Tuni Aka Fara Fita Tour,A Shirye Shiryen Zaben 2019.Abun Duba Da Jin Dadi Shine,Yadda A Kowacce Karamar Hukumar Da Akaje,Sai Jagorori Sun Ziyarchi Fadar Hakimin Wannan Karamar Hukumar. Wanda Yana Nuna Irin Girmamawa Da Ake Yiwa Masarauta.
Ziyartar Masarautu Da Akeyi,Anayi Ne Domin Kara Bayyanawa Al’Umma Cewa Su Iyaye Ne Da Ake Son Mu Dinga Girmamawa.Kuma Wannan Ziyara Ana Kaiwa Ne,Dan Sanya Albarka Ga Wannan Shugabanin Namu.
Muna Godiya Ga Allah Da Ya Hada Mu Da Jagorori Na Gari,Ya Bamu Nasara A Zaben 2019.
Haka Zalika A Fitar Da Ake Ana Karbar Yan P.D.P Da Yan Kwankwasiyya.Dan Haka Muke Sanar Da Ku Cewa,Anyiwa P.D.P Tumbur A Jihar Kano.
Dan Haka Mutanen Kano Sunce Sai Baba Buhari, Baba Ganduje,Da Baba Shekarau. A.P.C Daga Sama Har Kasa.
Abdullahi Ahmad Tadada
Chairman #S4S
Dan Kwamatin Yada Labarai Na Buhari/Ganduje
DALILIN DAYASA RABIU KWANKWASO BAI SAKE NEMAN TAKARA BA A ZABEN 2019
KWAMISHINAN YADA LABARAI NA JIHAR KANO MALLAM MUHAMMAD GARBA
Dalilin da yasa tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai sake tsayawa takara ba shine tsoron shan kayi a hannun a tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, kamar yadda gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana.
Kwamishinan yada labaran gwamnan jahar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 20 ga watan Janairu, inda yace Kwankwaso ya ji tsoron kada Shekarau ya kunyatashi ne yasa bai sake neman tsayawa takarar Sanata a zaben 2019 ba.
Malam Muhammad Garba ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a gangamin yakin neman zaben Ganduje daya gudana a karamar hukumar Karaye ta jahar Kano, inda ya bayyana Kwankwaso a matsayin ‘Kararre’, wanda bashi da wata sauran tasiri a siyasar Kano.
“Sanata Kwankwaso ya fahimci tabbas idan ya tsaya takara da Shekarau zai sha kunya, don haka yasa yayi yan dabaru ya janye daga tsayawa, domin ya san babu makawa sai Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya kayar da shi.
“Idan baku manta ba Shekarau ya yi ma Kwankwaso jina jina a zabukan 2003 da 2007, inda ya kayar dashi a zaben gwamna a 2003, sa’annan ya kayar da dan takararsa a yayin zaben gwamna na shekarar 2007.” Inji shi.
Bugu da kari, Garba yace irin kalaman da Kwankwaso ke furtawa a yayin kamfe ya nuna cewar bashi da masaniyar sauyin da aka samu a siyasar jahar Kano, kuma kalamai ne irin na wanda ya riga ya san ba zai ci zabe ba.
“Zaizayewar Kwankwasiyya, da kuma yadda jigoginta suke ficewa daga cikinta suna dawowa cikin jam’iyyarmu mai albarka, jam’iyyar APC ya nuna cewa mun kayar da Kwankwaso da dan takararsa na gwamna tun ma kafin a kada kuri’a.” Inji shi.
Local Government Chairman Punished After Shouting APC At PDP Rally
Sakon Girmamawa Zuwa Ga Masoya #S4S
Salam, Barka da warhaka, tareda fatan kana cikin koshin lfy
Chairman #S4S2019 na jiha Abdullahi Ahmad Tadada ya umarceni na mika godiya gareka da jinjinar girmamawa, masamman yadda kake bunkasa tafiyar Sardaunan Kano dakuma kungiyar #S4S2019
- Allah yakara basira, yabamu nasara a duk inda muka tsinci kanmu.
HATTARA
Komai yana da ka’ida, komai yana da lokacinsa, yanzu lokacine na zaben Maigirma Mallam Ibrahim Shekarau a majalisar dattawa ta kasa.
Hakane zai bada dama ga sauran bangarorin Najeriya su kara fahimtar nagarta, dattako, kwazo, jajircewa da kuma fasaharsa.
#S4S2019
DANBATTA/MAKODA APC CAMPAIGN
YAU MUN BUNNE P.D.P DA KWANKWASSIYYA A DANBATTA / MAKODA.
GOBE ZAMU YI JANAZAR P.D.P DA KWANKWASSIYYA A ROGO/KARAYE.
KANO TA GANDUJE CE.
NAJERIYA SAI BABA BUHARI.
#S4S2019
The Journey Begins
Thanks for joining me!
Good company in a journey makes the way seem shorter. — Ibrahim Ali Ahmad


You must be logged in to post a comment.