Hadurran Da Ke Addabarmu

#S4S2019

“Sanin kowa ne cewa, akwai neman gyara wajen yadda muke sarrafa ababan hawa, wadanda suka hada da motoci da babura da kekuna harma da tafiya a kasa akan titinanmu.

Haka kuma mun tashi mun tarar da al’adar tallace-tallace a Kasar Hausa. Kuma abin takaici shine ‘yanmata ne yawanci su ke fadawa cikin wannan musiba.

Bunkasar birane da canjin rayuwar al’ummah da hijira daga wuri zuwa wuri sun sa a yanzu dabi’ar talla tana jefa ‘ya’ya mata cikin hadarin gaske, wannan tasa yazama wajibi mu yi kokarinmu wajen ‘yantar da ‘ya’ya mata daga wannan musiba ta tallace-tallace domin su sami damar neman ilimi har zuwa mizanin da za su iya.” – H.E Mallam Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano)

Daga Na’Allah Raheemeeb

Dogaro Ga Allah, Jari

#S4S2019

“Ina so a ko da yaushe jama’a su rika tunawa cewa, kamar yadda Shari’ar Musulunci ta shimfida, manufarmu ita ce, ta inganta rayuwar ‘yan Adam domin su sami ‘yanci da dogaro da kai, maimakon tumasanci da yawon raraka da abubuwan da addinin Musulunci yayi hani dasu.

Wannan yunkuri yana daya daga cikin ayyukan da muke aiwatawa domin cimma wannan bukatu namu na inganta rayuwar dan Adam” – H.E Mallam Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano)

Daga Na’Allah Raheemeeb

Kawai Dai Ina Tambaya

#S4S2019

Ance Atiku Abubakar zai shigo Kano ranar Lahadi 10/02/2019 domin kaddamar da yakin neman zabe a karkashin Jam’iyyar sa ta PDP.

Babban abin tambaya anan shine, idan tawagarsa ta zo Kano ina so na san waye zai tarbeshi?

Ma’ana, kungiyar PDP ta su Amb, Aminu Wali ce me masaukinsa ko kuwa kungiyar Kwankwasiyya ce za ta saukeshi?

Mu jira lokaci ya tabbatar da wannan magana, shin Atiku zai sa alamar hular kwankwasawa ko kuma zai sa irin hular Kanawan Dabo?

Kowa dai ya san wadannan bangarori guda biyu da muka bayyana, ba za su iya hada hannu domin karbar bakon nasu ba, duk wanda yayi nasarar karbarsa daga cikin su, dayan kuwa za’a barshi da kumfar baki.

Daga Na’Allah Raheemeeb

Ginshikin Cigaba Yana Tare Da Zaman Lafiya

fb_img_1549005869487-1205144426.jpg

#S4S2019

“Ina so in jawo hankalinmu cewa, kokarin neman zaman lafiya da kyautatuwar al’ummah ba zai yi tasiri ba idan gwamnati da masu hannu da shuni suka yi biris da irin halin kaka-ni-ka-yi da jama’a suke ciki, rashin aikin yi, masamman a tsakankanin matasa, ba irin musibar da ba zai jawo ba.

Mun sani cewa, matasan da basu da aikin yi, da su ake amfani wajen ruruta wuta akan abin da bai taka kara ya karya ba. Gwamnati ta daina yin kunnen uwar shegu da ‘yan tsirarin mutanen da suke kokarin tayar da hankalin jama’ar Kano, a tabbatar an hukunta duk wanda ya yi kokarin kawo tarzoma da fitina a wannan Jihar tamu mai albarka.” – H.E Mallam Ibrahim Shekarau CON ( Sardaunan Kano)

Daga Na’Allah Raheemeeb

SANARWA TA MUSAMMAN

Mai girma Mal Ibrahim Shekarau yana farin cikin gayyatar dukkan Yan Social Media na Jam’iyyar APC musamman Kananan Hukumomi 15 na Mazabar Sanatan Kano ta Tsakiya wanda suka Kano Municipal Gwale Fagge Nasarawa Tarauni Kumbotso Ungogo Minjibir Madobi Kura Garun Malam Dawakin Kudu Warawa da Gezawa da kuma Dala ganawa ta musamman gobe Asabar da misalin karfe 11 na safe a dakin na Mundubawa Hafsat Hall. Sanarwa ce data shafi dukkan yan Social Media Masoya Sardauna da Jam’iyyar APC.

Allah bada ikon zuwa Amin.

Sanarwa
Nasir Harun Alfalaky Alkanawy
Secretary New Media Communication Directorate

Tsamar Nama – Ibrahim Z Bello Kura

OPERATION TSAMAR NAMA A MAZABAR ALI MADAKIN GINI.

Sakamakon hawan Arfan siyasa da jam’iyar APC ta yi jiya a Karamar Hukumar Dala, Mai Girma Gwamna Dr Abdullah Umar Ganduje OFR ya karbi Mallam Karibu Ibrahim shugaban Mazabar Yalwa dake karamar hukumar Dala wadda take mazabar dan taka karar Sanatan jam’iyar PDP na Kano ta tsakiya Ali Madakin Gini wanda kuma dan kwamitin tsare tsaren sa ne. Ya chanza sheka, ya koma tafiyar Gwamna Ganduje da jam’iyyar APC kuma ya keta katin sa na kungiyyar Kwankwasiyya, yan Guru Maharaja. Shugaban Operation Tsamar Nama kuma Mataimakin Gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya kuma bashi dabino Ajuwa, dan Madina domin karya makircin guru Maharaja.

Hassan Saad NA Le-le
Mas Lukman
Ahmad Alasan Kabo
Usman Izi Kura
Muhammad Uba Adam
Gamu Nan Bisa Kanku
Kuyiwa Kanku Kiyamullailin Siyasa
Alkiyamar Siyasarku ta Tsaya Chak

S4S Cikin Hotuna

Hon. Abdullahi Ahmad Tadada ya jagoranci Shugabanni da mambobin kungiyar nan ta #S4S2019 wacce tayi fice wajen tallata manufofin Maigirma Sanata mai jiran rantsuwa H.E Mallam Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano) zuwa gangamin taron yakin neman zabe da sada zumunci a kananan hukumomin Dala, Gwale da Municipal, Alhamis 7/2/2019

Daga Na’Allah Raheemeeb

Najeriyarmu A Yau – Daga Yaquba Ibrahim Hayin Nomau

WALLAHI ba kasar chena bache ALLAH kuwa ba amerika bache karfa kuyi zaton jamani ne ko engiland wlh ba indiya bane ,
,

n

an dai da kuke gani najeriya che ayau karkashin jagoranchin farin dattijo BABA BUHARI chigaba irinsa nafarko da kasarmu ta samu da sannu alkhairin baba zai game duk najeriya mudai tayashi da adu,a ALLAH yaqara dorashi kan makiyansa

Halin Mutum Jarinsa

#S4S2019

“Dole mu mike mu yi aiki tare domin mu yaki zalunci da zaman kashe wando da halin ko-in-kula, wadanda suka taru suka yi mana katutu a halin rayuwarmu ta yau.

Wadannan munanan dabi’u su suka kara habaka irin zaman kunci da jahilci da kokarin tada fitina da a yau muka sami kanmu a ciki, na tabbatar babu inda wadannan halaye za su kaimu.

Saboda haka, ina kira a garemu gaba daya, da mu tashi tsaye wajen cusa wa kanmu akidoji na kitki, kamar su hakuri, juriya, kaunar juna, neman halal, bin doka da oda da kuma uwa uba, tsoron Allah.

Daidaikun mutane da kungiyoyi a birane da kauyuka, dole kowa ya mike tsaye domin ya bada tasa gudunmawa wajen wannan kokarin na neman zaman lafiya da ci gaban Jihar Kano da Najeriya gaba daya” – H.E Mallam Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano)

Daga Na’Allah Raheemeeb

Gyara Kayan ka

Nafi Shekara Biyu Zuwa Uku Ina Wannan Nazarin da Bibiyar Comments a Social Media.

‘Yan kudancin Nigeria, Musulmin su da kiristocin su, ‘yan APC da ‘yan PDP, basu zagi da cin mutuncin Professor Yemi Osinbajo Koda ko sun saba masa a ra’ayi.

Kiristocin Nigeria tare da banbancin darikun su basa zagi da cin mutuncin Mathew Hassan Kukah, duk da cewa, da yawan su basa biyar sa sallah. Wannan shi ake cewa “Discipline”( not technical meaning).

Abin mamaki, anan Arewa musamman ta Musulmi, abu ne mai sauki Yaro dan kasa da shekara 30 ya zagi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alh. Atiku Abubakar, Dr. Ahmad Gummi, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ko wani daga cikin manyan Malamai ko Sarakuna, ko yayi masa cin zarafi don dai ya sabawa ra’ayin sa.

Babban abin lura anan shine, mutum biyu baza suyi sabani ba cewa, daga 1999 zuwa yanzu ‘yan kudu sun fimu cin gajiyar demokradiyya nesa ba kusa ba. Ashe ba zagi da cin mutuncin manya kesa a samu ba!!

Bayan Manzon Allah S. A. W. ba wanda biyar maganar sa ko ra’ayin sa yake tilas. Ra’ayin kowa ijtihadi ne, yakan yiyu ya zama daidai yakan yiyu ya zama kuskure. Amma rashin yarda da ra’ayin wani baya nufin sai kayi masa cin mutunci da cin zarafi.

Ina kira ga Musulmin Arewa musamman matasa da muji tsoron Allah, mu kama bakunan mu da hannayen mu daga cin mutuncin mutane musamman Wadanda Allah ya baiwa manyan shekaru da matsayi a cikin mu, dasunan sabanin ra’ayi. Wannan bai taba zama wayewa da ci gaba a kowane civilasation ba, haka kuma bazai taba zama addini ba.

Allah Ya dora mu a hanya madaidaiciya. Ameen.

*Dr. Jabir Sani Mai-hula.*

Mallam Kamaye – daga Usman Solo

Zuwa ga Yan uwana masoya Maigirma Malam Ibrahim Shekarau!!!

Naga wasunmu suna damuwa wai don yan Kwankwasiyya sunawa Sardauna laqabi da suna KAMAYE (Jarumin Dadin Kowa)… Ni a fahintata wannan ba abin damuwa bane illa alfahari.

Iya sanina Mal. Kamaye mutum ne mai Gaskiya da Rikon Amana, Mai Hakuri da inda ya tsinci kansa, Mai tawakali… Kuma mutum ne mai fikira azancensa, ga hangen nesa da kira a aikata gaskia. Matsalar sa itace talauci wanda Allah ya jarrabeshi dashi, kuma yaci jarabawar sa kasan cewar bai zurmu da son duniya ya fada aikata wani mugun hali ba. To saboda Allah menene banbancin SHEKARAU da KAMAYE?

Duk abin dana lissafa na KAMAYE haka shima SHEKARAU yake, duk cikin manyan yan siyasar Nigeria babu talaka kamar Mal. Shekarau saboda baici kudin yan fansho ba, baici kudin local govt ba, babu wani abu daya taba cewa ya nutse a ruwa ko awani waje, yayi mulkin shi yagama lafiya baici dukiyar Kanawa ba. Ya hakura da inda Allah ya ajiyeshi baice lalle sai ya mallaki katafaren gidan gona a wani gari ba, bai siye gidajen makotansa ya hada ya gine su cikin gidan saba. Ya iya talaucin sa.

Ya Yan uwana Sardaunawa ina kira da kukarbi kyautar girmamawar nan da Yan KWANKWASIYYA sukayiwa Jagoranmu… SHEKARAU/KAMAYE! Alh. Buba zasuce mana mu daga hankalin mu.😂🤣😂

FAHIMTA TA CE inji Umar Faruq Muhammad

FAHIMTATA CE 

 

Jihadi ne Maigirma ga Kanawa suyi yunkurin kawar da Kungiyar Kwankwasiyya cikin siyasar Kano.

 

Dalilai na

Kungiyar tayi kaurin suna wajen koyawa yara rashin kunya da kausasa harshe ga Shugabanni.

 

In kana sauraren shirin siyasar Rediyo zakaji mafi yawan Kalmomin rashin ladabi suna fita ne daga bakin Kwankwasiyya

 

Shugabansu Katobara, Mabiyan sa Tsageranci.

 

Muhada Kai mukauda wadannan miyagun Ta’adu.fb_img_1549218672241346219121.jpg

ZAMAN LAFIYA YAFI ZAMA ‘DAN SARKI

“Rashin zaman lafiya baya cikin tsari na dimokaradiyya, haka kuma baya cikin tsarin addinin Allah.

Addinin Musulunci ya yi tir da duk wani tsarin da ya amince da kisan kai da kwace da kuma kone-konen dukiyoyin bayin Allah.

‘Yan siyasa da shugabannin addini da sarakan gargajiya da ‘yan kasuwa da mata da matasa da ‘yan uwanmu mazauna Kano, ina kira a garemu gaba daya da mu yi kokarin fahimtar junammu, mu zauna da juna cikin kauna da lumana.

Ta haka ne kurum za mu iya yakar illolin da suka addabemu; kuma ta hakane za mu iya sake gina harsashin dawo da halayenmu na zaman lafiya da hakuri da juriya da kuma kaunar kasa, wadanda mutanen Kano suka yi fice akansu.” – H.E Mallam Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano)

Daga Na’Allah Raheemeeb

BANBANCIN SHEKARAU DA SAURAN daga Bello Muhammad Sharada

Shekarau yana cikin mutum 30 da hukumar zabe INEC ta kasa ta sahalewa ya tsaya takarar sanata a Kano ta tsakiya. Yana takara ne a jam’iyyar APC mai alamar tsintsiya.

Mallam Ibrahim Shekarau yana da bambanci da sauran masu takara, a fuskoki guda bakwai.

Shekarau malamin makaranta ne. A tarihin siyasar Najeriya, masu kwarewa a fanni biyar ne suke kan gaba. Malaman makaranta sune farko, domin da Sardaunan Sakkwato da Tafawa Balewa da Aminu Kano da Shehu Shagari duk malaman makaranta ne. Sai lauyoyi su Awolowo, sai ‘yan jarida da marubuta su Nnamdi Azikwe, sai masu damara irinsu MD Yusuf, sannan ma’aikatan gwamnati ‘yan admin. Kano Central ta yi sanatoci guda biyar, cikinsu babu malamin makaranta. Duk masu neman wannan kujera a yau a duk jam’iyyun babu malamin makarantar da ya kai Shekarau. In akwai a fada mini.

ta biyu, Shekarau tsohon ma’aikacin gwamnati ne, wanda ya kure wa aikin maleji. Ya san ciki da bayan aikin gwamnati, babu a inda za a layance masa. Cikin masu neman wannan kujera babu wanda ya taka wannan matsayin. Abin sha’awa Shekarau ya zauna da kantoman soja da gwamnonin farar hula amma, ya gama aiki ba a taba tuhumarsa da kowacce irin almundahana. A masu neman babu mai wannan shaidar.

na uku, Shekarau ya yi gwamnan Kano shekara takwas a jere. Duk jinsin mutanen Kano babu wanda ya yi kuka da shi. A lokacin da ya yi gwamna kudi tsaba na mutanen jihar Kano naira biliyan 582 suka biyo ta hannunsa, aka yi amfani da su don al’umma amma bai dauki sisin kwabo ba ta haramtacciyar hanya. Cikin masu neman wannan kujera babu wanda ya taba yi gwamna. Mutum daya ne cikinsu ya rike kananan hukumomi 15, dayan kuma a inda yake warkajaminsa a karamar hukuma ce kwaya daya jallin jal. Babu hadi a tsakanin wanda ya yi gwamnan Kano Ta Dabo, Jallabar Hausa da sauran.

Na hudu, Shekarau ya taba zama zababben dan takarar shugaban kasa na jam’iyya ta kasa a shekarar 2011. A zaben ya samu kuri’a dubu 900. Wannan yana nuna ko ina a fadin Najeriya, Shekarau yana da jama’a. Wannan matsayin da ya kai ne aka yi shirin gidan talabijin na BBC HardTalk da shi, sannan ya shiga muhawar ‘yan takarar shugaban kasa da gidan talabijin na NN24 suka shirya har ya zama zakara. A cikin wadanda suke neman wakilcin mutanen Kano Central babu wanda ya taka wannan matakin. KO AKWAI? Ku ce mini babu.

Da Shekarau aka yankewa jam’iyyar APC cibiya, kuma da shi aka yanka mata ragon suna. APC ita ce jam’iyya ta ‘yan hamayya ta farko a tarihin Najeriya da ta kafa mulki. Ya san kowa a cikinta, kowa kuma ya san shi. Da ya shiga jam’iyyar PDP tare da shi da Sanata Ike Ekweremadu suka yi aikin yi wa PDP gyaran fuska da saita ta bisa turba. A lokacin da yana gwamna shi ne kadai gwamnan da bai yi canjin sheka ba ya tsaya daram a jam’iyyarsa ta ANPP. Duk masu takarar Sanata Kano Central babu mai wannan gogewar.

yi.ministan ilimin tarayyar Najeriya na tsawon wata goma. Ma’aikatar ilimi ita tafi kowacce ma’aikata girma da fadi da kwaramnniya. Shi ne.mutum.na farko wanda ba Farfesa da ya rike ma’aikatar a tarihi kuma ya yi abin kirki. Ku fada a cikin masu neman wannan kujerar sanata, wa ya yi ko da ministan sati ne? BABU KAWAI

In kun cire suk abubuwan nan guda shida, ina son ku gaya min mai shiga sabgar jama’a a cikin maneman kujerar, ina nufin yaje daurin aure da janaza da ta’aziyya da duba maras lafiya. Akwai limami cikinsu?
Wane a cikinsu ke daukar waya da amsa tes, ya saurari tsoho da tsohuwa da yaro. Waye mai tausayi da jinkai da hakuri da yafiya, cikakken dan dimokuradiyya? Waye cikinsu zaka ao neman naira dari ya baka 200?

Zaka iya gaya masa kowanne suna Duna, Kamaye, Wakilin Arna, Yaci kudin Makamai, Dan ci da addini ko.Mayaudari koMatsoraci, IYAKARTA KENAN

AMMA Wadannan abubuwan shi ne bambancin Shekarau da sauran. Me wannan gogewar da banbamcin shi ya kamata mu aika wakilci a majalisar dattawan Najeriya

TALLA NAKE YI: KUMA BAN YI KARYA BA

Mayaudaran ‘yan siyasa sun fara shigowa cikin al’ummah da sunan taimako a garesu

Al’ummah da ‘yan siyasar Jihar Kano sun dade da wayewa masamman a fagen al’amuran yau da kullun dake faruwa a farfajiyar Najeriya dama Duniya bakidaya, idan mukayi duba na tsanaki zamu gane haka ta yadda jama’a suka waye wajen sauraron labaran duniya a radio da karanta jaridu, mujallu da kuma kallon tashoshin talabijin.

Kasar Najeriya babu wata kabila da zata kama kafar hausawan Jihar Kano a wannan fagen na fahimtar inda duniya tasa gaba a harkokin yau da kullun. Wannan ita ce tasa muka gane ‘yan siyasa ma yaudara da kuma masu fatan taimakawa al’ummah, wadanda idan an kira sunayensu za kaji ana sanya mu su albarka da kuma wadanda ake tsinewa saboda irin wahalar da talakawa suka dandana a hannunsu lokacin da suka mulkemu.

Kuma ba sa tunawa damu sai lokacin da wata dama ta neman kuri’ar mu ta taso, domin yaudara zakagansu suna kuka da hawaye wai suna tausaya mana, a hannu guda kuma suna bamu hakuri cewa sunsan basuyi mana daidai ba amma yanzu sunzo ne domin su bamu hakuri, za su gyara barnar da sukayi a baya, haka kuma zama gansu da dan wani hasafi wanda bai taka kara ya karya ba duk saboda yaudara.

kara tunasar daku abinda kuka dade da sani cewa, duk abinda sukazo dashi hakkinkune da suka zalinceku suka tara, daga su sai iyalinsu, shine suka dan tsakuro abinda bai wuce suba almajirai ba domin su baku da nufin ku sake dangwala musu damar darewa kan madafun iko, yadda zasu sake danne dukiyar da Allah yabamu domin mu amfana wajen more rayuwa.

kira gareku, idan sun fito da ita sun baku ku karba, kuma kuzabi cancanta kuzabi wanda bazai danne dukiyarku ba, kuzabi wanda yasan mutuncinku, kuzabi wanda yake kallonku kamar iyayensa ko yayyansa ko kannansa ko yayansa.

Daga Na’Allah Raheemeeb

KUJERAR SANATAN KANO TA TSAKIYA daga Aminu Ibrahim Dabo

Kujerar sanatan kano ta tsakiya, kujera ce mai matukar muhimmanci a majalisar dattawan najeriya kuma duk wanda zai je kan wannan kujera ana buqatar mutum mai daraja da dattako da cikakken hankali da ilimi mai zurfi wanda idan yayi magana zai dauki hankalin al,ummar kasa bakidaya. domin majalisa ba waje ne na hargowa da hayaniya ba, dan haka mai girma sardaunan kano shine wanda ya cancanta da ya zama wakilin al,ummar kano ta tsakiya a waccar majalisa mai albarka. don haka DAN TSAMAGE NA DALA wannan kujera tafi karfinka domin ba nanaye da dora gilas a karan hanci ake buqata ba.

An Aje Kwarya A Gurbinta Daga Muzammil Mandawari

Sanya sunan Alh Aminu Dantata a Gadar sama ta Murtala Muhammad way da sunan marigayi Alh Tijjani Hashim Galadiman Kano a underpass ta Kofar ruwa abune daya dace kuma yayi daidai duba da irin gudunmawarsu ga alummar jahar Kano da Jihar baki daya an ajiye kwarya a gurbinta

Tabbas dole na yabawa Gwamnan Kano Ganduje wajen girmama sunan Kano elders, duba da gwamnatocin baya da aka dinga sanyawa gadoji sunan gwarawa da garori, gaskia Ganduje ka Kyauta a wannan Fanni kuma dole a yaba Maka

Wannan raayina ne ba siyasa ba.

Labarai Cikin Hotuna Daga Shamsu Maishadda

Waddannan kadan daga cikin kananan hukumomin da muke halarta. Inshaa Allahu APC zamu ci zabe 019 .mu bama alfahari kuma ko bamu taru a inec sakamako zai fito mun lashe zabe a fadin jihar kano da kasa baki daya.

Manufarmu

#S4S2019

Kowa ya sani cewa gini baya zama mai nagarta saboda kyakkyawar filasta ko kyale-kyalen da aka yi masa daga waje; yana zama mai nagarta ne kawai ta hanyar harsashi mai karfi da aka assasa masa.

Haka ma al’ummah ba za ta zama mai karfi, mai kwarjini, mai arziki kuma abar sha’awa ba, sai tana shigar da kyawawan dabi’u cikin zukatan ‘ya’yanta. Kokarinmu na gina al’ummarmu akan hanya ingantacciya shine manufarmu – H.E Malam Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano)

Daga Na’Allah Raheemeeb

Mikiya Hangen Nesa

THE MISSION kamar kullun jiya a rally na Kumbotso Wanda shugabanta na jahar kano ya jagoran ta Alh. Dahiru G. Shekarau. Allah kaba Shekarau Senator, Abdullahi Umar Ganduje da Buhari Su maimaita Amin.

#S4S2019

Kai Tsaye Daga Gidan Gwamnatin Jihar Kano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR yayi Kurunkus, Inda da yammacin nan ya jagoran ci Tawagarsa da tahada da Mataimakin Gwamna Dr Nasir Yusuf Gawuna, Tsohon Gwamna Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau,Shugaban jam’iyar APC Abdullahi Abbas Sanusi,babban Daraktan yakin Neman zaben Gwamna Alhaji Nasiru Aliko koki. Zuwa Gidan Tsohon Mataimakin Gwamna Farfesa. Hafiz Abubakar MFR dake Unguwar Jan bulo dan Sada Zumunci.

Uba Danzainab
Special Adviser New Media,
Goverment House Kano.
03/02/19.

Kumbotso ta dinke

#S4S2019

03/02/2019

DUBBAN ‘YAN KUNGIYAR KWANKWASIYYA NE SUKA JEFAR DA JAJAYEN TAGIYOYINSU DOMIN KOMAWA JAM’IYYAR APC A KUMBOTSO

Bayan da Maigirma Gwamnan Kano Dr Umar Abdullahi Ganduje da Maigirma Mallam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) da sauran ‘yan tawagarsu sun kai ziyarar neman zabe a karamar hukumar Kumbotso.

Wasu dubban ‘yan Jam’iyyar PDP Kwankwasiyya sun dangwarar da shahadarsu, kuma sundawo Jam’iyyar APC, wadannan mutane sun hada da mata da maza, matasa da dattijai.

Sunyi alkawarin bada gudunmawa domin kafa sabuwar gwamnatin APC me mutunci a karkashin Gwamna Ganduje

Haroun Shekaran Gama

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN.

Yanzun nan nake samun labarin cewar ‘yankwankwasiyya suna zarewa mutane karfe suna kwace musu wayoyi da kudade a rallyn da suke yi yanzu haka a karamar hukumar Dala.

Muna rokon Allah ya kare dukkan aluma daga wannan halayya tasu. Ya Allag ka hanasu dawowa mulkin jihar Kano don kada su halasta mana fashi,sutale da satar baburan aluma

A Daidaita Sahu

#S4S2019

Idan har ya zuwa yau akwai wadanda ba su fahimci manufarmu ta A Daidaita Sahu ba, to a taikaice manufar ita ce Gwamnati ta jagoranci jama’a domin bude sabon babin alkhairi a cikin rayuwar al’ummah bakin daya.

Tunaninmu shine, cikin amincewar Allah (SWT) da kuma goyon bayan jama’armu bakin daya, mu gina al’ummah ta gari wadda take a tsaye wajen kulawa da addini, wadda kuma za ta zabura wajen neman na kai, da kare mutunci, da kuma kulawa da kyakkyawar zamantakewa – H.E Mallam Ibrahim Shekarau CON (Saradaunan Kano)

Daga Na’Allah Raheemeeb

Nura Sani Jibrin Gwagwarwa

INNAH LILLAHI WAINNAH ILLAIHIR RAJUUN!
NACIKA DA MAMAKI AKAN ABINDA MALAM IBRAHIM SHEKARAU YAYI.

Cikin wani yanayi naban mamaki tareda alhini Wanda masu iya karatun turanci da rubuntun turanci kan Kira (surprised) ko (marvellous)

Haduwarmu keda wuya yayin isarda sakon da megidana ya turani jahar jigawa dutse, a tashar mota a yau,

Sainaji ance salam alaikum, na amsa da waalaikassalam, dan Allah Abokina ko kaine Nura sani jibrin Gwagwarwa, Sardaunan matasan Gwagwarwa,? Nace kusan hakanne Amma meyasa kake tambaya Nura Sani Jibrin Gwagwarwa ko yayi maka laifi ne?

Sam ko kusa kawai ina kaunarsa kamar yadda yake kaunar Sardaunan Kano, kuma na dogara da shafukansa wajen sanin dukkan ababan daya shafi harkar siyar Gidan Sardaunan Kano dama jahar Kano baki daya kasan yanda yake tiri tiri da kare dukkan wani abu da zaimanto ya danganci Sardaunan Kano,

Nace hakane? Yace eh wallahi dan haka nake son Zama aminin sa ta kowace hanya.

Rufe bakinsa keda wuya Sai wata Baiwar Allah tace Kamar kuna maganar Mal Ibarahim shekarau?

Nace hakane hirar sa mukeyi.

GYARA ZAMA KUSHA LABARI.

Acewar wan nan baiwar Allah ashekara ta 2006 tashiga cikin masifa da Balai irin Wanda bata taba ganin irinsaba, Amma sakamakon Mal Ibrahim shekarau ta fita ta numfasa saita fashe da kuka tareda adduoi kamar haka,

Allah yanda Mal Ibrahim shekarau yashare Mana hawaye kashare Masa nasa Nace Amin.
Allah ka suturtashi kamar yanda ya suturtamu Nace Amin
Tace ubangiji ina tawwsali da dukkan wani aiki danayi ka karba daka biya dukkan wani Abu da Mal Ibrahim shekarau zainema a gurinka ka biya Masa Nace Amin.
Allah karabashi da duniya lafiya shida dukkan makusancin shi Nace Amin.

Uhmn! Tacigaba kamar haka, a wan nan shekarar Munkasance a gidan gadon mijina wanda su biyu sukayi tarayyah akai,

Bayan tsawon shekaru mun hayay yafa harshi megidana takaiga karfisa yayi kasa kwatsam sai dan uwansa dasuke ciki daya yakaishi kotu domin araba gado kokuma ayi sulhun gado musaya afiddashi,

Abu kamar wasa akai cinikin gurin Naira Miliyan daya da dubu dari bakawai, mukayi alqawarin biyan kudin Amma Kash Allah bai hore manaba,

Ga Yara har Guda Tara gashi Abinda zamuci shikansa kullum sai a hankali domin dreba ne megidana a lokacin Babu mota han nunshi.

Na rasa Abinda yake min Dadi kawai saina yanke shawara Koda zan mutu zanje gidan Gwamnati bakuma zandawoba Koda kwana nawa zanyi tunda naji yanda Gwamna yake taimakawa alumma Ina sa ran wataqil in an isar da sakon mu ya iya biya mana koda kudin hayane mu koma kafin asaida gidan.

Zuwana gidan Gwamnati keda wuya Sai maaikatan tsaro suka hanani shiga Tareda kiranada mahaukaciya magan ganu kala kala kin dauka Gwamna kamar kene duk lokacin da ake so zaa Ganshi? Wasu masu hankali naban shawara inje radio anacikn haka saiga wani Bawan Allah yafito daga cikin gidan Gwamnati a motarsa zaifita.

Sai shi wan nan mutum ya tsaya dukkan ma aikatan suka juya da kiransa ranka yadade wani kusadani Naji yace S.A. dayan Kuma yace Yarima ne.

Bayan ya saurari dukkan abinda ke tafe dani yana Shirin fara yimin magana sai wayarsa irin Mai Budewar nan tayi Rin sainaji yana cewa ok sir yes sir ina gate, sai yacemin toke bari an kirani Amma kijirani tukun muga ta Ina zamu bullowa lamarin, yabawa jamian tsaron ummarni da su bani guri in jira shi.

Bayan yashga kamar da Minti 30 sainaga yafito tareda tambaya a Ina gidan yake Kuma inshirya mutafi Allah yadubi zuciyata,

Kiran da akaimasa Maigirma Gwamna ne yakirashi domin bashi wasu ayyuka, shine yake tambayarsa dama baka fitaba kenan? Nace Masa nazo fita amma ga Abinda ya dakatar Dani, yanaji haka sai shi Gwamna yace nawa ne kudin gida nagaya Masa Miliyan daya da dubu dari bakawai, Abin mamaki sai yace Ina zuwa yashiga cikin dakinsa ya dauko Naira Miliyan Biyu Tareda umartata da muje asiyi Gidan in dam ka miki takardun gidan Kuma in baku ragowar dubu dari uku kuyi gyare gyare da siyan kayan Abinci kuyi zaman ku.

Hakan Kuma akayi, mukaje yasamana gidan a ranar akabamu takar dunmu aka Kuma bamu ragowar kudin shikansa wallahi ko Naira bai cire ba haka ya wanzar da abinda aka Dora Masa.

Dan haka Nida yayana da megidana baza mudaina yima Sardaunan Kano Kuma sanatan Gobe danizinin Allah Mal Ibrahim shekarau adduaba har iya karshen rayuwar mu inshallah.

Hakan yasa matsayina na Masoyinsa Mai kaunarsa duda Ana kokarin rabamu dashi na gabyadace in bada lokacina tunanina fahimtata in Kara fitoda kyawawan halayen sa,

Hakika Ina alfaharin da samun jagora Abin sawa agaba ayi tun kaho dashi Sardaunan Kano Mal Ibrahim shekarau.

Daga
Nura sani jibrin Gwagwarwa
Sardaunan matasan Gwagwarwa.
Masoyin Sardaunan Kano idan har baa Rabamuba.

Kuhuta lafiya.

Sannu Da Zuwa Kumbotso

GENERAL COORDINATOR TEAM CAMPAING KUMBOTSO NA MAIGIRMA SARDAUNA,

HON FATIHU UBA SA’AD

Yana kiraga Daukacin Al ummar kumbotso masoya maigirma SARDAUNA da maigirma GWAMNAN jahar kano,

Kuma yana maraba da Zuwan masu Girma

H,E DR, MAL IBRAHIM SHEKARAU
SANATAN KANO TA TSAKIYA 2019,

TARE DA MAIGIRMA GWAMNA KANO 4+4

DR, ABDULLAHI UMAR GANDUJE 4+4=8

Zuwa karamar Hukumar kumbotso Domin gangamin taron kaddamar da Takara A jam’iyyarmu Ta APC SAK Sama da kasa,

Wanda za’ayi kamar haka :-
Rana :- LAHADI 3/2/2019
Wuri :- Cikin garin kumbotso primary School

Allah yabada ikon zuwa Amin,

Announcer_______
Coordinator General Team Campaign Kumbotso
HON FATIHU UBA SA’AD

# S4S2019 SOCIAL MEDIA TEAM CAMPAING KUMBOTSO

Labarai da dumi-duminsu

Jam’iyyar PDP tayi kira ga hukumar zabe da ta haramtawa shugaba Buhari shiga takarar zabe ranar 16/02/2019.

Wannan ya biyo bayan gangamin taron yakin neman zabe da shugaba Buhari ya gudanar a Kano ranar Alhamis 31/01/2019 wanda ya dauki hankali yan adawa, inda Jam’iyyar PDP ke zargin kasar Niger da shigowa domin kawo mutanen su domin taimakawa Buhari yaci zabe.

Kamar yadda labari ya iske mu, mai taimakawa gwamnan Kano ta fuskar yada labarai Alh Salihu Tanko Yakasai ya tura da hotunan gwamnonin kasar Niger akan shafin sa na twitter yayin da suka kawo ziyara fadar gwamnatin Kano a daidai lokacin da Shugaba Buhari ke shirin sauka a Kanon Dabo

Yanzu abin jira mugani shine, ko hukumar zaben zata dauki matakin haramtawa Shugaba Buhari shiga takarar zaben na 2019

Canjin Sheka

Jam’iyyar APC a Jihar Gombe tayi babban kamu inda ta cafko Daraktan yakin neman zabe na Jam’iyyar PDP Alhaji Bala Bello Tinka

Wannan magana ta fito daga bakin fadar shugaba Buhari inda ya gana dashi a jiya Alhamis a fadar gwamnatinsa

APC SOCIAL MEDIA TEAM KANO STATE

Gyara kayanka dan,uwa

Akwai rayuwa bayan zabe. Kar ka bari harkar siyasa ta hada ka rigima da wani. Kayi siyasa mai tsafta cikin mutunci da girmama juna. Ka girmama ra’ayin wanin ka shima ya girmama naka.

Ta’addanci da bangar siyasa bata dace da duk mutum mai hankali ba, kar ka bari wani dan siyasa yayi amfani da kai wajen tayar da tarzoma a cikin al’umma. Kar kayi zaton ‘yan siyasa suna amfani da kai ne don ci gaban kasar ka, suna amfani da kai ne su mulke ka don jin dadin rayuwar su.

ALLAH Ya ba mu ikon gyarawa Ya bamu Shugabanni nagari masu kishin mu. Juma,at kareem

Nasir Harun Alfalaky Alkanawy

KO KUN SAN???

Ko kun san kafin zuwan Malam Ibrahim Shekarau Gwamnan jihar Kano, babu wani abu da ake kira CONSTITUENCY PROJECT?

Sardaunan Kano shine ya fara kirkiro constituency projects don kyautata alakar Majalisa da bangaren Zartarwa.

Obasanjo shine ya fara kwaikwaya, yanzu kuma kowace jiha tana yin hakan.

Mai wannan basirar yana bukatar kuri’armu don zama Sanatan tsakiyar Kano.

Muzabi Sardaunan Kano don samun constituency projects ingantattu.

Juma’at Mubarak, Insha Allah

Design a site like this with WordPress.com
Get started