
#S4S2019
‘Yan Najeriya na bukatar shugabanni masu kishin kasa masu tabbatar da an maido da zaman lafiya arziki da cigaba da walwala, ba zamu amince da komawa gidan jiya ba musamman a hannun mutanen da suka maida kasar baya.
Kowa ya sani cewa, Jam’iyyar PDP ta fito fili ta nemi afuwar Al’ummar Najeriya saboda sunsan irin ta’adin da suka aikata a Gwamnatin su, domin kuwa bahause yace idan ba rami mai ya kawo rami?
Lokaci bai yi ba da Jam’iyyar PDP zasu komo domin neman darewa kan kujerar mulkin Najeriya a halin yanzu, bayan shekaru hudu (4) kacal da barin kujerar, sunyi shekaru gona sha shida (16) suna yin abinda suka ga dama.
Don haka ‘yan Najeriya ba zasu amince a sake sayar musu da kadarorin da suka mallaka ba, a wancan lokacin ma haka suka sayarwa da kawunansu dukkanin albarkatun Najeriya daga su sai ‘ya’yansu, yanzu kuma suna so su sake samun irin waccan damar su karasamu shikenan mu zama bayin turawa, su kuma su tafi can da iyalansu suci gaba da hole rayuwarsu.
Sanin kowane cewa, dan takarar PDP ya sha alwashin sayar da matatun mai da muke dasu, sannan yayiwa kungiyoyin masu luwadu da madigo alkawarin basu damar cin karansu ba babbaka, duk kuwa da cewa addinan Musulunci da na Kiristoci sun hadu domin yakar wannan dabi’a, inda suka ki yadda ayi dokar a baya domin bada dama ga irin wannan fitsara da turawa ke kokarin shigo mana da ita, sai gashi mai neman shugabancin kasar a tutar Jam’iyyar PDP yace susha kuruminsu indai ya hau kujera zai basu dama.
Ya zama wajibi ga Musulmi da Kiristoci mu hada karfi wajen yakar masu kokarin maida hannun agogo baya.
Daga Na’Allah Raheemeeb







































hukumar ta Nasarawa itace mafi yawan kuri”u a duk Nigeria da kimanin kuri’a dubu dari hudu da uku, 403,000. Haka zalika karamar hukumar ta Nasarawa itace karamar hukumar Mataimakin Gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna, da tsohon Gwamna kuma dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya Mallam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, dan haka muma sa ran ita kadai zata bawa Gwamna Ganduje kuru’un da zasu sa ya linka sauran abokan hamaiyar sa.




You must be logged in to post a comment.