PDP DA APC A KANO CENTRAL
Hukumar zabe ta kasa wato INEC, ta saka ranar Asabat 16 ga Fabrairu 2019 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben Sanata a Kano ta Tsakiya.
A wannan ranar za a hada wa mutum takardar zabe guda uku. Ta shugaban kasa wacce zai zabi shugaba Muhammadu Buhari ko waninsa, sai kuma ta Sanata wacce zai zabi Mallam Ibrahim Shekarau, ko waninsa. Sannan ta dan majalisar tarayya.
A Kano ta tsakiya akwai kananan hukumomi 15. Sune: Dala da Gwale da Nassarawa da Kumbotso da Kano Municipal da Tarauni da Ungoggo da Minjibir da Gezawa da Warawa da Dawakin Kudu da Kura da Madobi da Garun Mallam da Fagge. Duk wanda yake da kuri’a a wadannan kanananan hukumomi zai zabi Shekarau ko wani a matsayin sanata.
Yawan masu neman kujerar majalisar dattijai a Kano Central 30 ne a jam’iyyu 30. A cikinsu akwai mata uku da maza 27.Mutum uku cikinsu sun haura shekaru 60, biyar sun haura shekaru 50, sauran duka kasa da 50 suke, mafi kankantar shekaru a cikinsu shi ne Shehu Munzali dan jam’iyyar AGA shekararsa 33.
Manyan jam’iyyun da za a buga da su sune APDA wacce Muhammadu Abacha yake neman gwamna a cikinta. Sai APC mai dan takara tsohon gwamna Shekarau, sai PDP mai Ali Madakin Gini, dan majalisar tarayya mai ci daga Dala, sai PRP mai Sanata Rufa’i Sani Hanga.
Da Hajiya Laila Buhari da Ali Madaki da Shekarau da Sanata Rufa’i duk ‘yan cikin kwaryar birnin Kano ne.
Hukumar zabe ta yi wa mutum miliyan uku a Kano Central rijista. Akwai mazabu 172 a Kano Central, sannan akwai akwatunan zabe dubu 3713. A zabukan da aka yi a baya, na shekarar 1999 wanda ya yi nasara dan jam’iyyar PDP ne marigayi Kura Mohammed da kuri’a 193,895, wanda ya yi nasara a 2003 Sanata Rufa’i Hanga ya ci da kuri’a 288,708 a jam’iyyar ANPP, a 2007 Sanata Muhammad Bello ne ya wakilci Kano Central bayan ya lashe a ANPP da kuri’a 542,477, a 2011 Sanata Lado ne ya yi nasara da kuri’a 359,050 a jamiyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi yake kan kujerar Kano central a majalisar dattiji bayan ya samu kuri’a 758, 383. Kwankwaso ne aka fi samun mafi yawan kuri’a a zabensa a cikin zabuka biyar da aka yi a Kano Central.
Yanzu zabe ya sake zagayowa, a ganina, wannan zaben za a yi shi ne a tsakanin Hon. Ali Madaki na PDP da Mallam Ibrahim Shekarau na APC, Madugun Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa ne ya tsayar da Ali Madaki, ita kuma APC ta baiwa Shekarau. Sauran jam’iyyu duk rakiya za su yi. Amma Allah ne mafi sani. A siyasa komai yana iya faruwa.
Tsayar da Ali Madaki yana daga cikin ragon azanci da Kwankwaso ya yi wa Dala da Kano. A majalisar tarayya tun daga shekarar 2011 Ali Madaki yana kokari, yana wakilci mai ma’ana, bai kamata rana tsaka a hankadar da shi daga kujerar ba. Shekarunsa ba su kure ba kuma ya fara zama dattijo a majalisar tarayya mai hawa biyu. Zai fi bada gudunmawa in ya ci gaba a wannan kujerar. Kano tana bukatar ‘yan majalisar tarayya gogaggu da sanatoci kwararru don bada wakilci mai nagarta da mutunci.
Yadda ya kamata shi ne mutanen Kano Central su zabi Mallam Ibrahim Shekarau ya maye gurbin kujerar Kwankwaso. Dattijo ne, majalisar ta dattijai ce, zai tarar da abokan aiki da yawa da ya sansu suka san shi, da za su hada gwiwa don taimakon Najeriya da mutanen Kano da Kano Central. Ya dace, ya cancanta kuma zai iya wakilci, saboda guri ne na lallami da lumana da saukin kai da tsantsar dimokuradiyya da bani-in-baka, duk ya iya su. Guri ne da ake tashi a yi bayani a gamsar da saura, Shekarau ya iya. Majalisa dakin doka da ka’ida ne, al’adarsa ce. Wakilin da zai wakilcin kwaryar birnin Kano ya zama wanda za a rika ganinsa ne a Abuja, sannan lokaci-lokaci zai zo Kano, hadimin al’umma da zai saurari koke ya kai gaba, sannan ya san halayyar mutanensa sarai. Duka Shekarau ya hada su.
A Kano Central a yi APC, a yi Shekarau, shi ne farar dabara.
NA BAR KU LAFIYA

You must be logged in to post a comment.