Sun Amfana Da Abubuwan Hawa

Gaskiyar magana dole a yabawa Hon Nasiru Ali Ahmad domin shine na farko daya saukewa masu tiri-tiri da takarar sa kabakin arziki

Musa Dambele Nazer Danhalak da sauran yan gwagwarmaya ina taya murna.

DG Rabi’u Baba Nabegu kaima Allah ya saka da alkhairi domin wannan duk kokarin ka ne.

Najeriya Ta Dakatar Da Hakar Gwal A Zamfara

Gwamnatin Najeyiya ta dakatar da ‘yan kasashen waje masu hakar gwal a Jihar Zamfara da kewayen ta.

Kamar yadda mukaddashin babban sifetan ‘yan sanda na kasar Mohammed Adamu ya bayyana cewa anyi haka ne domin a sami damar dakile masu tada kayar baya tare da yin garkuwa da mutane a Jihar.

Daurin Aure Cikin Hotuna

A wannan rana ta Lahadi 7/4/2019 daya daga cikin ‘yan gwagwarmaya a fadar mundubawa Mallam Haroun Shekaran Gama ya sake angwancewa kari akan angwancewarsa ta fari, yanzu haka Mallam Haroun Shekaran Gama ya zarce sa’ansa.

Muna addu’a Allah yasa albarka cikin iyalinsa ya bashi ikon sauke nauyin da ya karu akansa na yin adalci a tsakankaninsu, Allah yabada zuri’a dayyiba.

A madadin shugabannin #S4S2019 karkashin jagorancin Alh. Salisu Indabawa da Alh. Haruna Muhammad Gama Garkuwar Sardaunan Kano da Shugaban S4S na Jihar Kano Hon. Abdullahi Ahmad Tadada.

Ni Na’Allah Raheemeeb nake cewa Allah ya bada zaman lafiya.

ZAMU SAKA SHEKARAU A MANYAN DATTIJAN MAJALISARMU

Inji Sanata Ahmed Lawan

Dan takarar shugabancin majalisar dattijai Sanata Ahmed Lawan (APC-Yobe) ya bayyana cewa akwai wasu zababbun mutane da a koda yaushe majalisar dattijai ta kasa ta ke kaddara su a matsayin manyan dattijanta.

Ya ce, zababben Sanata na Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau, zai kasance daya daga cikinsu a wannan majalisa ta tara.

Ya ce, ‘yan majalisar dattijan Najeriya sun yi matukar farin ciki da murna da kasancewar Shekarau a zaurensu, saboda tun kafin ya zama gwamna mutum ne mai bin ka’ida da da’a, da kuma ya zama gwanan Kano ya Daidaita Sahunta.

Sanata Ahmed Lawan da shi da wasu sanatoci su goma sun ziyarci Mallam Shekarau ne a gidansa Juma’ar nan domin neman goyon baya da sanya albarka a takarar shugabancin majalisar dattijai ta Ahmed Lawan.

A jawabinsa Shekarau, ya gode musu, da suka yi takakkiya gurinsa, tare da shaida musu yana cikin wannan tafiya, kuma ya karbeta.

Mutum Bashi Da Tabbas

Nasan wani bawan Allah wanda yake zaune bashi da aikin yi,hakan ne yasa kullum matar sa sai ta fita unguwa domin ta samu abinda zata ci idan ta fita sai dare take dawowa.

Shi kuma yakan je majalissar abokai domin ya samu abinda zai kai bakin sa

Ana haka ne aka fadawa wani dan siyasa yace ya kawo takardun sa kuma cikin kankanin lokaci ya sama masa aikin gwamnati wanda yanzu haka matar sa bata fita ko ina rayuwar su ta inganta matuka.

Amma abinda ya bani tsoro ya bani mamaki shine ganin yadda wannan bawan Allah dashi da matar sa suka yaki gwamnatin nan sosai wai su basa son ganduje sun manta da niimar da Allah yayi musu ta sanadin wannan gwamnatin.

Kai wallahi sai da ta kai ni kaina gaba suke dani saboda ina son ganduje.

Allah ka tsarkake mana zuciyar mu ka sa mu kaunaci masu kaunar mu.

Masu Tafiya A Hanyar Hadejia Wajen ‘Yan Kaba Ayi Hattara

Wani ganganci sai bakin mutum

Yayin da wata trailer dauke da mai tafadi mai yana zuba a kan hadeja road kusa da Benni international school.

Madadin a nesanceta amma al’ummar mu sai ma kara kusantarta suke. Allah ya kyauta ya kiyaye tashin wuta.

Daga Abubakar Datti Dakata

Kamar Yadda Aka Saba Kowace Jummah

Mai Girma Zababben Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Ya halarci Sallar Juma’ah a Masallachin Yandutse dake Bompai anyi Zaman Fada kamar inda aka Saba.
Jibril Muhammad Na Tara

Tayaya Mai Mulki Zai Gane Yayi Kuskure?

Sau da dama zaka sha mamaki idan kaga yadda ake mu’amalantar masu mulki. Sai kayi mamaki tayaya mai mulki zai gane yayi kuskure, alhali mafiya yawancin mutane in suka je wajensa basa gaya masa hakikanin al’amari.

Hatta wasu Malamai da suke sukar shugabanni kan yadda suke tafiyar da Gwamnati, idan suka samu damar yin ido biyu da Shugabannin sai kaji suna yi musu addua ta fatan alheri kamar babu wani abu da ya faru na matsala.

To ta yaya Shugaba zai san yayi kuskure, alhali kowa yazo gunsa fatan alheri yake yi, bayan kuma masu sukar ra’ayinsa gasu a gabansa suna ta karkarwa suna cewa Allah ya taimake ka, ya baka yawan rai, kana kokari mutane suna yabawa, sai sam barka.

Wata rana George Bush yana Shugaban kasar Amurka, wata mata ta taba tare shi a hanya tace masa, “kai Shugabanmu ne, da kudinmu ake biyanka albashi, abinda kake yi a Iraqi ba daidai bane, a lokacin Bush yayi ta kokari ya nuna matar cewar saboda ita da sauran miliyoyin Amurkawa ake wannan yaki, amma matar taki yadda”.

To, mu kuwa, duk wanda ya samu damar ganawa da wani Shugaba gani yake kamar yaga daren lailatul kadari, yayi ta maganganun da zasu janyo a bashi kudi ko mukami. Allah ya shirye mu.

Yasir Ramadan Gwale
04-04-2019

TIRKA-TIRKAR SIYASAR KUMBOTSO !

Banso cewa komai ba amma dai lamarin yakai matsayin da zamu iya magana kasancewar mu Ahalil zikiri akan wannan batu, abu mafi muni a cikin wannan magana shine mafi yawancin masu magana akai basu da wani tabbaci akan lamarin iya kacinsu bazai wuce samun bayani daga wani bangare ko dai masu suka ko kuma masu kariya

Tabbas Wanda ake suka babban mutum ne a siyasa kuma jagora babu haufi akan haka

Masu suka suma tabbas sun sami kofa sun gano kuskuren wannan jagora sun kuma dukufa akan sukarsa ta hanyar fito da kurakurensa filli tare da kiraye kirayen maigirma gwamana ya dauki mataki akansa,

Ta’aliki na anan shine :

Kowanne bangare suji tsoron Allah kada idanuwa su rufe a kirkiri Shari domin kawar da wata dama ko ni’ima da Ubangiji yayiwa wani bawansa wannan kuskure ne kuma Allah bazai bari ba kuji tsoron Allah Ku tsaya akan gaskiya domin kurafin ku ya zama ba kushe da hassada bane

A gefe guda kuma akwai masu bada kariya da yawansu suma basa kumbotso a lokacin da wannan al’amari da ake zargi ya faru sabida haka nasihata garesu itace suma suji tsoron Allah kada suyi shaidar zur kuskurene kuma Allah bazai barsu ba duk kokarinka akan kayi kariya idan ya zama karya zaka kare bazakayi nasara ba fatana ya zamana cikin yakini kuke kare gaskiya tabbas Allah yana bayan gaskiya

Daga karshe Dukan mu yan Adam ne zamu iya yin dai dai kana zamu iya akasin haka,

Siyasa kuma anyi angma yanzu gwamnati zaa shiga kowa yana da hurumin bada shawara Dan haka ina kira ga yan siyasa da shugabani Dan Allah Ku bayar da shawarwari nagartattu Wanda zasu kara daga darajar jahar mu ta kano a wannan zubi na mataki na gaba wato ( Next Level )

Daga karshe nima zan bayar da shawara zuwa ga maigirma gwamna mas’alar kumbotso batune irin na Dan Hausa Wanda yake cewa ( idan kaji gan-gami akwai labari )

3/4/2019
Sulaiman Ibrahim k

Tafaru Ta Kare

Ta Faru Ta Kare, Ranar Da Ake Jira Domin Banbace Makaryata Da Masu Gaskiya Tazo. Dr Abdullahi Umar Ganduje Da Dr Nasiru Yusuf Gawuna Da Zababun Yan Majalisar Dokoki Na Kano Na Jam’iyar APC. Sun Karbi Shaidar Cin Zaben Su Daga Wajen Hukumar Zabe Ta INEC.
Allah Ya Sa A Fara Lafiya, Yasa A Gama lafiya.

Daga Abdullahi Ahmad Tadada

Shugaban S4S na Jihar Kano

KULLUKUM RA’IN…

Daga Umar Faruq Muhammad.

Daga 2015 har zuwa 2023 Shugaba Muhammadu Buhari ne babban wanda za’a yiwa tambaya akan al’amuran dasuka faru a Nijeriya.

PMB shine ‘First citizen’ a Nijeriya, don haka shine wanda yafi kowa cancantar daukar nauyin abubuwan dake faruwa a Nijeriya.

Shin Shugaba PMB yana kwana da abubuwan dake faruwa a Zamfara kuwa?

Karmu manta da fatawar da muka ginu a kanta a 2015 cewa duk rukicin da ya haura 24hours akwai sanin Mahukunta a cikin sa, yakamata Talakawan Arewa mu tunawa Gwamnatin PMB wannan tsohuwar fatawar.

Kisa batare da hakkin Shari’a ba babban laifi ne a wajen Allah, kare rayukan Al’umar kasa kuma babban nauyi ne rataye a wuyan Shugabanni.

Yakamata PMB ya farka!

Allura Zata Tono Garma

Kalubalantar nasarar da Maigirma Gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben da ya gabata wanda PDP ke shirin yi a kotu, shine kuma zai tozarta Jam’iyyar ta PDP a Jihar Kano baki daya.

Domin allura zata tono garma, masamman kujerun majalisar Jiha da PDP suka samu za’a bankado kullin da ke cikin wannan zaben inda Jam’iyyar APC zata karbe wadannan kujerun a kotu sakamakon aringizon kuri’un da APC ke zangin PDP tayi.

Idan baku manta ba Jam’iyyar ta APC ta bukaci Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Kasa reshen Jihar Kano ta bata bayanin yadda aka kada zabe a kananan hokumomin dake kwaryar birnin Kano guda takwas (8)

TUN DAGA JAHAR GOMBE YAZO FADAR MUNDUBAWA…

Wannan Bawan Allah dake hannun hagun Mai girma Sardaunan Kano, wani Masoyinsa ne daga Jihar Gombe. Sunansa Ismail Garba lokaci bayan lokaci yakan taso yazo domin ya gaida Mai girma Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Haka idan wani abu na farin ciki yafaru da Sardaunan zai taso domin taya murna ga Sardaunan na Kano.

Yanzu ma yataso tundaga Jihar su ta Gombe domin gaisuwa ga Malam Ibrahim Shekarau tare da tayashi murna zabensa Sanatan Kano ta Tsakiya.

Mai girma Sardauna yana farin ciki tare da nuna jindadinsa ga wannan ziyara.

Malam Ismail Garba Gombe Allah yabada ladan zumunci amin.

Bazan Yada Karya Ba

Nidai Banga Wanda Zaisani Na Yada Karya Ba Bayan Nasan Illar Haka Cikin Addini Na

Daga Sani Kabir Kwankwasiyya

Wani Matashi Dan Kwankwasiyya Yace Shi Ba Jahili Bane Dan Haka Baiga Wanda Zai sashi Yada Karya Ko Kage Dan Kare Manufarsa Ta Siyasa Ba Bayan Yasan Kabarin Mu Ba Daya Bane

Matashin Yace An sasu Yada Labarai Kan Cewa Ana Tashin Hankali Ko Za’ayi Tashin Hankali A Kano Bayan Zabe ,Andauko Tsoffin Hotuna Na Fadan Jos Da Kaduna Kai Hadda Fadan Boko Haram Ance Suyita Posting Akai

Yace ‘”Amma Ni Gaskiya Bazanyi Ba Dan Nasan Bahaka Bane Bana Yada Hoton Karya Kuma Bana Sharri a Siyasa ta” Inji shi

Sani Yace Shi Dan Kwankwasiyya Ne Kuma Hargobe Kwankwaso Ne Zabinsa ,Amma Shi Ba Jahili Bane
Allah Yasa Mugane Gaskiya Kuma Ya Bamu Ikon Binta ” – A cewar Sani Kabir Kwankwasiyya

RATAYE NAJEEB AKAYI

Daga Kamal A Baba Mahaifin Najeeb.

Bansan me nayi muku ba, kuka rataye wannan yaro najeeb Kamal A Baba an kashe shi har lahira.
Bayan an tashe su daga Makaranta, naje na ɗauko su, da shi da “yan uwansa, Nauwar da Nabeel, na kawo su Gida, jiya Alhamis babu makarantar Islamiyya sai Najeeb yace Abba don Allah ka taho min da Cumputer ta daga wurin gyara, kaga su Yaya Nauwar duk sun ɗauko tasu sina yi aiki tunda yau alhamis babu Islamiyya, nace Najeeb insha Allah zan biya na karɓo maka, tunda an gyara ma. Yace to Abba nagode.
Da yammacin jiyan dai misalin ƙarfe 5:00 na yamma ina Kasuwa wurin nema, sai Mai ɗaki na (Ummu Nauwar) ta kira ni a waya tana kuka, tana cewa Najeeb yana suma, sai na taso da sauri na nufo Gida, muna zuwa Asibiti likitoci suka duba sai suka ce min nayi hakuri Allah ya karɓi abin sa.
Bayan na dawo Gida da dare sai naga Igiya a ɗaure a jikin ƙofa a cikin Gida na, wanda hakan ya tabbatar min cewa lallai Rataye Najeeb akayi, akwai ɗa na Nabeel (ƙani ne a wurin marigayi Najeeb ɗin) ya ce yaga lokacin da almaji na ya cireMarigayin daga jikin Igiyar da aka rataye shi ya kwantar da shi a ƙasa.
Jami’an tsaro da Likitoci sun gama binkicen su sun bamu Gawar sa, insha Allah za’ayi Jana’izar sa ƙarfe 2:30 bayan an sakko daga Masallacin Juma’a a Gidan Alh Aminu Baba dake G/Ƙaya bayan Gidan Alh Ali me Tangaran.

Haƙiƙa Najeeb ya sha wahala, domin wuyan sa duk ya nuna alamar jin ciwo wanda likitoci suka tabbatar da cewa rataye shi akayi.

Waɗanda suka kashe wannan Yaro Idan ma wani laifi nayi muku, ba Yaron nan ne ya yi muku ba,
Yaa Allah kana gani, na kawo Kuka na gareka Yaa Allah ka sakamin akan wannan zalumci da akayi min, Yaa Allah.

IDAN NASAMI DAMA SAI NAYI RASHIN MUTUNCI!!

Daga: SANI ROGON AIKAWA DALA.

(Kalaman wani yaro da naji da kunnena)

Jiya Talata ina tsaye Daidai jakara Bola zan hau babur Din Adaidaita sahu, sai wani yazo saura mutum daya, amman Da wani yaro agaba yazauna gefen babur din hannunsa rike da kullun buhun Leda dakuma wani kwano, ban vata lokaciba na hau sai tafiya, Muna tafiya ina waya da wata mace, banyi auneba sai naga babu yarondake zaune agaba, nayi mamaki naceda mai adaidaita sahun ina kuma yaron dake zaune agaban mashin din naga yasauka bamu karasa inda zai saukaba, budar bakin mai adaidaita sahun sai yacemin “CEWA YAYI ASHIRINCE DASHI NIKUMA A TALATIN NAKE ZUWA” take naji wani bakin ciki ya cikamin zuciya, saboda bai kyautaba baisan wanne hali yaron yake cikiba, nace masa wallahi malam bakada imani, musulmine fa dan uwanka yaro, wanda baifi shekaru gomaba, shin naira gomace zatasa ka kasa taimakonsa ga kaya. Zuciyata cike da fushi na sauka daga kan Adaidaita sahun, nadawo akasa ina neman yaron, nafi minti goma ina nemansa ban ganshiba, zuciyata cikeda bakin ciki, kawai sai na fasa tafiya a dan sahun nabiyo ta lunguna da kafata, IKO SAI ALLAH, saura kadan in karasa sai na hangi yaron yanata sauri, duk saurina yafini sauri, duk fa wannan saurin da yakeyi kayane akansa, dakuma kwano a hannunsa, nayi sauri naje na tarar dashi, nace masa saurin me kake yaro?

ALLAHU AKBAR!!! HAWAYENE sharkaf a kan kuncinsa sunata zuba, tausayinsa ya kamani, nace masa shin ba kaine muka hau adaidaita sahu dakaiba a jakara?

yacemin nine, nace to mai yasaka kuka?

yacemin ina kukane saboda tun laasar nabaro gida, wannan Abincin kuma ummarmu da kannena suna jirana inkai musu suci! nace masa to a ina kake karvo abincin?

sai yacenun Abincin sadake daga Gidan HAJIYA MARIYA MAHAIFIYAR DANGOTE, Kullum sai naje na karvo saboda mahaifinmu ya mutu, kullum sai na shafe awanni biyu zuwa da dawowa akafata, sannan in hau mashin na naira ashirin zaman Gaba akaini gida!

take tausayinsa yakamani nace masa kayi hakuri wata rana sai labari yaro, ga mamakina sai naji yacemun “MALAM WALLAHI DUK SANDA NASAMU WATA DAMA SAI NA SHUKA RASHIN MUTUNCI SAI NA AIKATA RASHIN IMANI, SABODA AN RASA MASU TAUSAYA MANA!!!

take sai naji kwallah na neman zubomin a idanuna, nace masa kayi hakuri ba dukka mutane suka zama dayaba, muje gidan inga umman taku, nace masa!!! da muka fito titi, muka sake hawa wani mashin din har kusada kofar gidansu, muka sakko muka taka da kafarmu har kofar gidansu, wani abin tausayi uwar tana tsaye a soro yara biyu mace da namiji suna kuka kusa da ita, da Alama kukan yunwane, suna ganinmu suka rike kwanon dake hannun yayannnasu suka fara budewa, mahaifiyarsu bazata wuce shekaru talatin da biyarba, Amman wahalar rayuwa na neman tsofarda ita, cikin razana tacemun BAWAN ALLAH LAFIYA?
Allah yasadai lafiya, na kwashe labari na gaya mata, cikin tausayi tace wallahi badan wannan yaronba Abinci sai ya gagaremu, mahaifinsu ya rasu tsawon shekaru uku, Alumma sun gaza taimaka mana, yabarmu agidan Haya dakuma yara guda uku, basa zuwa makaranta, saboda halin rayuwa, kullum wannan yaron shike zuwa ya karvo mana sadakar Abinci.

babban abinda yabani mamaki, unguwar ga mawadata amman angaxa basu tallafi

munfi mintuna talatin muna tattaunawa da uwar, nayi Alkawarin dinka musu kayan makaranta tareda kaisu makarantar gamida yi mata alkawarin wasu abubuwa wanda nasan zan iya. na dauko dan abinda baxai gagaraba na mika musu, yaronnan yanata godiya uwar kuwa banda kuka babu Abinda takeyi, nace mata kiyi hakuri zan dinga zuwa lokaci zuwa lokaci, kiyi hakuri kada kidamu rayuwace wata rana sai labari.

“DARASIN DANA KOYA*
Da yawan mutane rashin agaxa musu shine yakesawa zuciyarsu ta qeqashe, yakamata mu dinga agazawa raunana, muma sai ubangiji ya agaxa mana, duk wanda ya nemi agaji mu agaxa masa rayiwace bamusan inda zamu tsinci kanmuba wallahi.

ubangiji ya agaxa mana.

Adalci ‘Yan PDP

Daga El-Mansoor Yusha’u Kyauta

PDP takama Sokoto anyi Adalci.
PDP takama Bauchi anyi adalci.
PDP takama adamawa anyi adalci.
PDP takama Taraba Anyi adalci.
PDP takama benue anyi Adalci.

APC takama Kano Amma Anyi zalunci.

To Anki Ayi Adalcin Duk Abinda zakuyi Kun dade Bakuyi ba Ganduje ne Gwamna Cikin yardar Allah.

Mun Shirya Tsaf!

Daga Baballe Kabiru Isyaku

Mun shirya tsaf! Mu na da hujjoji kwarara da su ke tabbatar da cewa gwamna Ganduje shi ne ya lashe wannan zabe”.

Wasu lauyoyi yan asalin Jahar Kano fiye da su dari uku [300] sun yi alkawarin kare gwamnan Jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a gaban kuliya kyauta ba tare da karbar ko da sisin kwabo ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka ce wasu lauyoyi guda dari [100] sun yi damarar kare dan takarar gwamnan Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP ya yin shari’ar da za su shigar kan zaben gwamna da su ke zargin su ne su ka ci.

Lauyoyin karkashin jagorancin Barista, Sayyadi Ahmad Nasara sun ce wajibi ne a matsayinsu na yan Jahar Kano, su je Kotu domin su ba wa gwamna kariya duba da irin kokarin da ya yi wajen gina Jahar Kano.

“Taba darajar Gwamna Ganduje tamkar taba darajar Jahar Kano ne, dan haka dole mu fita mu je mu bawa gwamna kariya domin ba za mu lamunci a zubar da kima da darajar Jahar Kano ba.

Mun shirya tsaf! Mu na da hujjoji kwarara da su ke tabbatar da cewa gwamna Ganduje shi ne ya lashe wannan zabe, da zarar kotu ta bukata za mu gabatar da su”.

A cewar Barista Sayyadi Ahmad Mai Nasara Jagoran Lauyoyin da su ka yi alkawarin kare gwamna Ganduje kyauta a gaban Kotu.

Ana Wata Ga Wata

Daga Hussaini Alhassan H.A

A Gobe Alhamis 28/03/19 kotun daukaka Kara dake Kaduna zata fara sauraron daukaka Karar da PDP reshen jihar Kano tayi dangane da karar da Hon. Alh. Ibrahim Ali Amin Little ya shigar akan yadda aka fitar da Engr. Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP.

A baya dai wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin cewar hanyar da aka bi wajen zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP haramtacciya ce, inda kotun ta umarci PDP data sake sabon zaben fitar da gwani kuma ta aikewa da hukumar zabe ta kasa Dan takarar gwamnanta a jihar gabanin zabe.

Bayan PDP ta daukaka kara an jingine wancan hukuncin zuwa lokacin da za’a kammala suraron wannan daukaka Kara da PDP tayi ,Wanda hakan ne ya bawa Abba Kabir Yusuf damar shiga zabe.

Masana Shari’a na ganin matukar Alh Ibrahim Al-amin Little ya samu nasara a wannan shari’a to hukuncin ya nuna cewar PDP ta shiga zaben gwamna a Kano harma ta samu kuri’u amma ba tare da dan takara ba kenan.

YADDA DILLIN TAKANYI DILLIN HAKA MA DILKIN TA KANYI DILLIN

Daga Haroun Shekaran Gama

Wallahi da na saurari maganganun kwankwaso sai na tausaya masa bisa yadda naji muryarsa tana rawa da shasshekar kuka bisa yadda kokawa da cewar wai an zalunce shi.

Ina gama saurararshi sai na fashe da dariya,nace mai guma cuta an guma masa duba da irin zalunci da rashin imanin da ya dinga aikata mana a baya.

Da farko dai duk wanda ya kasance tsatson jamjyyar ANPP ne to zai iya tuna zaben cike gurbi da ya wakana a kananan hukumomin Gaya da Garko yasan yadda wannan mutumin yayi amfani da karfin mulkin da yake zuga shi a wannan lokacin yaci mutuncin alumarmu,kai a karshe ma yasa aka hana Sanata Kabiru Gaya saukowa daga motarsa don yayi zabe inda a karshe haka ya hakura.

Abu na biyu shine,a shekarar 2014 lokacinda ya gabatar da zabukan kananan hukumomi,wallahi ni kaina a wannan zaben dakyar nasha a hannun ‘yan iskan da suka debo suka hanamu zabe a mazabunmu.

A shekarar 2015 lokacin muna cikin jamiyyar PDP wallahi haka yasa aka dinga dukanmu akayi mana kaca-kaca aka hanamu zabe duk domin yana da mulki a hannunsa ana zuga shi da kiranshi mai takalmin karfe.

Idan alumar Kano basu manta ba da kansa yayi wani ikirari a 2015 cewar yayi mafarki kazarsa tayi kwai 44 kuma ta kyankyashe su babu bara gurbi inda har yayi shekara hudunsa babu wata jamiyya da ta samu koda kansila a jihar Kano.

Shin wanda yayi irin wannan rashin mutuncin a lokacin da ludayunsa ke kan dawo shine yanzu zaizo mana da maganar wai an zalunceshi bayan irin adalcin da gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi wajen kyale masa kujerun majalisar jiha har guda 12.

Don haka kwankwaso da kwankwasawa kuyi karatun ta nutsu ku gane cewar ZAMANI KOWA DA NASA.

MASAURATAR KANO TA SAMU MATSALA KENAN ??

Bayan bayyan sakamakon zaben Gwamna a Jahar Kano, Masoya da Magoya bayan Gwamna Ganduje da jam’iyyar APC, sunje har gidan gwamnati domin murnar lashe zabe.

Ana tsaka da murna Hoton SARKIN KANO dake like tare da na Gwamna a jikin bangon babban dakin TARO na gidan gwamnati (Coronation Hall), ya hadu da wasu fusatattun Matasa inda suka jingina Tsani suka yagoshi.

Hakan yana nuni dacewar akwai wani da badaidai ba da Sarkin yayi lokacin zabe?

Dayawan magoya bayan Gwamna Ganduje da Jam’iyyar APC suna ganin Sarkin na Kano yashiga Siyasa kuma sai yadauki layin da yasa’ba da na Gwamnati da Jam’iyya mai Mulki.

Tun kafin akai ga zabe wasu suke zargin Sarkin na Kano yana goyan bayan Jam’iyyar PDP ne. Har akai zabe nan ma zargi yasake karfafa kancewar Sarkin na Kano yacire makudan kudade yabayar yace a zabi PDP.

Nima Mukhtar Hashim Hotoro ina daga cikin mutanen da sukaje gidan gwamnati domin taya murna, amma na kasa bawa kaina amsar da yasa aka cire Hoton Sarki.

Najiyo wasu ma suna kira ga Gwamna kan cewa lalle maganar nada Sarki da akayi a baya akwai Maganar INCONCLUSIVE cikinsa.

Dan haka suna kira ga gwaman da ya duba lamarin.

Nidai a matsayina na Mukhtar Hashim Hotoro bana goyan bayan Sarakuna su dinga shiga harkar Siyasa har su dauki ‘bangare.

Nafi yarda da cewar su Iyaye ne ga kowa dan haka duk wanda yazo shine nasu.

Abunda zan iya cewa kawai a nan Allah yazabawa MASARAUTAR KANO Abunda yafi Alheri gareta amin.

25/03/2019
Mukhtar Hashim Hotoro.

Sakamakon Karshe Na Gwamnan Kano

ZAGAYEN FARKO RANAR 9 MARCH 2019

PDP Abba K Yusuf 1,014, 474
APC Abdullahi U Ganduje 987, 819

ZAGAYE NA BIYU RANAR 23 MARCH 2019

APC Abdullahi Ganduje 45, 876
PDP Abba K Yusuf 10, 239

JUMLAR SAKAMAKON ZABUKAN

APC 1,033,695
PDP 1,024,738

BANBANCI APC da PDP 8,982

Zaben Cike Gurbi A Kano A Mahangar Yan Sanda

DIG Micheal Ogbizi a hirarsa da ya yi da gidan Talabijin na Channels yau 23 ga Watan Maris, 2019 da karfe 3:27 zuwa 3:36 na yamma. Ya ce

“A mazabar Gama (karamar hukumar Nassarawa) jama’a sun fito da yawan gaske wajen yin wannan zabe. Kuma an yi zabe cikin kwanciyar hankali.”

“A wasu wurare kadan haka an so a dan samu yamutsi, amma mutanenmu sun kai dauki da wuri. Saboda haka komai ya zama cikin lumana da kwanciyar hankali tuntuni.”

“MAGANAR WAI AN KAMA WANI KWAMISHINA DA KUMA MAGANAR WAI AN KASHE MUTANE BIYU, DUK KARYA CE KAWAI.”

“Akwai isassun jami’an tsaro a wuraren jefa kuri’a.”

“Ba wani zancen wai akwai ‘yan iska sun yi abinda suke so. Wannan zance ne kawai.”

Mazugal A Karamar Hukumar Dala

Ya isa shaida cewa, zaben da ake sake maimatawa yau a Jihar Kano yana tafiya lami-lafiya.

Mazugal ta Karamar Hukumar Dala ba’a barsu a baya ba wajen fitowa da kada kuri’unsu.

Allah ya sa a gama lafiya kamar yadda aka fara lafiya

Belli Ta Karamar Hukumar Rogo

Rashin kammaluwar zabe yau zai kammala a zaben da ake sake fafatawa a wasu akwatuna dake Belli ta Karamar Hukumar Rogo.

Masu zabe sunyi fitar kwari domin zabawa kansu abinda ya dace, kuma wannan ya isa shaida cewa, ana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

GAMA Cikin Karamar Hukumar Nassarawa A Yau

Daga dukkanin alamu, komai yana tafiya daidai kuma cikin kwanciyar hankali a mazabar Gama.

Masu jefa kuri’a sun fito suna sauke nauyin da ya doru a kansu.

Daga yanzu an shiga “MATAKI NA GABA” a Jihar Kano

UMARNIN AJIYE JAR HULA: Da walakin Goro a miya

Daga Umar Faruq Muhammad

Kowa yasan yadda Kwankwaso yabawa Jar hula Muhimmanci hatta sallar Juma’ah da Eid baya halartar su da wata hula ba Ja ba.

Lokacin da za’ayi zaben Gaya da Garko Kwankwaso ya Umarci mabiyan sa na 44 LGs sunje sun mamaye tashoshin Zabe da JAJAYEN HULUNA, suka hana kowa dangwala kuri’a sai mai Jar hula.

MUHADU A MUNJIBIR ma haka Kwankwasiyya sukaje da Jajayen huluna suka haifar da fitina, a karo na biyu Gwamnatin tayi shirin da suka kai da kafafun su.

Labari yabayyana cewa Kwankwasiyya sunyi tanadin tayar da tarzoma a zaben Gobe, an samu labarin Dillalin Albasa yayi wata ganawar sirri da Mafarauta da ‘Yan sara suka, akan aikin da zasuyi musu a tashoshin zabe.

Wannan dakatar da sanya Jar hular ta tabbatar mana cewa akwai wani Mummunan Kulli.

In sha Allahu Kullin ku kuntacce ne.

#KanoTaGandujeCeDaYardarAllah.

Ali Nuhu: ‘Abin da ya sa na shiga harkokin siyasa gadan-gadan’

Shahararren dan wasan Hausa Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa ba sabon abu ne ‘yan fim su shiga harkokin siyasa ba, kamar yadda yanzu ‘yan wasan Hausa suke yi.

Dan wasan ya bayyana mana hakan ne a wata hirar musamman da muka yi da shi a Kano ranar Laraba.

Ya ce an saba ganin ‘yan wasa suna shiga harkokin siyasa a duniya “kuma su zabi bangaren da suke goyon baya.”

“Wannan shi ne dalili na farko da ya sa na ji cewa ni ma wannan karon ya kamata a dama da ni,” in ji shi.

Daga nan ya ba da tabbbacin cewa daukar bangaren da suke yi a siyasa, ba zai jawo cikas ga sana’arsu ba.

“Ni ina ganin idan dai mutum ya dauki bangare kuma yana da hujjarsa ta daukar bangaren ba na jin wannan zai shafe shi. Kuma idan aka yi la’akari da yadda muke siyasar wasu na bangenan nan, wasu kuma suna wan can bangare,” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa: “Saboda haka duk inda ta fadi sha ne. Akwai dai ‘yan uwanmu a kowane bangare.”

Har ila yau, ya ce bambancin siyasar da ke tsakaninsu da abokan sana’arsa bai jawo wata rashin jituwa ba.

A karshe kuma ya ce ba ya tunanin wasu masoyansa za su iya juya masa baya saboda suna goyon bangaren siyasa daban da nasa.

https://www.bbc.com/hausa/labarai-47651139

Design a site like this with WordPress.com
Get started