Sanannen ‘dan jarida Jaafar Jaafar wanda ya fitar da video na zargi akan Maigirma Khadimul Islam Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya wallafa wannan rubutun a shafinsa na racebook tun ranar 25-9-2018 kamar yadda za’a gani a wannan screenshot.
Idan ba wata boyayya a kasa Malam Jaafar a matsayinka na ‘dan jarida da kariyar da kake takama da shi na dokar aikin jarida ya kamata ka tona asirin Kwankwaso da na Surukinsa amma sai kace wai an hanaka, waye ya hanaka?
Indai wadanda suka sa ka saki videon batanci na zargi akan Maigirma Gwamnan Kano domin su cimma burinsu na siyasa, to bai kamata ka boye wani abu da ka sani akan abokan adawarsa ba a matsayinka na ‘dan jarida, wannan shine adalci.
Ina kuke mutanen Kano? ya kamata ku tilasta wannan ‘dan jarida ya fada muku boyayyen abu game da Kwankwaso da Surukukinsa kar kuje kuyi zaben da zaku dawo kuna da na sani, domin babu shakka akwai wani mummunan abu a kasa da yake boye a kansu kuma ‘dan jaridar ya sani amma yace wai an hanashi yin rubutu a kai.
Malam Jaafar Jaafar lokaci yayi da zaka ceto al’ummar jihar Kano daga fadawa hannun su Kwankwaso da surukinsa, idan kayi haka duniya zata yarda kai ‘dan jarida ne na gaskiya wanda ba wasu kake yiwa aiki ba.
Jam’iyar APC ta jihar Kano ta nemi hukumar zabe da ta bada sunayen masu sa ido na gida da na kasar waje wato observers da aka tantance domin jan’iyar APC na zargin Kwankwasiyya sun yi amfani da na bogi a zaben daya gaba ta.
Sannan kuma Jami’ar ta APC ta sake neman hukumar zabe da ta bata jadawalin na’urar zabe wato CARD READER na wasu kananen hukumomin cikin birnin Kano inda PDP ta tafka magudi da aringizon kuri’a. Wannan tabbas zai kwayewa yan Kwankwasiyya zani a kasuwa da tona musu asirin irin gidogar da suka shirya a zaben daya gabata.
Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
Narch 20, 2019.
Hukumar EFCC ta bayar da notis cewa nan gaba kadan, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai bakunce ta, domin a samu bahasi daga gare shi akan kudi naira miliyan 70 da aka kwasa daga kowacce karamar hukuma guda 44 na KANO. Jumlar kudin ya kai naira biliyan uku da miliyan 80 kuma an kwashi kudaden ne domin aikin kamfen na takarar shugaban kasa da Kwankwaso ya yi a 2014 a jam’iyyar APC tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari. EFCC ta ce ta samu korafi ne daga wani lauya da yake wakiltar Comrade Abubakar Maishanu da wasu mutanen tun a 2015 kuma ta hada takardun ta, amma tirka-tirka a kotu wanda Kwankwaso ya shigar shi ya jawo jinkiri. Yanzu kuma ta samu dama mai kyau. A saurareta.
Allah dan tsarkin mulkinKa, dan Isar zatinKa, domin darajar litattafanKa, domin sunayenKa tsarkaka, wadanda AnnabawanKa da ManzanninKa da Amintattun bayinKa suke rokonKa kake amsawa, wadanda muka sani da wadanda bamu saniba dan soyayyar da Kakeyiwa Annabi Muhammad SAW, Ka bayyana wannan bawa naKa a duk inda yake.
Karka bari a barka a baya wajen sauraron zababben Sanatan Kano ta tsakiya Mallam Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano domin jin yadda zata kaya a gidajen radio kamar haka;
Talata, 19/3/2019
1. Arewa Radio – 10pm.-11
2. Guarantee Radio- 11pm.-12
3. Express Radio – 11pm.
4. Dala Radio – 8pm.-9
5. Rahama Radio – 10pm.-11
6. Freedom Radio – 11pm.-12
Wasu rahotannin sirri da aka samu daga wata majiya mai tushe da ta bukaci a sakaya sunanta, sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wata ganawar sirri da manya-manyan jiga-jigan jam’iyyar (PDP) da ke sashen kudancin kasarnan yankin Inyamurai.
Majiyar ta tabbatar da cewa sun yi ganawar ne domin kulle-kullen yadda za su ci zaben gwamna a Jihar Kano a zaben da za a sake ranar Asabar mai zuwa.
Inyamurai sun tabbatar da cewa, muddin Kwankwaso ya kawo wa jam’iyyar PDP Jihar Kano to ba makawa 2023 za su mara masa baya ya samu tikitin yi wa jam’iyyar takarar Shugaban kasa.
Sannan sun yi masa alkawarin tallafa masa da makudan kudaden da za su taimaka masa wajen sayen kuri’un masu zabe.
Babbar manufar Inyamurai a Jihar Kano ita ce, idan dan PDP ne ya ke mulkin Jihar za su samu cikakkiyar dama a Jihar Kano, tayadda za a sakar musu mara su gina gidaje da coci-coci a duk inda su ke so ba tare da gwamnatin Jiha ta hana su rawar gaban hantsi ba.
Haka kuma, za su samu dama da karfi ta hanyar tattalin arziki ta yadda za su mamaye kasuwanni da masana’antun Jihar Kano sannu a hankali.
Sannan kuma su na da babbar ajanda kan batun zaben shekarar 2023, domin sun lissafa cewa, muddin su ka samu Jihar Kano, to dan takararsu na shugaban kasa ba zai samu wata gagarumar matsala ba a Arewa duba da yadda Kano ta ke da yawan al’umma da kuma zama fitilar Siyasar Arewa.
A karshen tattaunawar sun cimma matsaya Kwankwaso zai kawo wa jam’iyyar PDP gwamna a Jihar Kano.
Sannan kuma gwamnan zai zama tamkar rakumi da akala, wato ma’ana sai abin da Kwankwaso ya ce shi zai yi a Jihar Kano. Haka kuma shi ma Kwankwaso umarnin Inyamurai zai rika karba ya na ba wa Abba domin cimma musu muradunsu.
Dan haka, al’ummar Jihar Kano su hankalta, kada su yarda Abba ya zama gwamnan Jihar Kano duk yadda za ayi su fita da katunan zabensu ranar Asabar, su kada Abba domin gudun fadawa hannun Abba a zahiri amma kuma ta bayan gida Inyamurai ne su ke gudanar da mulkin.
Kowa ya sani, a Jihar Kano an nemi a gina Coci a Jami’ar Bayero, amma aka hana, to yanzu idan mu ka yarda PDP ta kafa mulki a Jihar Kano, to fa sun samu cikakkiyar dama ne da za su cimma manufofinsu.
Amma mai karamin hange zai iya cewa ai Jihar Kano ta na da tsayayyen Sarki za a iya hana su wani abun, to ku sani gwamna ya na da karfi fiye da sarki, kuma muddin zai kawo musu matsala za su iya ba da umarnin a cire shi.
Duk wanda ya zabi Abba tamkar ya sa hannu ne cewar ya amince Inyamurai su mamaye Jihar Kano, haka zalika, duk wanda ya zabi Ganduje tamkar ya amince ne da zaman Kano karkashin ikon Hausa/Fulani Musulmai.
Assalamu Alaikum,
A Madadin Shugabanin Kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S) Na Jihar kano, Kananan Hukomomi Da Na Mazabu.
Muna Kira Ga Dukkan Masoya Da Magoya Bayan Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano)
Da Suke Guraren Da Za’a Sake Zabe. Da Su Fito Ranar Asabar 23/3/2019 Domin Zaben Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam) Da Mataimakin sa Dr.Nasiru Yusuf Gawuna.
Karkashin Tutar Jam’iyar A. P. C Mai Alamar Tsintsiya.
Domin Ci Gaba Da Aiyyukan Alheri Da Akeyi, Da Wanda Za’a Fara Anan Gaba. Dan Samun Karuwar Arziki Da Zaman lafiya.
Allah Ya Sa Ayi Zabe Lafiya, A Gama lafiya.
Allah Ya Bawa Jam’iyyar A. P. C Nasara.
Ameen Ya Allah.
Mun Gode,
Abdullahi Ahmad Tadada
Shugaban S4S Na Jiha
Ina matukar mamaki idan naji madugun kwankwasiyya yana ikirarin shine mai kishin kano
A 2003 munyi wasu ‘yan majalisu guda biyu Hon gali umar na abba daga kano municipil da Hon barau jibril maliya daga tarauni duk wani dan arewa yana alfahari dasu bama dan kanoba amma sabo rashinkishin kano da kuma biyan bukatar mai gidansa obasanjo yazo yakadasu wanda sanadiyyar haka tasa shugaban kasa na wananna lokacin obasanjo yasamu damar kashe kano da arewacin nigeria ta hanyar kakaba mana talauci shikuma madugu bukatarsa tabiya shikuma talakan kano ko oho
amma kuma ahaka yanzu shine wai mai kishin kano hhhmmm muje zuwa
A wata hira da manema labarai anan Kano, Sanata mai barin gado Rabi’u Musa Kwankwaso yace, Ganduje shine ya bata tsarin siniyariti, ma’ana shine a dauki karami a sakashi akan babba, badan Ganduje yayi haka din ba da yanzu babu matsala.
Shekara ta 2023 da shine zai zabi wanda yaga dama yace shine zai tsaya takarar gwamna a Kano.
Ni tambayata anan itace, Kwankwaso yanzu ya dauki Abba K Yusuf ya dorashi akan su Garba Bichi, Dan gwani, Rabi’u Sulaiman Bichi, Danbazau, Aminu Dabo da dai sauransu, shi kuma wane tsaro ya karya?
Ko dukkaninsu dana lissafa Abba Kabir Yusuf gaba yake da su?
Dan jarida Jaafar Jaafar wanda ya fitar da faifan video na zargi akan Maigirma gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yazo da wata boyayyar ajanda da yake da ita akan Malaman jihar Kano
Jama’a kusan kowa dai yanzu yana da masaniya akan abinda ya faru da Babban Alaramma Mahaddacin Al-Qur’ani Sheikh Ahmad Suleman Kano, amma ku duba abinda Jaafar Jaafar ya wallafa a jaridarshi ta Daily Nigerian a shafinsa na Twitter
Da ya tashi kawo labarin sai yace; Just In: Sheikh Sulaiman “Arba’in wa Arba’in” kidnapped ma’ana; “yanzu yanzu anyi garkuwa da Sheikh Sulaiman “Arba’in wa Arba’in”, me Arba’in wa Arba’in yake nufi? yana nufin hudu da hudu
Jama’ idan baku manta ba, dab da za’a gudanar da zaben Shugaban Kasa a wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar (idan ban manta ba a Abuja ne ko Kaduna) an gabatar Sheikh Ahmad Sulaiman Kano don ya rufe taro da addu’ah, yayi amfani da muryansa mai dadi a cikin addu’ar da yayi da harcen larabci ya roki Allah ya karawa shugaba Buhari shekaru hudu akan shekaru hudun farko da Allah Ya bashi, ya ambaci “Arba’in wa Arba’in” da larabci, idan ba’a manta ba na daura videon a wannan shafin nawa
Amma wace irin kiyayya ce haka zai sa wannan ‘dan jaridar Kwankwasiyyah Jafaru zaiyi amfani da kalmomin Arba’in wa Arba’in ga Malam Ahmad Suleman Kano bisa wannan tsautsayin da ya sameshi?, ai duk gabar dake tsakaninka da Malam bai kamata ka sako lamarin siyasa kan abinda yake jarrabawa ne daga Allah ba, kai ma bakafi karfin Allah ya jarrabeka da hakan ba, sai dai idan bakayi imani da kaddara ba
Wannan abin da kayi cin mutunci ne, ya nuna mana bakaji tausayin abinda ya samu Malam ba a matsayinka na musulmi, kuma daga dukkan alama kana cike da jin haushinsa, ta Allah ba taka ba Jafaru, Malam yayi addu’ah da bakinsa mai albarka kuma Allah Ya amsa shugaba Buhari ya zarce
Kuma ka sani mutuncinka da na wadanda kake yiwa aiki a jihar Kano ya zube warwas a gurin Masoya Sheikh Ahmad Suleman Kano, kuma indai juninka cin mutunci da batanci wa Malamai Mahaddata Qur’ani karshenka ba zaiyi kyau ba, muna tir da Allah wadai da rashin tausayawarka ga Malam Ahmad Suleman Kano
Allah Mun kawo karar wannan ‘dan jarida gareka Ka nuna masa aya!
Muna rokon Allah Ya kubutar mana da Malam Ahmad Suleman Kano tare da abokan tafiyarsa Amin
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Malam Ibrahim Shekarau sun umarci ‘ya’yansu
1. Haruna Ibrahim Shekarau (Chiroma)
2. Usman Abdullahi Umar Ganduje (Abba)
da su shiga cikin ‘yan uwansu Matasa wajen zagawa kananan hukimomin Jihar Kano 44 domin tallata hajjar APC.
Haka kuwa akayi.
Amma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tura Dansa
Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso kasar Dubai domin ya cigaba da rayuwarsa,
Sai gashi (Kwankwason) yana Umartar ‘ya’yan Talakawa da su zama ‘yan Jagaliya. Wai su dauki doka a hannunsu.
To ga #Shawara
Indai kunga ya kira Mustapha domin ayi Wannan zanga-zanga dashi, to lallai kunsan kaunarku yakeyi
Inko bai kirashi ba to sai kusan matsayinku a gurinsa.
Allah wadai da wannan mummunan tanadi da Kwankwaso yakewa mutanen Kano, wai tunanin PDP Kwankwasiyya zata sake dawowa kan kujerar gwamnatin jihar Kano.
Dan kuwa labarin sirri da yake samunmu yanzun nan ance jiya Jumaa da daddare ne ya kafa wani kwamitin da zai bi wurare a cikin Kano domin gano ko me aka yi da filayen da ya kwacewa mutane, wanda zuwan gwamna Abdullahi Ganduje ya mayarwa mutane da mallakar filayensu.
Ance Kwankwason yana ta zage zage jiya har yana cewa duk shegen da yake da hannu wajen dawowa da jamaa filayensu zai masa mummunar illa idan Abba Gida Gida ya samu cin zaben gwamnan Kano a zaben cike gurbi da za a yi ranar Asabar mai zuwa.
Kwamitin karkashin shugabancin Baba Umar yaba shi wa’adin kwanaki hudu da yazo masa da cikakken rahoto kan filayen da aka mayar da gine-ginensu da kuma filayen da har kawo yanzu masu mallajar filayen basu samu damar ginewa ba.
Jiya an ga yan kwamitin a sukwane tsakar dare suna bin titin daya tashi daga Kabuga zuwa titin Kofar Ruwa suna ta aune-aune da wasu injiniyoyi marasa kishin jamaa. Har ma labarin namu ya gano yadda shugaban kwamitin Baba Umar ya bugawa Kwankwaso waya da tsakar daren yake gayawa madugun nasu yadda jamaa suka dawo da gine-ginensu.
Sannan an ga wadannan yan kwamitin a wasu bangarorin cikin birnin Kano daga can bangaren Mariri Hotoro da wajejen su Tishama, suna duba ko akwai yiwuwar su kara gano wasu filayen ko gidajen da gwamnatinsu idan wai sun ci zasu kwacewa mutane da sunan wai zaa yi wasu ayyukan jamaa.
Allah Ya raba mu da wannan mugun mutum, Allah Ya saka mana kan wadancan filayen daya kwacewa mutane haka kawai. Wanda hakan ne ya jawo mutuwar wasu bayin Allah ba gaira ba dalili. Saboda sun samu ciwon hawan jini nan take.
Kar Allah ya ba Kwankwaso damar samun mulkin Kano, amin summa amin.
A ranar da aka rantsar da Malam Ibrahim shekarau a matsayin gwamnan Kano a jawabin sa na farko yace ya daukewa mata biyan kudin makaranta
Da zuwan sa gwammnan Kano Karo na biyu Sen Rabiu kwankwaso ya dawo da biyan kudin makarantar, har akai hira da kwamishinan ilimi na wancen lokacin yake cewa duk uban da bazai iya biyawa yarsa kudin makaranta ba yayi mata aure
Kasa da shekara daya zaibar gwamna kwankwaso ya kirkiro free education wanda yayi campaign dashi na takarar shugaban kasa
Da wanda yayi shekara 8 yana free education da wanda yayi watanni waye yayi free education ga Dalibai….?
Ya kamata a dena yaudarar ku da free education domin a samu mulki ko ta halin kaka.
Kamar yadda muka sha fada a baya cewa, Kwankwaso ne zai dawo mulki a karo na uku (3) a Jihar Kano matukar al’ummr Kano din suka zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamna, a wata ganawa da yayi a Kaduna da magoya bayansa, Kwankwaso yace, Abba bazai biya ma’aikatan na Jihar Kano mafi kankantar albashi na dubu talatin (#30,000) da Gwamnatin Buhari ta amince dashi ba.
A cewar Kwankwaso, wannan wata manuface ta Jamiyyar APC wacce ba zamu aiwatar da ita ba, kuma munsan ba zamu sami komai a asusun Gwamnatin Kano din ba, sai dai zamu biya albashi akan lokaci, wato 25 ga kowane wata koma kafin haka.
Yanzu dai zabi ya ragewa Jama’ar Kano da ma’aikatan Jihar, ko dai su ba Kwankwaso damar sake dawowa mulki a karo na uku (3) ko kuma su zabi Ganduje a karo na biyu (2)
Kowa yasan kungiyar Kwankwasiyya tayi Imani babu ruwan Siyasa da Addini, kwanannan Madugun su yace da Magada Annabawa sudena tsoma baki a siyasa ko kuma yayi amfani da Mumbarin sa na Ashariya ya ragargaje su.
A wurin ‘Yan Kwankwasiyya Madugun su Takalmin karfe ne dashi, kowa yataka ya taku.
Lissafin Kwankwasiyya babu wanda ya isa yatauye wa Madugu hakki, shiyasa ma zakaga babu tausasa harshe a wurin mafi yawan su.
Shin yanzu kuna tunanin Allah zai shiga lamarin Addu’ar dakukeyi bayan abaya kun dauka kune zaku iya kwatarwa kanku?
Manzo (S. A. W) yace damu Katuna da Allah lokacin dakake cikin walwala sai yatuna da Kai in kashiga kunci.
Allah Madaukakin Sarki yatserar da Annabi Yunusa daga cikin kifi saboda dama can yakasance cikin MUSABBIHIN, badon haka ba da Allah kyale shi zaiyi har zuwa ranar karshe.
Lokacin da Fir’auna yaga ruwa zai hadiye shi sai yace yayi Imani da wanda bani Isra’ila sukayi imani dashi, sai Allah yace dash sai yanzu bayan da yaki karbar Imanin?
Ba a fafar gora ranar tafiya, ci da Addini ba aikin ku bane, ku koma sana’ar ku taci da Takalmin Karfe.
Tare da girmamawa a gareku. Ina yi muku sallama ta addinin Musulunci, Assalamu alaikum.
Nine dan uwanku, Ibrahim Shekarau, wanda kuka zaba tare da sauran takwarorina a matsayin sanatoci domin mu wakilceku a Majalisar dattijai ta Najeriya.
Masoya da yawa suna tambayar gaskiyar zantukan karya da suke yawo dangane da samun sabani da shugabanninmu na jam’iyyar APC a Kano. Wannan labarai ne na kanzon kurege da aka kitsa su domin karya karfin jam’iyyarmu da dangantaka da junanmu a lokacin da muka samu mafi rinjayen ‘yan majalisar dokokin jiha a zaben da ya gabata.
KADA KU SAURARE SU. Ni Sardaunan Kano, babu komai tsakanina da shugabannin jam’iyya sai alheri. Wannan zance karya ne, bai faru ba. Ba a yi ba. A kan titi na tsince shi kamar yadda kuka ji shi.
Ina kira ga duk masoya da ‘yan uwa su yi watsi da wannan karya. Shakiyanci ne na masu siyasar da farfagandar karya da yaudara. Ina rokonku a ranar 23 ku fito a duk inda za a maimaita zabe a fadin Kano, ku dangwalawa APC. Kada mu banbamta shugaban kasarmu na APC da sanatocinmu na APC da ‘yan majalisar tarayyarmu na APC da ‘yan majalisar jiharmu na APC da gwamnan jiha.
Allah ya ja zamanin Najeriya
Allah ya ja zamanin Kano
Allah ya ja zamanin APC
Yanzu Haka a GWAGWARWA POLICE STATION
Dandazon yan jam’iyar PDP kwankwasiya daga Gama sunzo su kwaci yan uwansu wanda aka kama sunabi gidagida a Gama suna siyan kuria
Amma yan sanda sun bude wuta sama da HARBI DA TIYAGAS
Makaryacin Dan jaridannan
Jafaar Jafaar – shine mutum na farko da ya wallafa labarin kanzon kurege na shirin tsige cp wakili a shafinsa na Daily Nigeria
Sbd adawarsa da Gwamna Ganduje Allah ka tsinewa wanda bayason zaman lafiyar kano.
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano , Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na kira Ga daukacin al’ummar Jihar Kano da a kwantar da hankula, a zauna lafiya tare da girmamawa da ganin mutuncin juna musamman a wannan lokaci da mu ke ciki.
Mu sani cewa zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma shine tushen kyautatuwar rayuwa da ci gaba a kowanne lokaci.
Jihar Kano ta mu ce baki daya. Don haka mu guji aikata duk wani abu ko kalamai da ka iya haifar da rashin zaman lafiya sakamakon sabanin ra’ayin siyasa ko makamancinsa.
Mai Girma Gwamna na kira ga iyaye da shugabannin al’umma su sa ido kan ‘ya’yansu da jama’arsu, su kuma tsawatar yayin da aka ga suna kokarin aikata ba daidai ba ko kuma daukan doka a hannunsu.
Hukumomin tsaro za su ci gaba ta ayyukansu na tabbatar da zaman lafiya da kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma a ko’ina a fadin Jihar Kano.
Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Allah ya taimaki Jihar Kano da daukacin al’ummar Jihar Kano. Amin.
Sako daga:
MALAM MUHAMMAD GARBA
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano
11/3/2019
The Kano State Police Command has warned residents of the state against celebrating unofficial results of the Governorship and State House of Assembly elections.
Ganduje yayiwa jagoranmu Sardauna halacci kuma ya mutunta Sardauna a fili qarara kowa ya gani, wanda hakan ya jawowa gandujen baqin jini a wajen wasu yaransa da suka ganin sun wahalta masa.
Gandujen yayi wa Sardaunan wannan halarcin ne a dai-dai lokacin da wadanda Sardaunan ya goya suka ci amanarsa, koda kuwa gandujen yayi hakan ne don cimma wani burinsa (kamar yadda wasunmu suke kafa hujja).
Yanada daga cikin sunnar Ma’aiki(SAW) maida alheri ga wanda yayi masa sharri, balle kuma uwa uba wanda yayi masa alheri.
Ko wanne dan adam, ciki harda ni da kai dake muna da ‘yan kura-kuranmu da baza’a rasa ba, saboda haka shiyasa addininmu ya koyar damu cewar duk sanda zamuyi magana akan hali ko ‘dabi’a ta mutum, mudinga adalchi muna auna ayyukansa na alheri da akasin haka. Wanda hakan zai bamu damar yi masa adalci wajen yanke masa hukunchi.
A “NAWA” ganin da kuma dan zagaye zagayen danayi tsakanin garuwa da dama na arewa dakuma kudanchin qasar nan between 2015 zuwa yau, a gaskia interms of physical projects and some of his policies are far more better than most of the gwamnatocin.
Anan Kano maganar gaskia duk da wasu ‘yankura kurai da baza’a rasaba yayi qoqarai sosai. Wajen kawo wasu ayyuka da talaka zai amfana, karasa asibitocin zoo road dana giginyu kadai da yayi ya isa a yaba masa, wanda gwamnatin rabi’u musa kwankwaso taqi karasawa da gangan don ayyukan Shekarau ne.
Anan nakejan hankalinmu da mu daure mu nutsu sosai muyi amfani da tunanimu wajen ganin munyi iya qiqarinmu mu nuna masa cewar muma ‘yan halak ne, mu kumayi kokarin jifan tsuntsu biyu da dutse daya. Wato mufito qwanmu da kwarkwatarmu mu zabi ganduje kamar yadda Sardauna ya fada, sobada ayyukan alherin da yayiwa kanawa da kuma mutunta dattijanmu da yake ciki harda jagoranmu Sardauna.
Lamuran rayuwa dakuke gani kowa yana gudanar dasu ne gwargwadon yadda ya fahimta.
Lissafin Fahimtar Siyasar Kano ya tabbatar damu akan tsarin goyawa Gwamna Ganduje baya a zaben Gobe, ku kuma taku fahimtar ta saba da tamu.
Meyasa bazaku tsaya ataku ku barmu a tamu ba sai kudinga nuna tamu sabawa Allah ce saboda kuna ganin Ganduje yana da wani laifi?
Don Allah masu biyoni ta Inbox da sunan nasiha ko Jan hankali kuyi hakuri ku dai na, jinake tare da ku muka yi tallan PDP lokacin da Arne ke takara da Musulmi? Meyasa a lokacin kuka manta da Ayar da tace
“عبدمؤمن خيرمن مشرك…؟
Ita dai Fahimta fuska ce, ku dauki tamu a matsayin IJTIHADI kamar yadda taku din ma Ijtihadi ce.
Tare da girmamawa a gareku, ina yi muku fatan alheri, ina rokon Allah ya yi riko da hannayenmu gaba daya.
A satin da ya gabata, kun fito kun zabeni da abokan aikina Sanatoci biyu da ‘yan majalisar tarayya a mazabu 24 a tutar jam’iyyar APC.
Mun gode kwarai da karamci da kuka nuna mana ta hanyar bamu dama mu wakilceku. Mun karbi amana kuma da yardar Allah ba zamu ci amanarku ba. Ina rokon duk wanda ya samu damar yin zabe a makon da ya gabata, kuma ya bamu kuri’arsa, ya daure ya cika ladansa a wannan Asabat mai zuwa.
Ina rokonku ku fito, fitar dango ku zabi jam’iyyar APC KAWAI,.mai alamar tsintsiya, ita ce jam’iyyarmu, a cikinta muka ci zabe, kuma a doron bayanta zamu wakilceku, mu yi muku ayyukan alheri da Allah ya nufa tare da hadin gwiwar gwamnatin jiha.
1 Kace bakasan GANDUJE ba saboda zargin cin hanci da rasha amma kana San KWANKWASO shida aka kama dumu dumu har aka yanke masa hukuncin white paper 2003.
2 Kace bakasan GANDUJE saboda ya sayar da filin masallaci amma kana San KWANKWASO Wanda ya rushe masallatai.
3 Kace bakasan GANDUJE Saboda ya rufe wasu makarantu Amma Kanasan KWANKWASO daya kori malaman makaranta.
4 Kace bakasan GANDUJE saboda baikai yara makaranta kasashen waje ba Amma ka manta 65% na yaran da KWANKWASO ya tura kasar wajan a lokacin GANDUJE suka gama makarantar kuma saidai ya biya musu kudin suka samu wannan damar.
5 Kace bakasan GANDUJE saboda yana sayar da filin gomnati Amma kanasan KWANKWASO Wanda shi filin jama’a ma ya kwace ya ya siyar wasu ya rabar.
kace kanasan KWANKWASO ne soboda yayi underpass guda 2 Shima GANDUJE yayi 2 ga ta uku nan Yana yi
Kace kanasan KWANKWASO ne saboda yayi flyover to Ai wadda ganduje yai tafi ta sa tsayi
Note: Ku rike jarhular Amma kano Sai Uban Abba Insha Allah
A kowane lokaci ana bukatar shugabannin al’ummah su dinga fadawa mabiyansu gaskiyar al’amari da aikata daidai da gujewa ba daidai ba, domin kara musu kwarin gwuiwa a inda aka sami aikata daidai, haka kuma kaucewa rashin daidai yayin da aka sami wani sabani.
Wannan shine yake rage tsegumi da jita-jita da rashin tabbas a tafikas da al’amuransu, kungiyar kwankwasiyya ba ta iya yin wadannan abubuwa, a hannu guda kuma, Sardaunawa suke kwatantawa, shiyasa daga karshe al’amuran Kwankwasawa suke samun damuwa yayin da gaskiyar abubuwa suka bayyana sabanin abinda shugabanninsu suka dasa musu a zukatansu.
Na tabbatar da cewa, da shugabannin suna kokarin jawo hankalinsu akan gaskiyar lamari, ko shakka babu mabiya bazasu fada cikin rudani mai firgitarwa ba, yayin da hakikanin gaskiya ta bayyana, duk lokacin da muka kwatanta mabiyan gidan Sardaunan Kano da mabiyan gidan Kwankwaso zakaga banbancinsu kamar sama da kasa, domin a fadar Mundubawa inda Sardaunan Kano yakewa mabiyansa huduba ta gaskiyar inda aka tsinci kai, ba haka yake faruwa a fadar Lugard ba.
Wannan dalili yasa mabiya Mallam Ibrahim Shekarau sukafi nutsuwa da kwanciyar hankali domin an sanar dasu gaskiyar lamari, sababin mabiya Kwankwaso wadanda a kowane lokaci suke cikin rudani na rashin sanin tabbas.
Tun ranar da wata babbar kotun shari’a ta gwammanatin tarayya a Kano ta fidda hukuncin soke dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP, sai Kwankwasawa suka shiga rudani, domin shugabanninsu sunki fada musu gaskiyar lamarin, inda sukaci gaba da shaida musu cewa wannan hukunci bai shafi gwaninsu Abba K Yusuf ba.
Tambaya anan itace:
1) A wace Jam’iyya Abba K Yusuf yake takara?
2) Akwai wani dan takara ne da Jam’iyyar PDP a Jihar Kano tabawa tuta bayan Abba K Yusuf?
Indai tambaya ta farko, amsar itace, PDP
Tambaya ta biyu kuma, amsar itace, Abba K Yusuf ne kadai mai tutar
To, gaskiyar lamari shine, takarar Abba K Yusuf kotu ta soke, kodai an ambaci sunansa ko ba’a ambata ba, saboda shine dan takarar gwamna a PDP mai tutar shiga takara da sauran jam’iyyu.
Don haka, ina kira ga Kwankwasawa ku sani cewa, Jam’iyyar ku ta PDP bata da dan takarara a Kano a halin yanzu, saidai kawai rudani da kuke ciki.
You must be logged in to post a comment.