Babbar Kotun Tarayya A Jihar Kano Ta Soke Takarar Abba K Yusuf

Mai shari’a Lewis Allagoa dake babbar kotun tarayya a Jihar Kano ya soke takarar Abba K Yusuf na Jam’iyyar PDP sakamakon rashin gudanar da zaben fidda gwani da ba’ayiba

Sauran bayanai na nan tafe

Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa

Atiku ya bayyana dalilin da ya sa aka kama surukin sa da lauyan sa Source: Facebook

Atiku a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar 4 ga watan Maris, yayi kira fa wadanda ke hukunta su da su tuna cewa gwamnati aba ce da ake sanya ran za ta wanzar da zaman lafiya ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.

“An tsare surukina da lauyana, daya tsawon makonni 3 sannan dayan kuma kwanan nan aka kama shi. Duk suna biyan bashin mara mun baya da suka yi ne. Ina bukatar wadanda suke hukuntasu dan su tuna cewa hakkin gwamnati shine ta wanzar da zaman lafiya da yin adalci ga kowa, ba wai wadanda suka mara masu baya ba kawai.” A baya mun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Jama’til Nasaril Islam, Alhaji Sa’adu Abubakar III ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara a zaben 2019 daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu. Sai dai Sarkin Musulmai yayi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya sha kayi a hannun Buhari, daya rungumi kaddara, ya saduda, kuma ya rungumi zaman lafiya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Read more: https://hausa.legit.ng/1225376-atiku-ya-bayyana-dalilin-da-ya-sa-aka-kama-surukin-sa-da-lauyan-sa.html

An Raina mana Hankali – Ismail Lamido

Kano Central Situation Room

An Raina mana Hankali

Bayan zama da muka yi na kwana uku don sani halin da ake ciki a zaben Sanata kano ta tsakiya da sanin yanayin da zaben yake ciki tun daga fara shirin zabe har saka kuri’a da kidaya ta, munyi aiki tukuru wajen tabbatar da kuri’un da aka zuba sun tabbata an bayyana su.

Tun ranar farko da muka fara wannan aiki muka fara samun matsala daga wani daga cikin darktocin kwamitin yakin neman zaben Wanda baya ganin kimar kowa, kuma duk aikin da bashi ya tsara ba aikin banza ne a wajen sa, a wannan rana ba irin kushewar da baiyi mana ba wai bamu san aikin mu ba babu abinda muke.

Abin takaici sai da muka kammala aikin sai gashi yazo ya shige gaba ko kunya babu wai bai san haka aikin yake har ya kankane komai wajen gabatar da Ayyukan yan kwamitin a gaban Sanatan, ya gabatar da jawabi kai kace dashi akayi duk kwanakin da akayi aikin.

Wannan darakta shine ya sauke sunayen yan social media da aka saka zasuyi wannan aikin ya maye gurbin su da mutanen da ko waiwayar aikin basu yi ba har aka kammala.

Duk Wanda aka bayyana dan kwamitin da zaiyi aiki a Situation Room ne babu wanda yayi wani abu mutane biyar sune suka gabatar da wannan aikin banda su babu wanda ya yi wani abu sai zaman hira.

Bello Muhammad Sharada
Hon Muktar D Gora
Ismail Lamido
Usman Solo
Ibrahim Shehu

Banda wadannan babu wanda yayi wani aikin da aka gabatar a wannan dakin na tattara bayanai da sanarwa duniya halin da ake ciki.

Nayi wannan rubutu ne saboda an raina mana hankali an raina mana aiki mun gama shan wahala wasu suna yawo suna kafafa wai sune suka yi.

Zabi Ya Rage Naku – Nafiu Rabiu Sani Mainagge

“Ina da ilimin taurari..”

“Ina da ilimin ruwa..”

“Duk wacce ta daura atamfar da Ganduje ya raba ruwanta zai qafe…”

“Duk wacce ta daura atamfar aurenta zai mutu…”

“Aure miliyan daya zasu mutu a Kano…”

Tambayoyin a nan sune:

1. Shin Kwankwaso boka ne ko kuwa?

2. Yana da ilimin ruwa da taurari ya aka yi bai hango faduwarsu zabe ba a Kano?

3. Shin burinsa ne aure yayita mutuwa a Kano?

4. Meye ribarsa a maganganun batsa na cewa ruwan mata zai qafe?

5. Shin wannan ya kamata ya zama jagora ga al’umma mai mutunci da addini?

6. Shin ma wai, shine yake takara ko wani ne. Idan wani ne wanda ke takarar bai da bakin magana ne ko ba zai iya bane?

Gareku Kanawa.

Zabi ya rage naku.

BAREWA BA ZATAYI GUDU DANTA YAYI RARRAFE BA – Amir Yakson

Kowa ya zabi Abba Gida-Gida ya zabi a Rushe dakin Allah. Abba Gida-Gida shine ya jagoranci rushe masallatai a cikin garin kano a bisa umarnin Ogansa madugu.

Allah ka tseratar da mu daga irin wannan mulkin na karshen zamani

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Ana sanarda dukkannin Exco na jiha, da Co-ordinators na kananan hukumomi, da kuma dukkannin membobi na #S4S2019 cewa akwai zuwa yiwa jagoranmu kuma shugabanmu Khadimul Bn Adam wal Islam mai girma Sardaunan Kano wanda zuwan zai kasance kamar haka:-

Rana:-Lahadi 03/03/2019.

Wurin haduwa:- Fadar Mundubawa gidan Sardauna.

Lokaci:- 11:00am na safe idan Allah ya kaimu.

Allah ya bada ikon zuwa ameen.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S2019,
01/03/2019.

Ungulu Da Kan Zabo – Sani Adamu Hotoro

Ungulu da kan zabo daga wajen y’an kwankwasiyya. Bayan sun gama zagin baba buhari sun nuna cewar suma karfin su ya kawo 
Amma jim kadan bayan kanawa sun yi musu wanwar sai suka nuna yanzu su ma wai na buhari ne

Kun gama zabar atikun ku kunga bayyi nasara ba shine yanzu za ku rainawa kanawa hankali, mu mun ce sai uban Abba

Me Zakuce Akan Wannan

Munyi sallah mungayawa ALLAH ya bimana hakkinmu domin jakikanin gaskiya duniya tasani mu mukaci zane akamurdemana Allah gaka gasunan Allah kayimana sakayya ta Alkahiri Ameen
By HAMZA A ADO YAKO

Kwankwasawa
Ali Datti Yako

Zabe Na Gaba

Ga Sakon Kasashen Duniya Ga Yan Najeriya Akan Zaben 2019.Wannan Yabon Da Sukayi Mana Shine Zai Kara Tabbatar Da Dimukuradiyya Mai Dorewa A Najeriya.
A Saboda Haka Al’umma Mu Fito Ranar 9th March, Domin Zaben Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam Da Mataimakin sa Dr.Nasiru Yusuf Gawuna Tare Da Yan Majalisar Dokoki Na Kano Baki Daya.
A. P. C Daga Sama Har Kasa.
Sako Daga S4S

Mu Dan Dara

Godia da ruwan bama-baman kuri’a sai Borno

Qarar fashewar tukucin kuri’a sai mutanen Yobe

Akori maigida da kuri’un gidansa sai Gombawa

Kaki naka kaso mutumin kirki sai Adamawa

Gadara da nuna isar ruwan kuri’u sai Kanawa

Kafidda rai kuma abaka sai mutanen Nasarawa

Kasaka rai a hanaka sai mutanen Ibadan din Oyo

Tarun dukiyar kuri’u da qaramar kyauta sai Lagos

Kanaji kanagani amaka karfa-karfa sai jahar Rivers

Yaudara, rowa da yawan koke sai kasar Inyamurai

Uba yayiwa dansa allurar gata sai mutan Katsina

Iya karbar bako, su daukeshi kamar nasu sai Bauchi

Son kudi da tsoron Treasury Single Account sai FCT

Nuna bambancin fara da baqar kuri’a sai a Taraba

Jajircewa da jan wuyan ruwan kuri’a sai Kaduna

Taltalin kuru’u da calculator sai mutanen Jigawa

Anonymous

SAKON GODIYA

Da sunan Allah Ta’ala, mai rahama da jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu SAW.

Ni Sanata Ibrahim Shekarau, mai wakiltar al’ummar jihar Kano Ta Tsakiya,, ina farawa da godiya ga Allah bisa wannan nasara da ya bamu ta cin zaben sanata a jam’iyyarmu ta APC.

Wannan nasara ta al’ummar mu ce gaba daya, don haka ina godiya garesu duka.
Ina amfani da wannan dama na godewa jama’ar Kano Central da suka ga dacewar su zabeni don na wakilcesu a majalisar dattijai ta Najeriya.

Ina godiya matuka ga jam’iyyar APC ta kasa da ta jihar Kano da babban kwamitin kamfe dina da suka yi dawainiya har aka zo wannan matakin.

Haka kuma ina mika godiya ta musamman ga gwamnan jihar Kano da ‘yan majalisarsa da duk zababbunmu na APC masu komawa da sababbi da shugabanni zababbu na mulki da jam’iyya na Kano a kananan hukumomi.

Wannan nasara tamu ce gaba daya, kuma da yardar Allah, zamu ci gaba da amfani da ita don hidimtawa al’umma da basu wakilci na kwarai.

Nagode
Sanata Ibrahim Shekarau CON
Sardaunan Kano

SAKON TAYA MURNA DA KUMA BANGAJIYA.

A mamadin jagororin #S4S wato Alhaji Salisu Indabawa da Alh. Haruna Muhammad Gama (Garkuwar Sardauna) da kuma shugabanninta na jiha dana kananan hukumomi karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada. Muke amfani da wannan dama domin mika sakon bangajiya ga masoya da jama’ar Kano ta tsakiya da kuma yan jam’iyyarmu ta APC mai albarka bisa fitar dango da su kayi domin kadawa mai girma Sardaunan Kano kuri’a da jam’iyyarmu ta APC.

Da addu’a da fatan Allah ya sakawa kowa da alheri ya kuma huta gajiya.
Bayan haka kuma muna sake yin amfani da wannan dama domin mika sakon taya murnarmu ga mai girma Sardaunan Kano bisa nasarar lashe za6ensa da yayi wanda aka gudanar ranar Asabar 23/2/2019. Allah Ubangiji (S.W.A) ya sanya alheri ya kuma yi riko da hannunsa.

Da fatan Allah ya sakawa kowa da alheri ya kuma huta gajiya. Da fatan kuma yadda a kayi fitar dango aka kadawa mai girma Sardauna da shugaban kasa kuri’a ranar Asabar 23/2/2019 to haka za a fito ranar Asabar 09/3/2019 domin kadawa mai girma gwamna Khadimul Islam da yan takarkarinmu na majalisun jihohi kuri’a.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S2019,
25/2/2019.

Da Dumi-Duminsu

Mallam Ibrahim Shekarau ya lashe zaben Sanatan Kano ta Tsakiya da kuri’u masu rinjaye sosai

Mallam Ibrahim Shekarau ya sami kuri’u 506,271 a jam’iyyar APC.

Shi kuma abokin karawarsa Aliyu Sani Madaki ya sami kuri’u 276,768.

fb_img_1550875853981-1765866933.jpg

FADUWAR BAKAR SHAFA!

Bayan kammala zaben 2015 Abdullahi Rogo ya Jagoranci wata kangararriyar tawaga dasuka kangarewa Amintacciyar tafiyar Fadar Mundubawa.

Daga cikin dalilin su na waccen Kangarar shine wai Jagorancin Mundubawa yanada sako -sako a harkar samun Nasarar zabe, Tauhidin su yanuna musu sai an hadu da Kwankwaso za’a iya cin zabe, Kwankwaso ne Jagoran da zai rufe Ido aci zabe ta kowacce irin hanya.

Sun shirya Kutungwilar dasuka yaudari wani Jigo daga Siyasar Mundubawa sakamakon yarda da Aminci da kyautata zato dayayi musu.

Dayake Allah ba Azzalumin Sarki bane yau Mutanen nan sun jefa kansu a cikin tsaka mai wuya.

Suna da ‘Yanci a baya, yanzu sun maida kansu BAYI, sun fada kangin bautar Jar Hula, gashi kuma bautar ta tashi a banza babu biyan Bukata.

Allah yatabbatar musu Mulki nasa ne, kuma yana badashi ga wanda yaso a sanda yaso.

Haka kuma zamani yanuna musu Kwankwaso Karabiti kamar kowa in ba ya kan Kujerar Mulki, dama nasarar dasuke kalla yana da ita karfin kujerar Mulki ne kesa shi rufe Ido yayi karfa-karfar danne hakkin wasu.

Yanzu dai ta tabbata su Rogo da team disa sunyi Faduwar BAKAR TASA, don basuda wata kima da martaba cikin siyasar ‘Yan duniya da ‘Yan Addini.

Ina rokon Allah yakara durkusar da siyasar wadannan Mutanen.

Daga Umar Faruq Muhammad

Muna Taya Murna

Sen. Ibrahim Shekarau MEDIA

Yanzu haka muna SAS muna jiran sauran Kananan Hukumimi Hudu (4) Dala, Gwale, Kumbotso da Nassarawa kafin bayyana zaben Sanatan Kano me jiran rantsuwa a hukumance.

Ko shakka babu Al’ummar Jihar Kano munyi zabi nagari, mun zabi cancanta, mun zabi dattako, mun zabi alkhairi, mun zabi mutunci, mun zabi girmamawa, mun zabi karamci, mun zabi tsoron Allah

Muna taya Sanata Ibrahim Shekarau murnar wannan gagarimin zabe me cike da tarihi, inda Al’ummah suka fito kwai da kwarkwata domin yin zabe cikin mutunci da karamci da kwanciyar hankali.

Godiya ta musamman ga kwamishinan ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro yadda sukayi tsayuwar daka wajen kame da tsare dukkanin masu kawo tarzoma a tashoshin zabe.

Daga Na’Allah Raheemeeb

BAMBANCIN MUMBARIN HUDUBA DA NA MASU ASHARIYA

Shekaranjiya Juma’ah itace Jajiberin Zaben Shugaban kasa da Majalisar Dattawa data wakilai.

Mafi yawan Limaman Juma’ah sunyi amfani da Mumbarin su wajen kiran Al’umma suyi Nagartaccen zabe, sun siffanta irin Mutanen da yakamata a zaba.

AlhamdulilLah, alamu sun nuna tasirin Mumbarin su ya zarta na Masu Ashariyya, domin Mutane suna daukar irin hudubobin da Mallamai keyi.

Masu Ashariyya kuma sun fahimci tasirin Ashariyar su yana tsayawa ne kawai a Podium din su na Siyasa, sabanin Mumbarin Mallamai da tasirin sa ke aiki a Tashoshin zabe.

Daga Umar Faruq Muhammad

Kwankwasawa Sun Fara Tonon Sikili

Ba nine na fada ba, dayan nan ne ya fada

1. An baka naira milyan d’ai-d’ai ka bawa kowanne dan takarar majalisar jiha na jihar kano ka basu naira dubu dari biyar biyar

2 . An baka kabawa kowanne dan takarar majalisar wakilai milyan daya da rabi ka basu dubu dari bakwai da hamsin hamsin

3 .An baka kabawa kowanne dan takarar sanata milyan 3 ka basu milyan daya da dubu dari biyar biyar

4 .An baka milyoyin kudi dan daukar motocin zuwan Atiku ka rike kace da ‘yan takara susa kudin su su dauki motoci

5. An baka million 49 don aje taro sokoto ka kashe million 6 kacal ka tura sauran a aljihu

7. An baka manyan kudi dan ka raba zuwa kananan hukumomi amma ka kwashe

A lissafi yawan kudin da aka baka sun kai kowacce karamar hukuma ta sami million 30 amma ka kwashe kudin

A tawa karamar hukumar kudinda ka bawa gabadayan akwatuna sune naira dubu arba’in ,

Muna da akwatuna 155 gabadaya ,kudin akwatuna daya kamata a kashe sune naira milyan 62

A lalace muna sa ran za’a kashe koda naira million 25 ne, amma sai ka aiko da dubu 40 kacal

Da yardar Allah ka daina nasara a duk abinda kasa a gaba

“Jama’a Kwankwasawa fa sun soma ‘bara ,sun soma tonon silili da bankada ”

Daga Aminu Abba Mohd

SHEKARAU YA CI MAZAƁAR SA

Mazaɓar Sanata Mal. Ibrahim Shekarau

GIGINYU WARD
Mallam Ibrahim Shekarau’s polling unit

President:
APC 219
PDP :27

Senator
APC 188
PDP:84

Reps:
APC 148
PDP:108

AN KAYAR DA KWANWKASO A MAZAƁAR SA

Mazaɓar Tsohon Sanata Rabi’u Kwankwaso

KWANKWASO WARD
Rabi’u Musa Kwankwaso’s polling unit

Malamai Polling Unit 001

President
APC 538
PDP 140

Senate
APC 480
PDP 218

Reps
APC 519
PDP 310

Kamal A Baba

Idan Ma Banda Tsaurin Ido…..

Muna sa ran gobe In Sha Allah kamar e yanzu mun yi janaizar Kwankwasiyya a Jihar Kano. Inda Sanatocin mu guda uku duk zasu lashe zaben su, sannan yan majalisar taraiya su 24 suma tas zamuyi cinye du da Izinin Allah.

Kai idan ma banda tsaurin ido na yan Kwankwasiyya, ina Ali Madaki zai ja da Mai Girma tsohon Gwamna Kuma Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau? Ai wannan kamshin mutuwa Kwankwaso yaiwa Ali Madaki. Ga kuma tsohuwar zuma, tsohon Gwamna Sanata Kabiru Gaya wanda ya kawo wa Kano manya manyan aiyukan titi wasu an gama wasu ana kanyi? Ina zaka hada shi da bushashshen Rogo? Ta ina Ahmed Bichi zai kada Sanata mai turanci wanda baya tagumi a majalisa wato Sanata Barau Jibrin?

Ai ko ba’a gwada ba, Linzami yafi karfin bakin zakara.

A yan majalisar taraiyar APC ga irin su Hon Kawu Sumaila Waraka, ga Ronaldon Siyasa Hon Abdulmumin Kofa, ga Hon Abdullahi Mahmud Gaya kudi, ga Hon Goro wanda ya mamaye Fagge da Kewaye. Ga Yakudima Alheri ne a Dala, ga Hon Hafiz a Tarauni, ga uwa uba Jarumin maza Rt Hon Speaker Alhasan Rurum.

Gaskiya wannan shall din siyasa APC za tai wa Kwankwasiyya gobe da Yardar Allah. Tun yanzu ina san nai amfani da wannan dama na taya Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR murnar wannan gagarumar nasara kuma nai wa Kanawa Albishir da cewa In Sha Allah a zaben gwamna ma haka za muyi cinye du.

🎵 Ka bi Ubanka kai Abba, Baban Abba Ganduje. Kanawa sai Uban Abba. 🎵

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano.

Jumma’a Ranar Hutuce A Najeriya

#S4S2019

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware ranar Jumma’a 22/2/2019 ta zama ranar hutu ga ma’aikata domin su sami sukunin yin tafiya-tafiya zuwa garuruwansu su gudanar da zabe.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Ministan cikin gidan Danbazau wanda babban sakataren ma’aikatar Georgina Ehuriah ya wakilta.

A cewar Danbazau wannan hutu bai shafi ma’aikatan bankuna da kuma ma’aikata masu ayyuka na masamman ba, ya tabbatarwa da jama’a cewa, jami’an tsaro zasu tsare rayuwa da dukiyoyin al’ummah da ma bakin hauren da suka shigo domin sa ido a harkar zaben.

Daga Na’Allah Raheemeeb

Lambobin Jami’an Tsaro Na Katta-Kwana

#S4S2019

Rundinar ‘yan sandan Nigeria ta fitar da nambar wayoyi sashin Operation na rundinar ‘yan sandan Nigeria jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja wanda ‘yan Nigeria zasu kira domin isar da rahoton gaggawa akan barazanar tsaro da aka gani yayin gudanar da zabe a garuruwansu dake fadin tarayyar Nigeria

Ga nambar wayoyin jami’an ‘yan sanda masu mukamin Mukaddashi da Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda (DCPs/ACPs) wadanda suke jagorancin bangaren OPERATION a helkwatar rundunonin ‘yan sanda na jihohi 36 da birnin Tarayya Abuja kamar haka:

1- ABUJA: 08033002496
2- BAYELSA: 07031300557
3- KOGI: 08066002020
4- ADAMAWA: 08033454228
5- BAUCHI: 08037004504
6- DELTA: 08039718748
7- KEBBI: 08033187658
8- EBONYI: 08033138430
9- BENUE: 08033004406
10- AKWA IBOM: 08033098261
11- NASARAWA: 08033674240
12- KANO: 08035975219
13- NIGER: 08033025490
14- ZAMFARA: 08058036613
15- CROSS RIVER: 08036014140
16- EKITI: 08033432264
17- SOKOTO: 07061687138
18- LAGOS: 08073666666
19- KADUNA: 08081777095
20- ANAMBRA: 08036766461
21- ENUGU: 08034537136
22- ABIA: 08035888774
23- BORNO: 08068969292
24- YOBE: 08036434959
25- KATSINA: 08033113083
26- JIGAWA: 08060060064
27- GOMBE: 07038621264
28- ONDO: 08033281542
29- IMO: 08033911832/08074985926
30- KWARA: 08133480567
31- RIVERS: 08035873235
32- OSUN: 08136829534
33- SOKOTO: 08060674803
34- TARABA: 08036737929
35- OYO: 08023400797
36- EDO: 08033784327
37- OGUN: 08023433482

Jama’a ya kamata kowa ya dauki nambar wayan jiharsa ayi saving akan waya, da zaran anga wata barazana na tsaro a yayin gudanar da zabe a duk inda ake sai mutum ya kira nambar wayan jiharsa ya fadi inda barazanar take, nan take za’a turo mayakan ‘yan sanda domin su kawo agajin gaggawa, a taimaka a yada wannan sanarwan

Muna rokon Allah Ya sa ayi zabe lafiya a kammala ba tare da ko da jinin sauro ya zuba a dalilin zabeba

Daga Na’Allah Raheemeeb.

PDP Itace Matsalar Najeriya

1 – Sunce a lokacin da suka mikawa Buhari mulki a shekarar 2015 buhun shinkafa tana N8,500. Sun manta a lokacin da aka mika musu Mulki a shekarar 1999, buhun shinkafa tana N2,500.

2 – Sunce sun mikawa Buhari mulki litar petur tana naira 87. Sun manta an mika musu mulki a shekarar 1999 litar petur tana naira 11.

3 – sunce sun mikawa ‘Buhari mulki dala $1 yana daidai da naira 235. Sun manta an mika musu mulki a shekarar 1999 dala 1$ yana naira 20.

4 – Sunce sun mikawa Buhari mulki buhun siminti yana naira 2000. Sun manta an mika musu mulki siminti yana naira 400. Watau a takaice dai idan kana Neman international Me Renawa Jama’a Hankali da kaga dan PDP an gama. Wanda yayi shekara 16 yana tabka tdana’assa, wai shi ke zagin shekara uku, Allah ka taimaki Shugaba Buhari ka kare shi daga makircin makirai.- Allahumma Amin……

PDP Itace matsalar Nigeria

Daga Aminu Ali Kabara

Yau Na Hadu Da Kwankwasawa

Yau na hadu da kwankwaso a airport road na fito daga zungeru road , muka rankaya muka nausa zuwa junction na kings garden inda a nan wani mugun direba a cikin motoci masu yi masa rakiya yayi kokarin angaje ni gefe guda

Hhhhhh kai mugu bashi da kama, amma dai na tsira ne ba wai dan yaji tausayin dalibar da take bayan mashin dina ba sai dai dan dressing din da yaga nayi domin yayi zaton dan kwankwasiyya ne. Har jinjina yayi min da hannu

Ni kuwa nace kaga mugu da yasan Basardaune ne buge ni kawai zaiyi su tafi abin su

Daga Sani Adamu Hotoro

Wane Tanadi Arewa Tayi

Wane tanadi Arewa tayi domin ‘yan uwanmu dake kudu?

Labari yana nunawa cewa gwamnonin jihohin kudu maso gabas da manyan yan siyasa na yankin sun yi tanaji na Musamman domin samawa yan bangaren su motoci don su koma gida su yi zabe.

Abin da ake bukata ga kowa shi ne ya nuna PVC na wannan yankin kawai sai ya shiga mota kyauta daga gobe alhamis. Wannan tanadin an ce an yi shi ne a Lagos, Ibadan, Abuja, Kano da Kaduna.

Mu wane tanadi muka yi wa namu yan uwan da suke zaune a can kudu? Ko kuma bamu neman kuria a wajen su ne? Ina manyan yan siyasan mu su ke?

Mun zauna sai magana akan Ko ya kamata a bindige barayin akwati Ko bai kamata ba. Bamu da da wata magana sai yin raddi akan juna da bada labarin kanzon kurege. Malamai na addini sun kasa cewa komai sai dai tsinuwa da cewa wasu sun kafirta.
Haka za mu ci gaba da zama ba wata jagora sai dai son rai?

Bamu Amincewa Kowane Mutum Yin Aiki Da Na’urar Tantance Katin Zabe ba – Prof. Yakubu

#S4S2019

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Prof. Mahmood Yakubu ya sanar da manema labarai a yayin wata ganawa dasu cewa, ba gaskiya bane labaran dake zagayawa cewa, akwai wasu mutane daga wajen hukumar da aka amince su seta na’urar da take karanta katin zabe wato card reader.

Prof. Yakubu yayi wannan bayani ne yayin amsa tambaya daga wani dan jarida, inda yace, aikin rarrabawa da seta na’urar da kafata da sabuntata sun dogara ne kacokan akan jami’an hukumar zabe INEC kuma ba’a yadda wani ya aikata hakan ba sai jami’an hukumar.

A halin yanzu mun sami nasarar seta kashi 95% daga 100% inda ake sa ran karasa setawa gaba daya ya zuwa yau Laraba 20/2/2019

Daga Na’Allah Raheemeeb

Garuruwan Harbau Da Jangefe Za Su Amfana Da Dam

Aiki Aiki Aiki Aiki Aiki Aiki dai Engr Sani Bala

Idan baku manta ba dai Wakiln Kunchi Da Tsanyawa ya samarda Dam a garin #Danjaka dake karamar hukumar Kunchi da kuma garin Kwarwa dake karamar hukumar Tsanyawa

yadda ya saba to ya qara a yau 19/2/2019 mai gayya mai Aiki Honorable Dr. Engr Sani Bala Dan majalissar Tarayya mai wakiltar Tsanyawa da Kunchi kuma Dan takarar majalissar Tarayya a tutar jam’iyyar APC karo na biyu ya turo ma’aikatan aikin Dam da wakilansa domin su doba yadda za’a fara aiwatar da aikin Dam a Garin Harbau a karamar hukumar Tsanyawa da kuma garin #Jangefe dake a karamar hukumar Kunchi domin saukakawa al’ummar wannan garuruwa wahalar ruwan da suke fama da ita shekara da shekaru da kuma inganta noman rani a wannan yankuna.

wannan garuruwa sunnuna jin dadinsu da farin ciki a fili da kuma rokon ubangiji Allah ya maimaita mana wakilcin Engr Sani Bala 2019.

Sign…
Miko Abdulssalam Miko Tsanyawa Chairman #EngrSaniBalaSocialMediaTeam

Mu Tashi Mu Farka Domin Kare Kasarmu

#S4S2019

San zuciya, handama da babakere shine ya addabi Najeriya kuma yayi mata dabaibaiyi wajen rashin cigaban Kasar, wannan bayani ya fitowa ne daga bakin shugabannin kawo zaman lafiya na Kasa Gen. Abdussalami Abubakar (mai ritaya) da Bishop Mathew Hassan Kukah

A cewarsu, ya zama wajibi ga al’ummar Najeriya su kare dimokaradiyya, su rungumi gudanar da zabe a matsayin wata hanya ta zaben shugabanni na gari wadanda suka cancanta su shugabancesu.

Shugabannin sunyi wannan batu ne a yayin wata lacca mai lakani da Mu tashi mu farka domin kare kasarmu haka kuma sun duba yadda aka tsara zaben wannan shekara ta 2019 inda suka nuna damuwarsu ta yadda ake gudanar da zabe na rashin yin wani abin azo a gani game da cin zarafi da cin fuska da kona zuciya

Daga karshe sunyi addu’a Allah ya zaunar da Kasar mu lafiya ya yafe mana zunuban mu.

Daga Na’Allah Raheemeeb

Design a site like this with WordPress.com
Get started