

Zababben Sanatan Kano ta tsakiya a zaben da ya gabata Sen. Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano ya bukaci wadanda suka fadi zabe su ajiye banbance-banbancensu su hada hannau da shugaba Buhari domin cigar da Najeriya gaba.
Sanata Ibrahim Shekarau yace, duk da kalubale da soke-soke da gwamnatin Buhari take samu, wannan bai hana samar da abubuwan cigaba da gwamnatin ta samar ba, kamar yadda yace, shi kalubale yana tartare da duk wani nau’i na cigaba a rayuwa duk da yasan akwai wasu ‘yan majalisar ministocin Buhari da basu tabuka wani abin azi a ganin ba amma wannan bai hana Buharin gudanar da ayyukan ci gaban al’ummah ba.

Maigirma gwamna Abdullahi Umar Ganduje a bikin zagayowar ranar ma’aikata ta 2019 yace, daga yanzu babu banbanci tsakanin masu rike da takarar shedar karatu ta HND da Bsc a kowane fannin aiki a Jihar Kano.
Ko shakka babu, kwakwalwar Maigirma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje nesa take da sauran, ma’aikatan Jihar Kano suna godiya.

Gaisuwa Ta Musamman Gareku Ma’aikata
Yau rana ce da aka ware domin duk jinsin ma’aikata. Rana ce ta duniya, wacce manufarta shi ne a nuna muhimmancin gudunmawa da ma’aikata suke bayarwa wajen gudanar da mulki don inganta rayuwar al’umma
Ina taya ku murnar shagulgulan zagayowar wannan rana, wacce ta zo daidai da lokacin da majalisar dattijai ta sanya wa kasafin kudi na shekarar 2019 hannu. Haka kuma ya zo a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da mafi karancin albashi ya zama naira dubu 30.
Nima tsohon ma’aikaci ne, kuma yanzu dan fansho, na san ciwon duk ma’aikaci. Ina yi muku fatan alheri, tare da roko a gareku kasancewa kune ginshikin tafiyar da mulki, a tsaya a yi aiki gaskiya kuma aikin da aka bamu mu rike shi da amana, mu inganta shi, wannan shi zai karfafi masu mulki don su yi wa jama’a aikin da aka dora musu.
Na samu kaina cikin zababbun sanatoci, ku taya ni addu’a Allah ya yi riko da hannunmu. Insha Allahu zan wakilceku a zauren majalisa a matsayin tsohon ma’aikaci kuma zan wakilci gwamnati a matsayin tsohon gwamna don a samu nasarar walwala da jin dadi irin wanda duk ma’aikata suke samu a ko ina a duniya.
Nagode
Ibrahim Shekarau CON
Sardaunan Kano
![]()
Gwamnatin Kano karkashin maigirma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sa hannu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da Kasar Chaina inda za ta shigo da manyan motocin zirga-zirga a cikin gari.
Wannan ya biyo bayan yadda gwamnatin ke kokarin fito da wata sabuwar hanya ta saukakawa al’ummah a bangaren sufuri, inda a rashin farko za ta shigo da wadannan manyan motoci guda 100 kamar yadda kwamishinan ayyuka da gidaje Aminu Aliyu Wudil wanda ya wakilci gwamna ya bayyana.

ALHAMDULILLAH
Ina Godiya ga Dan majalisarmu Na Tarayya Hon Nasiru Ali Ahmad bisa Gwangwajemu da Sababbin Mashina a karkashin Jagoranchin Director General dinsa Majidadi Rabiu Baba Nabegu.
DG yace kowa sai ya amfana,
Jamilu Away Mai Jakai da Nura Kabaransi Gawuna da Jibril Muhammad Na Tara suna cikin Mutum 50 wadanda suka rabauta da Mashina a Yau.
Na fahimci a Karamar Hukumar Nassarawa kadai ake buga siyasa a Kano, sai Karamar Hukumar Dala da take bi mata.
Haroun Shekaran Gama
Umar Faruq Muhammad
Nafi’u Sale
Sayyada Jidda
Marakisiyya Sani Rano
Allah yakawo babban rabo.

Kungiyar gwamnonin Najeriya wato ‘Nigeria Governors Forum’ NGF ta shirya taron bita na kwana hudu, daga yau zuwa Laraba, wanda aka tsarawa sabbin gwamnonin da suka ci zabe da wadanda zasu maimaita a Abuja na duk jam’iyyun APC da PDP da APGA.
Zababben sanata na Kano ta tsakiya, kuma tsohon gwamna Mallam Ibrahim Shekarau yana cikin manyan malaman da zasu yi wa gwamnoni darasi akan tafiyar da mulki bayan cin zabe.
An gayyaci Mallam Shekarau da kuma wasu manyan jami’ai daga majalisar dinkin duniya da masana daga Turai da Amurka da malaman jami’a da wasu ‘yan siyasa a nan kasar don su bayar da ilimi a tarukan.
Mallam Shekarau ya bar Kano a yau domin halartar wannan bita da za a fara a yau da almuru.
An shirya laccoci da yawa da muhawara a kan batutuwa da yawa.
An saba gayyatar Mallam Shekarau irin wadannan manyan taruka a lokacin da ya rike gwamna da lokacin da ya yi minista saboda gogewarsa a wajen tafiyar da jama’a da mu’amala da irin salon da ya ke amfani a mulki da wanda yake kai na siyasa.
Bello Muhammad Sharada
Director New Media Directorate

Lokacin ina Brigade Special primary school munada Mallamai Kwararru wadanda ba ‘Yan asalin Kano ba, bazan taba mantawa da Form Mistress din mu a Primary 4 ba Malama Mulikat.
A Secondary school dinmu ta GSSS Stadium ma muna da Mallamai Yarabawa, Inyamurai da Kabilun Arewa, ina Alfahari da wani Banufen Mallamin mu mai suna Mallam Hanafi.
Abokan mu dake Makarantar Commercial ta Airport Road suna bamu labarin kwarewar Mr. Augustine wajen koya musu lissafi.
Duk Mutumin Kano yasan cewa a lokacin da ake da irin wadancan Mallaman ana samun nagartacciyar koyarwa, a duk Makaranta zakaga Majorityn Mallaman Kanawa ne, tsiraru ne baki da aka hadu dasu ake sahihiyar koyarwa.
Gwamnatin mu ta 1999 – 2003 datazo sai ta fitar da wani gurgun tsari na korar duk wani Mallamin Makaranta wanda ba Dan Asalin Kano bane.
Abin takaici kuma aka kasa cike gurbin su da asalin Kanawan.
Matukar zaka cire son zuciya zaka gamsu cewa wannan ce Bakar dabarar data fara nakasta ilimi a Jihar Kano.
Zan dora a rubutu nagaba.
Daga Umar Faruq Muhammad

Sakamakon abin da ya faru a Kasuwar Magani, Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da kakaba dokar hana zirga-zirga awa 24 a Karamar Hukumar Kajuru, har sai abin da hali ya yi

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya sauka filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake babban birnin taraiya Abuja bayan dawowar sa daga kasa mai tsarki inda ya gabatar da ibadar sa ta Umrah. Gwamna ya samu tarbar Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sanata Barau Jibrin da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnati.
Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
April 25, 2019.

Maigirma Kwamishinan raya karkara da birane Musa Iliyasu Kwankwaso yayi ikirarin cewa, shine ya jawo tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso cikin harkokin siyasa.
Musa iliyasu Kwankwaso yace, a siyasance ni shugabansa ne, nine kuma na bashi karfin gwuiwa ya tsaya takarar dan majalisar wakilai ta tarayya a lokacin yana aiki a hukumar ruwan sha da gine-gine (WRECA) amma bayan wannan lokacin sai Rabi’u Musa Kwankwaso ya sauka daga layin da muka dorashi.
Tunda Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama gwamnan Kano karo na fari, bai sake gudanar da sahihin zabe a Jihar Kano ba, saidai magudi kawai a zauna a raba yawan kuri’un da yakeso kowane dan takara ya samu.
Ko da a wannan zaben da aka gudanar na baya-bayannan, haka ya debo mutane daga Jihar Kaduna zuwa Karamar Hukumar Madobi domin yin magudin zabe, inda al’ummar garin suka koresu.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar mana cewa, madugun kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya fara korafi akan yadda hulunan Abba Zaman Gida suke yawo a gari ba tare da alamar kwankwasiyya ba.
Nan take madugun yace babu kalmar kwankwasiyya a jikin hulunan, wannan yana nuna an dauko hanyar shafe kalmar ta kwankwasiyya a doron kasa, wato da sun ci zaben ma an daina maganar kwankwasiyya kenan sai “Abba Zaman Gida”
Menene ra’ayinku akan wannan magana?

Daga Umar Faruq Muhammad
Yau duk inda ka karada a social media zakaga Yan Kwankwasiyya suna ta murna da yada Labaran cewa Kotu tace a karbe kujerar Kawu Sumaila ofr saboda bai shiga Primary election ba.
Yada wannan labarin bai nuna komai ba sai cikakkiyar son zuciyar Yan Kwankwasiyya.
A 2015 kowa yasan Kwankwaso takardar takarar Shugaban kasa yasiya bata Sanata ba, kuma zaben fidda Gwani dayayi na Shugaban kasa ne ba sanatan ba.
Abba Kabir dasu Sule Halilu ne suka barje gumi a zaben fidda Gwani, a karshe Abban yayi Nasara, da Kwankwaso yasha kasa a zaben sama sai yadawo tsakiyar Kano yakarbe takarar, da Sule Halilu yayi inkari a kotu sai Kwankwasawa sukace Kiyayya ce da Hassada.
Don Allah mene bambanci tsakanin takarar Kwankwaso ta sanata 2015 data Kawu 2019?
in har ka aminta Kawu ba bisa ka’ida yahau ba to tilas ka yarda haramtacciyar kujera Kwankwaso ya hau a 2015.

Jam’iyyar PDP ta kasa reshen Jihar Kano ta janye zanga-zanga lumana da tayi shirin gudanarwa Alhamis 18/4/2019
Wannan zanga-zanga, kamar yadda Jam’iyyar tace, ta shirya ta ne domin nuna kyama ga yadda jami’an tsaro suke kamawa da kullewa da musgunawa harma da barazana da rayukan magoya bayanta ba tare da aikata wani laifi ba.
Wannan sanarwa da sakataren riko na Jam’iyyar PDP Alh Shehu Wada Sagagi ya sanyawa hannu tace, janyewar ta biyo bayan wani ci gaba da aka samu daga jami’an tsaro na DSS inda suka saki magoya bayanta da suka hada da Salisu Yahaya Hotoro da Babangida Bangis wadanda jami’an tsaro suke tsare dasu batare da aikata laifin komai ba.

Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya bayyana cewa duk da yake Sanata Ali Ndume dan uwan sa ne, dan Jihar sa, ba zai yi wa uwar jam’iyyar APC tawaye ba.

Jam’iyyar APC ta zabi Sanata Ahmed Lawan shi ne zai zama shugaban majalisar dattawa, yayin da Sanata Ndume ya ce bai yarda ba, zai tsaya takara, kuma zabe za a yi ba nadi daga cikin jam’iyya ba.

Bayan mun fadi a zaben 2011 dandanan aka fara bamu kwarin gwiwar cewa muna zuwa kotu za’a kwace kujerar gwamna daga hannun kwankwaso a bawa malam saluhu
Cikin bayanin kwarin gwiwar ne har SHEHU ISA direba yace mun dauko bature mai suna GEORGE WASH FINGER daga America wanda zaiyi aikin gano mutanen da suka yi zabe sama da daya da kuma wadanda suka yi aringizon kuri’u
Haka kuma akace ita alkaliyar wato justice IYABO OLADINI KASALI tana tare da mu domin taga hujjojin mu masu karfi ne.dan haka zata kwace daga hannun kwankwaso ta bamu.
Haka akayi ta lakaba mana igiyar zato, amma ranar da za’a yanke hukunci bayan munyi dafifi muna jiran ace an bamu gwamna sai muka ji ance sai mun bawa kwankwaso naira dubu hamsin na bata lokaci ma bayan an tabbatar masa da nasara
To wannan duban nake yiwa kwankwasawa masu igiyar zato kuma insha Allah sai kunsha takaicin da muka sha a 2011
Daga Sani Adamu Hotoro

Allah yayi wa Galadiman Katsina kuma tsohon ministan shari’a na zamanin Sardauna, Justice Mamman Nasir rasuwa

Sai Gabriel Olonisaki Chief Of Defence Staff yake shaidawa yan jarida cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarcesu dasu aikata dukkan wani kalar rashin tausayin da suke dashi a cikin aikin soja ga Barayin dake kashe mutane tare da sacewa a jihar Zamfara….
Tsantsar rashin mutumci nake son ku aikata musu, ko kadan kada ku saurara musu, kar ku kuskura ku sake dawowa wajena nan Villa ba tare da babban sakamakon aikin dana sanyaku ba…..
Bazan lamunta ba, idan na kara jin labarin barayi sun kashe ko sun sace a jihar Zamfara da sauran garuruwan da ake aikata laifuka….
Ku ragargajesu, ku antayamusu, kuyi kacha kacha dasu, ku mamaye dukkan dazukan da suke boye, ku fesa musu wuta ta sama da kasa, ku addabesu ta yadda shakar iska zai dinga yimusu wahala…..
Fassarar jawabin Chief of defence staff kenan, amma nayi gyare gyare da kuma kare karen bayanai yadda zasu dace damu……
Rabiu Biyora ya wallafa a shafinsa.
Sanata Ahmed Lawan da Ali Ndume dai ba sabbin-yanka-raken shiga Majalisar Dattawa ba ne. Sun jima ana gogawa da su.
A baya za a iya cewa ‘yan gida daya ne, wato Jihar Barno. Amma tun bayan kirkiro Jihar Yobe, sai Lawan ya raba hanya da Barno.
Ali Ndume ya kuma a Majalisar Tarayya ya na mamba. Har Shugaban Masu Rinjaye ya taba rikewa. Shi ma Ahmed Lawan haka. Kuma dukkan su su na APC ne.
A cikin garken manyan shanun Majalisar Dattawa, Lawal da Ndume duk manyan bijimin sa za a kira su. Kowa na jin kan sa, kowa na ji da karfin sa sannan kuma kowa na da girda-girdan gogaggun shanun da ke bayan sa.
Yayin da Lawan ke takama da manyan shanun cikin garken APC, wadanda suka ce lallai shi ne zai zame wa sauran shanu uwar-garken Majalisar Dattawa, shi kuma Ndume Goga ne mai shiga gaban jerin garken shanu, kuma Goga ne mai nike wa shanu turba.
Ndume ya na takama da manyan kosassun shanun da suka ci suka yi taiba, sannan kuma suka bijire wa duk wani Ardon da ya nemi ya yi huda da su ba tare da huda musu hanci ba.
Wadannan kosassun shanu sun tsaya kai da fata cewa ba za a yi amfani da su a noman daminar bana ba, matsawar a gonar Ahmed Lawan za a yi noman.
Su abin da su ke so kawai shi ne a kai su gonar Ndume, a can za su saki jiki, su yini kuma su kwana, ko da Ndume bai ba su ruwa da harawa ba.
Shugabancin Majalisar Dattawa dai ya zama abin da Hausawa ke cewa: Gurugubji damben dattawa, wai wanda ya fyace shi ya yi kuka.
To, ga shi dai gaggan shunu biyu, kuma dukkan su duna, sun fito kowa na son kujerar. Kuma kowa ya sai tayar da kura ya ke yi, ya na ruri.
Shin tsakanin Lawan da Ndume, wa zai ji tsoro ya hakura? Wa za a kayar idan aka bar su biyun kowa ya gwada karfi ya kwaci kujerar.
Wato kokawar da babu ruwan ka, dadin kallo gare ta.
Sanata Ahmed Lawan dai babu tababa yaron jagoran APC, Bola Tinubu ne. An sha fadar haka, kuma har yau bai taba fitowa ya nesanta kan sa da Bola Tinubu din ba, ballantana kuma ya karyata.
Bola Tinubu ne a sahun gaban ganin Lawan ya zama Shugaban Majalisar Tarayya, dama kuma shi ne ya jajirce a 2015 ya ce Lawal din ne za a zaba.
Na biyu kuma shi ne Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa baki daya, Adams Oshimhole, wanda shi ne ke shiga-nan-fita-can domin ganin lallai hakar sa ta cimma ruwa, Lawan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Rukunin mutane na uku da ke goyon bayan Lawan, su ne sanatocin APC, wadanda ba su iya sauyawa daga abin da jam’iyya ta ce a yi, kuma su na goyon bayan Lawan.
GAGGAN DA SANATA LAWAN KE TAKAMA DA SU
Sanata Ahmed Lawan dai babu tababa yaron jagoran APC, Bola Tinubu ne. An sha fadar haka, kuma har yau bai taba fitowa ya nesanta kan sa da Bola Tinubu din ba, ballantana kuma ya karyata.
Bola Tinubu ne a sahun gaban ganin Lawan ya zama Shugaban Majalisar Tarayya, dama kuma shi ne ya jajirce a 2015 ya ce Lawal din ne za a zaba.
Na biyu kuma shi ne Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa baki daya, Adams Oshimhole, wanda shi ne ke shiga-nan-fita-can domin ganin lallai hakar sa ta cimma ruwa, Lawan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Rukunin mutane na uku da ke goyon bayan Lawan, su ne sanatocin APC, wadanda ba su iya sauyawa daga abin da jam’iyya ta ce a yi, kuma su na goyon bayan Lawan.
GAGGAN DA KE GOYON BAYAN NDUME
Ko shakka babu Sanata Ali Ndume na da magoya baya da yawa, masu son ganin ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Rukunin farko, akwai ‘yan APC masu ganin bai yiwuwa a ce tsofai-tsofai da su, a hana su yin zaben shugaban majalisa, kamar yadda doka ta tanada.
Su na jin haushin don me haka kawai Adams Oshimhole zai maida su wasu kananan yara, kamar daliban sakandare, ga shi kuma shi bai ma taba yin sanata ba?
Akwai kuma gaba dayan sanatocin PDP, wadanda tabbas ba su goyon bayan Sanata Ahmed Lawan. Za su so a ce wani wanda ya yi wa APC tawaye ne ya zama shugaban majalisa.
Ko da yake su ma na PDP din, akwai rade-radin cewa idan ta yi rincimi, za su tsaida dan takarar da wasu hasalallun sanatocin APC za su hadu da na PDP, a zabe shi.
A nan ana nufin akwai yiwuwar idan rikicin shugabancin ya kara tirnikewa, zai iya komawa a hannun PDP, kamar dai yadda aka yi a 2015.
JERIN WADANDA SUKA TABA RIKE MAJALISAR DATTAWA
Nnamdi Azikwe (NCNC): 1960
Dennis Osadebe (NCNC): 1960 – 1963
Nwazu Orizu (NCNC): 1963 – 1966
Joseph Wayas (NPN): 1979 – 1983
Iyorchia Ayu (SDP); 1992 – 1993
Ameh Ebute (SDP): 1993
Evan Enweram (PDP): 1999
Chuba Okadigbo (PDP): 1999 – 2000
Anyim Pius Anyim (PDP): 2000 – 2003
Adolphos Wabara (PDP): 2003 -2005
Ken Inamani (PDP): 2005 – 2007
David Mark (PDP): 2007 – 2015
Bukola Saraki (PDP): 2015 Zuwa Yau

Mai Girma Zababben Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano tare da Tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya Lado a Protocol Lounge Aminu Kano Airport.
Allah ya kai ku lafiya.

Kotun tarayya ta mai shari’a Lewis Allogoa da ke sauraron karar da EFCC ta shigar da zababben sanata na Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau da Ambasada Aminu Wali da Injiniya Mansur Ahmed,ta bada izinin ya je ya yi ibadar Umara a cikin wannan watan Ramadana in Allah ya kaimu.
A yau a zaman da aka yi, wanda shi ne zama na 11, kotu ta baiwa akawunta izinin ya baiwa Mallam Shekarau fasfo dinsa domin ya je kasa mai tsarki.
EFCC tana ci gaba da kawo shaidun da ta dogara da su wajen shigar da korafinta, zuwa jiya ta gabatar da shaidu guda hudu, saura shaida guda daya.
Tunda shaidu suka fara bada bahasinsu babu ko mutum daya da ya ambaci sunan Mallam Shekarau, kuma ma’aikatan banki sun gaya wa kotu cewa duk ma’amalolin da aka yi ba su sabawa ka’idojin aikin banki ba.

Munci karo da wani rubutu na AlkalaminSantsi inda yake karyata wani rubutu da yake yawo da sunan Sanata Ibrahim Shekarau
Mun sami wannan rubutu daga wani shafi na twitter mai dauke da Official TL of Ibrahim Shekarau, ganin wannan labari akan wancan account yabaka karfin gwuiwa cewa daga bakin Sanata Ibrahim Shekarau yake.

Matukar ba haka bane, to lallai akwai matsala masamman ta daukar labari daga shi wannan account, saboda gudun yada “FAKE NEWS” don haka masu wannan twitter handle su gaggauta yin bayani ga jama’a
#S4S2019

Wai wannan wasu su ke bi a matsayin jagora, mutuminda yace da mahaifinsa ‘WAWA”. Mutanenda Allah (S.W.A) ya ambata a cikin alkur’ani mai girma. Wallahi dana bishi a matsayin jagora gwara ma nabi wanda ba musulmi ba a matsayin jagora muddin ba zai hana ni addini na ba, dama shi na san ba musulmi ba ne. Kuma addini na bai hana ni mu’amilla da shi ba.
Amma wannan wanda gashi musulmin ne amma baya ganin girma da daraja ta addinin nawa, baya mutunta musulmai da malamai yan’uwa na, baya daraja da girmama manya da mahaifansa, bai damu da addini ba. Shi yasa ko lokacinda a kace ya dawo PDP ni banyi zumudi da kuma wata murnar dawowarsa ba, ballantana wai har na saka wata jar hula hular tsafi. Kuma ba abin mamaki ba ne dan wasu sun dauke shi a matsayin jagora, tinda hausawa na cewa shan Koko daukan rai. Amma mu duk abinda za muyi munfi so muyi shi wanda koda a gaban Allah (S.W.A) zaka iya kare kanka. Kuma dama ance idan za kaso mutum ka so shi dan Allah, haka ma idan za ka ki mutum to ka ki shi shima dan Allah.
Saboda haka muna san mai girma Sardaunan Kano ne dan Allah. Haka ma muna kin Kwankwaso dan Allah ne. Wanda ni ina fata ma ko a lahira Allah ya hada ni da shi. Kuma ko a lahira da ace ana yin siyasa wallahi shi zan sake yi kamar yadda nayi shi a duniya.
Basheer Basardaune,
#S4S2019,
10/4/2019. — with Lawan Namure, Abdullahi Ahmad Tadada, Abba Saraki and Sadiq Yallow Fagge.

A satin da ya gabata takwarorina tsaffi da sabbin sanatoci zababbu, sun ziyarce ni har gida a Kano
Wadanda suka ziyarce ni sune:
Sanata Danladi Sankara APC Jigawa
Sanata Bello Mandiya APC Katsina
Sanata Barau I Jibrin APC Kano
Sanata Yahaya Abdullahi APC Kebbi
Sanata Solomon Adeola APC Lagos
Sanata Lekan Mustapha.APC Ogun
Sanata Degi Eremeinyo APC Bayelsa
Dukkansu sun zo karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Sanata Ahmed Lawan APC- Yobe, wanda yake takarar shugabancin majalisar a yanzu.
1. “Na ji dadi matuka da aka girmama ni, kuma nagode kwarai.
2. ” A matsayina na zabbaben sanata ina addu’ar Allah ya zaunar mana da wannan sabuwar majalisa ta tara daidai cikin zaman lafiya don a samu yi wa al’umma hidima da zai haifar wa da kasarmu gagarumin ci gaba”
3. “Ina taya ka murnar wannan takara. Wannan babban kalubale ne. Nema abu ne mai zaman kansa, haka kuma shugabanci. Abin dadin kuma, mun san me neman da dadewa.”
4. “Kai daya ne cikin takwarorinka, na gamsu da wadannan abokan naka kwararru, za a samu shugaban majalisa na Najeriya da kowa zai yi alfahari da ita.”
5. “Na tabbata kana da duk wata kwarewa da zaka jagoranci majalisa. Muma masu yi maka kamfen ne ka zo ko baka zo ba. Baka bukatar ka ce mu yi, ko ka rokemu, mu dafa maka. Mun san ina muka dosa, wa kuma zai jagorance mu”
Wannan shi ne matsayina – Senator Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano


Hukumar zabe mai zaman kanta reshen Jahar Kano ta kammala shiryawa tsaf don kare kanta a kotu da zarar kotun ta nemi su a kan wani korafi ko wata kara da wani dan takara ko wata jam’iyya ta kai su a zabubbukan Kano da a ka gabatar na 2019. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin daraktan yada wayar da kai na hukumar kuma babban kakakinta a jihar, Malam Garba Lawal, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa bayan kammala mika takardun shaidar cin zabe da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da ’yan majalisar jihar guda 40, wadanda su ka hada da ’yan majalisa daga jam’iyyar APC su 26 da kuma jam’iyyar PDP 14 a majalisar dokoki ta jahar, inda kuma a ka mikawa gwamnan tare da mataimakinsa da ’yan majalisar jiha na APC a filin wasa na tunawa da tsohon shugaban kasa, Marigayi Sani Abacha, inda daukacin wakilan PDP su ka kaurace wa taron bikin, amma su ka karbi takardunsu a ofishin da ke Kano, kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa LEADERSHIP A YAU. Ya ce, “al’ada ce kuma abu ne da a ka saba, ba baQo ba cewa duk lokacin da a ka gabatar da zabe wasu su kan nuna rashin gamsuwarsu da zabe kuma su garzaya kotu kamar yadda doka ta ba su damar yin hakan kuma ba laifi ba ne kowane dan kasa ya nemi hakkinsa da damar sa a gaban kotu kamar yadda tsarin mulki ya tanada ya kuma yarda a yi hakan.” Ya ce, wata karar ko wani korafin ya na samu asali ne daga zaben fidda gwani a matakin Jam’iyya wanda ake kira da Primary Election da turanci to kuma a wani irin mataki ne da zarar an kai kara koto to koto takan nemi hukumar zabe ta INEC kuma mu mukanje ne mu ba da shaida kuma mu ka re kanmu akan wani abu da mai kara yayi zargi dan haka yanzu ma mungama shiryawa tsaf dan ka re kan mu a koto da zarar bokatar hakan ta tasu an neme mu a koto za muje dan kare kanmu. Haka kuma ya yabawa dukkanin masu rowa da tsaki a harkar gudanar da zabe tundaga kan al-ummar musulmi da abokan zaman su wajen yin addu’a na kamala zabe kamar yadda Allah ya nuna wannan lokaci na godanar da zabe yadda ya kamata sakamakon taka rawa ga dukkanin masu ruwa da tsaki sukayi inda kuma yayi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano da Qasa baki daya.
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2019/04/09/zaben-kano-mun-gama-shirin-kare-kanmu-a-kotu-cewar-inec/

👉 A ranar da aka rantsar da Mal. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Gwamna a 2003 ya shelantawa Kanawa cewa duk wata Daliba Mace Karatun ta Kyauta ne a Makarantun Jihar Kano, hakanan duk Yara Maza dake Karatu a fannin Kimiya da Fasaha (Science and Technology) suma Gwamnatin ta dauke musu biyan Kudin Makaranta.
2011 Kwankwaso na dawowa Gwamnan Kano yasoke wadannan tsarukan yace Almubazzaranci ne da dukiyar Gwamnati.
👉 Gwamnatin Mal. Ibrahim Shekarau har ta kammala wa’adinta tana biyawa ‘Yan Sakandire dasuka ci Qualifying kudaden Jarabawar Waec da Neco, daliban na samun damar yin Jarabawa guda biyu, kaga in yaro yasamu Matsala a daya watakila yadace a daya.
Nanma Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso yace Almubazzarranci ne, don haka Gwamnati tasoke biyan Waec kowa Mahaifin sa yabiya masa, Neco Kawai zata dauki nauyin biya.
Duk Mutane sun manta wadannan batutuwan, wasu kuma suna sane son zuciya ne yayi tasiri.
Daga Umar Faruq Muhammad

Yayin da mako daya ya rage hukumar da ke shirya jarabawar kammala Sakandare ta kasa wato NECO ta rufe karbar kudin rijistan dalibai da za su rubuta jarabawan a wannan shekara ta 2019, gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ba da umarnin fitar da kudi domin biya wa kafatanin daliban jihar da ke karatu a makarantun sakandare na gwamnati a fadin jihar.
Sannan Ganduje ya gargadi shuagabaninin makarantun da su guji karban kudi daga dalibai domin basu sakamakon jarabawarsu, inda ya ce kwanannan zai nada kwamitin da za ya bincika domin gano wadanda za su yi kunnen uwar shegu ga wannan umarni da ya bayar.



Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam ya karbi bakuncin ‘yan PDP tsagin Amb Aminu Bashir wali, Sen Bello Hayatu, Hon Salisu Buhari da Alh Yahaya Bagobiri a dakin taro na Africa dake fadar Gwamnatin Kano sunje fadar ne dan taya Gwamna murna da jaddada mubayi’arsu ga Gwamna a yayin maida jawabi Gwamna ya gode musu kwarai yabasu tabbacin dasu za’a gudanar da wannan Gwamnati.
You must be logged in to post a comment.