Sakon barka da jummah daga Sen Ibrahim Shekarau Media

#SHEKARAU4SENATOR (#S4S).

Kungiyar Shekarau4Senator karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada yauma kamar kowace juma’a tana yiwa dukkannin yan’uwa musulmi barka da juma’a da kuma fatan alheri. Da addu’a ga Ubangiji (S.W.A) mai kowa mai komai wanda baya bukatar wani abu a wajen kowa saidai kai ka nema a wajensa. Da ya yaye mana wannan annobar ta Covid -19 a jihar nan tamu ta Kanon Dabo da kasarmu ta najeriya da duk fadin duniyan nan.

Wayanda suka kamu da ita kuma Allah (S.W.A) ya basu lafiya. Mu kuma da bamu kamu ba Allah ya dada karemu. Allah ya bamu ikon cin wannan jarabawa dan alfarmar Annabi da alkur’ani.

Sako daga kungiyar

#Shekarau4Senator (#S4S),
17/04/2020.

Defeat COVID-19 Campaign, Sponsored by (S4S)

A press statement issued by the commissioner for Information and member of the committee, Malam Muhammad Garba indicated that Senator representing Kano North, Senator Barau Jibrin donated the sum of N4, 000, 000.00 million, while Senators Ibrahim Shekarau and Kabiru Gaya representing Kano Central and Kano South respectively contributed N2, 000,000 each

Shekarau4Senator (S4S)

Sen Ibrahim Shekarau da sauran Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya na Kano sun kai gaisuwa ga sarakunan Kano da Bichi

A yau Litinin 23/3/2020, Mai girma Sardaunan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau, ya jagoranci sauran sanatocin Kano ta Arewa, Kano ta Kudu tare da ‘yan majalisar Tarayya masu wakiltar Jihar Kano.

Zuwa taya murna ga Mai Martaba Sarki Kano Alh Aminu Ado Bayero da Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Nasiru Ado Bayero bisa tabbatar dasu a matsayin Sarakuna.

Allah ya yi jagora, ya karawa Mai Girma Sardauna Lafiya.

SHEKARAU4SENATOR (S4S)

Sen Ibrahim Shekarau ya halarci taron Shukhurah

A Yammancin rana Lahadi, 15 Maris,2020.
Mai Girma Sanatan Kano ta tsakiya Dakta Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya halarci taron Shukhurah walima na MSSN reshen Jahar Kano tare da karrama wasu daga cikin manyan baki.

SHEKARAU4SENATOR (S4S)

Sen Ibrahim Shekarau ya kai gaisuwa ga Sarkin Kano

A wannan rana ta Asabar 14/03/2020. Mai Girma Sardaunan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau yake gaisuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero.


Haka kuma makarantar Mal Aminu Kano School ff Legal Studies ta karrama Mai Girma Sardaunan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau, da lambar girma, saboda gudunmawar da ya bawa harkar Ilimi a rayuwar sa.
Allah ya kara daukaka da sutura.

SHEKARAU4SENATOR S4S

Sen Shekarau ya halarci taron liyafar mai sharia Bulkacuwa

Sanatan Kano ta tsakiya Malam Dr. Ibrahim Shekarau CON, ya halarci taron bikin kammala aikin shugabar kotunan daukaka kara ta kasa Zainab Bulkacuwa bayan ta cika shekara 60 a duniya.

Daga cikin manyan bakin da suka halarta akwai Mataimakin Shugaban Kasa Professor Yemi Osinbajo, gwamnoni, sanatoci da yan majalisar tarayya.


Ciki har da mai girma gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.


SHEKARAU4SENATOR (S4S)

EFCC na tuhumar Rabi’u Musa kwankwaso da wasu mutane biyu da danne kudin makamai #35bn

Hukumar EFCC na tuhumar tsohon gwamna kuma tsohon sanata Rabi’u Musa kwankwaso tare da wasu mutane biyu da yin ruf da ciki da kudadaen makamai har naira biliyan talatin da biyar (#35bn).

Tun bayan barin sa mulki, Rabi’u Musa kwankwaso yana shan kalubale daban-daban inda ake zargin sa da danne kudaden da aka bashi amana, masamman kudaden ‘yan fansho wanda tsohon gwamna kuma sanata mai ci a halin yanzu Sen Ibrahim Shekarau yace, yabar kimanin naira biliyan goma (#10bn) a asusun ‘yan fansho kuma sunyi batan dabo, harma yake shawartar ‘yan fansho su tuhumi Rabi’u Musa kwankwaso inda ya kai musu kudaden nasu.

Biri yayi kama da mutum, domin kuwa har zuwa yanzu ma’aikatan da suka bar aiki, suna fama da matsalar samun hakkokin su a Kano sakamakon wawashe kudaden da ake zargin tsohon gwamna Rabi’u Musa kwankwaso yayi.

Koma dai me ake ciki, zamuji inda gizo ke saka.

#SenIbrahimShekarauMedia

BA’A FITAR DA RAI DA RAHAMAR ALLAH

Daga Shehun Dashi:

Idan banda haka da sai ince baza’a sake yin Gwamnan da zai ya da arziki a cikin al’ummarsa kamar Mallam Ibrahim Shekarau

Sakon ta’aziyya ga coordinator S4S Gwale LG

A madadin shugabani da magoya bayan kungiyar Shekarau 4 SENATOR (S4S)

Muna mika sakon ta’aziyarmu ga dan uwa abokin gwagwarmaya Hon Yusif Ibrahim Mandawari, kuma coordinator na (S4S) Gwale LG, bisa rasuwar kanwar mahaifiyar sa.


Muna rokon Allah ya gafarta mata, yasa Aljannatul Firdausi makormar ta, ya bada hakurin rashin ta.


Sako daga kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S)

Sen Ibrahim Shekarau zai bayar da jarin dubu goma

Daga Uzairu Hassan Hussain:

A matsayi na na dan kasuwa nasani kuma ina ganin masu sana’ar da jarin su bai wuce dubu biyu ba 2,000,
Akwai wadanda ma basu da jarin ko sisi amma suna Sana’ar,

Misali a kasuwanni irin sabon gari, kasuwar wambai akwai yan kasuwar da suke zuwa shaguna su karbi kaya su tallata idan yamma tayi abinda suka sayar su dawo wa da me shago sauran kaya sannan su bashi kudin abinda suka sayar su kwashi ribar su,

Mafi yawan masu abincin sayarwa basu da jari suma,
Dayawa suna karbo kayan bashi ne wake shinkafa kayan miya harma da nama idan suka gama cin kasuwar yau washe gari su biya na jiya su dauki wani,

To kenan idan marar jari zaiyi kasuwanci kenan in kabasu koda dubu biyar 5,000 ne zasu yi harka.

To kenan indai za’a iya sana’a babu jari me zai hana me jari yayi in aka kara masa?

Kada hassada ta hanaku ganin alkhairin Sanetor Sardaunan Kano.

#SenIbrahimShekarauMedia

Innalillahi wa’inna illahir rajiun

SHEKARAU 4 SENATOR (S4S)


Innalillahi Wa’Innalillahi Rajiun

Allah yayi wa mahaifin abokin mu, dan gwagwarmaya, Jibril Muhammad Na Tara, Sardaunan K/Goje rasuwa.

Allah ya gafarta masa, yasa aljannatul firdausi makomar sa, ya bada hakurin rashin sa, da dukkan musulmi baki daya.


Sako daga Kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S)

Muna yiwa Dr Umar Mustapha fatan alkhairi

Kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S) tana yi wa DG Campaign na Sen Ibrahim Shekarau Dr Umar Mustapha Mai Mentholatum fatan alkhairi.

Sako daga (S4S)

Sakon barka da jummah daga Shekarau 4 Senator S4S

SHEKARAU 4 SENATOR S4S:


Muna yiwa dukkan musulmi barka da jummah. Allah ya karbi ibadun mu da adduo’in mu, ya jikan magabatan mu, ya bamu lafiya da zama lafiya.


Haka kuma, muna rokon Allah ya karawa jagoran mu Mal Dr Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) Sanata Kano ta tsakiya lafiya da karfin gwuiwa na ci gaba da taimakon al’ummar sa da addininin sa.


BARKAN MU DA JUMMAH
Sako daga Kungiyar Shekarau 4 senator (S4S)

Tina baya

Sen Ibrahim Shekarau ya nuna gwanancewa wajen gudanar da mulki yayin da cikin sa’oi 24 ya sasanta tsakanin makiyaya da manoma kamar yadda ya sasanta rikicin yajin aikin malaman jami’oi cikin sa’oi 24 daga rantsar daahi a matsayin ministan ilimi a shekarar 2015

S4S

Wane mataki ya kamata Sen Ibrahim Shekarau ya dauka

Idan kai ne Sen Ibrahim Shekarau, wane mataki za ka dauka akan kazafin da wasu mutane su ka yi maka na kisan Sheikh Jafar Mahmud Adam, sakamako yadda gaskiya ta bayyana, wadan da suka kashe shi sun yi furuci da bakin su a halin yanzu?

#SenIbrahimShekarauMedia

YABON GWANI YA ZAMA DOLE

Daga Alkalamin Uztazai:

Yau alkalaminmu zaiyi yabone ga jagora kuma jigo na tafiyar S4S na jihar kano baki daya, wato Hon Abdullahi Ahmad Tadada

Bawan Allah hakika ka cancanci yabo da jinjina, domin Allah kadai yasan irin soyayyar dake tsakaninka da sardaunan kano, tsakaninka dashi akwai soyayya gami da girmamawa.

Kayimasa hidima kayi masa biyayya sannan ka doramu akan layin yimasa hidima da kyautata zato a koda yaushe, Hakika ka cancanta a jinjina maka akuma yaba maka bisa namijin kokari da kakeyi wajen tsaftace tafiyar gidan sardaunan kano.

Hakika munayimaka kallon copy na sardaunan kano domin duk yanayin salo da dabi’unsa kayo gado, ka gaji tarbiyya ta siyasa agurin jagora, tabbas kai mutumin kirki ne.

Baka da girman kai
Baka da Raini
Baka da dabi’ar danne nakasa
Sannan gaka jagoran tafiyar S4S

Tabbas idan ka tabashi tamkar ka taba TeamUstazai ne

Allah ubangiji sa ya saka maka da mafificin alkhairi yakawomaka babban rabo mai albarka.

ALKALAMIN USTAZAI
15-02-2020

Shirye-shiryen taya murna ga Sen Ibrahim Shekarau

Daga (S4S):

Tuni shirye-shirye sunyi nisa na cikar mai girma Sardaunan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Mal Dr Ibrahim Shekarau murnar cikar sa shekaru goma da nada shi sarautar Sardaunan Kano.

Wanda kuma shine Sardauna na farko a Jihar Kano.
Muna rokon Allah ya jikan mai martaba Sarkin Kano Alh Dr Ado Bayero, ya jikan Sarki Alhaji da mai babban daki.

Allah ya karawa mai girma Sardauna lafiya, yasa ayi taro lafiya a gama lafiya.

Sakon fatan alkhairi daga kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S)

Daga Jihar Cross Rivers Laraba, 12 February, 2020

SHEKARAU 4 SENATOR

Mai Girma Sanatan Kano ta tsakiya Dakta Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya halarci taron bita na kwana uku akan dabarun tsara hanyoyin biyan albashi na kasa tare da Hukumar Kula da albashin ma’aikata ta kasa a Calabar jihar Cross Rivers a Kudancin Najeriya.

Mr Ag Ekpo Nta shine Shugaban Hukumar (Esq) wanda tsohon shugaban ICPC ne.

(S4S)

KANO CENTRAL: Kayan Kamfani daban dana Shago

Daga Umar Faruq Muhammad:

Kwanakin baya nayi rubuce-rubuce game da Yadda Sanatan Tsakiyar Kano Mal. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano yayi Ganawa da Shugabannin Kananan Hukumomi, Shugabannin APC na Kano Central, Shugabannin Jam’iyya na Kananan Hukumomi da Kodinetocin sa duk a Shirye-shiryen sa na kyautatawa wadanda yake wakilta.

A jiya Sardaunan Kano yakaddamar da kwamitin da zai Jagoranci bada tallafi ga masu Kananan sana’o’i Mutum 2000 daga Mazabu 172 dayake wakilta.

Wannan ne karon farko da Tsakiyar Kano tasamu Wakilin da yasan cewa wadanda suka zabe shi suna da hakki a abinda yake samu.

Sardaunan Kano ya yarda shi Sanatan tsakiyar Kano ne ba sanatan Neman suna a Arewa ba.

Allah yasa layar ta cigaba da kyan rufi.

#SenIbrahimShekarauMrdia

Sen Ibrahim Shekarau ya nada kwamatin cikar sa shekaru 10 da zama Sardauna

Maigirma Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya kaddamar da kwamitin Bikin cikarsa shekaru Goma 10 da Sarautar SARDAUNAN KANO.

Wannan kwamiti mai mutane 17 yana karkashin kulawar
1. GARBA Yusuf Abubakar (Garba Izala) Comm Chair.
2. Hon. GARBA Zumbur Rano
3. Hon. MUSA Sulaiman Shanono
4. Alh. SHEHU Yusuf Yakasai
5. Alh. DAUDA Raula
6. AUWALU Ibrahim DanZabuwa
7. Alh. IBRAHIM Mai Atampa
8. Alh. BALARABE Muhammad
9. Hon. AHMAD S Aruwa
10. Hon. KABIRU Bello Dandago
11. Dr SULE Yau Sule
12. Alh. NASIRU Dikko
13. AUWAL Muazu Kwalwa
14. MALLAM Sagiru TWada
15. YAKUBU Lawan Yarima
16. P’A. AHMAD Sulaiman
17. Mal. Bello Muhammad Sharada Committee Secretary

#SenIbrahimShekarauMedia

Saurari hira ta masamman tare da Sen Ibrahim Shekarau

Ranar Lahadi 9/2/2020 za ayi hira ta masamman da tsohon gwamnan jihar Kano, tsohon ministan ilimi kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu haka.

Sen Ibrahim Shekarau CON (Sardaunan Kano) da misalin karfe 10 na dare zuwa 12 na dare a Rahama Radio.

Karku manta da ranar Lahadi, 9/2/2020, 10 na dare zuwa 12 na dare a Rahama Rado

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau daga majalisa

SHEKARAU 4 SENATOR S4S

Masha Allah, muna kara godiya ga Allah da yasa muka zabi Jam’iyar APC. Domin a dalilin haka Al’ummar Kano ta tsakiya suka zabi malami, masani, jarumi tsayayyan jagora, a kujerar Sanatan Kano ta tsakiya.

Domin Samun kyakkyawan wakilci, saboda haka ya kai kudiri, ya goyi bayan kudirin. Ya gabatar da bukatun al’umar kasa, jiharsa da mazabar sa.

Tabbas zaben da Kano ta tsakiya ta yiwa mai girma Sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano anyi zaben nagari, jajirtacen wakili.

Shine shugaban Kwamatin Public Services Na Majalisar Dattawa, wanda nan bada dadewa ba yan Pension zasu dara godiya ga Allah, tare da godiya ga wannan jarimin mutum managarci yadda yake kokarin kwato musu hakkinsu.

Daga karshe muna rokon Allah ya kara masa lafiya, daukaka, juriya da dauriya. Tare da abokan aikinsa baki daya. Allah ya kara taimakon jam’iyar A. P. C.

Sako Daga

SHEKARAU4SENATOR (S4S),

Sen Ibrahim Shekarau ya kai ziyarar bazata

Shekarau 4 Senator (S4S)

Daren Litinin 10:18pm an hango Sanatan Kano ta Tsakiya Mal Ibrahim Shekarau ya kai ziyarar bazata a cikin daya daga asibitocin Kano Muhammad Abdullahi wase specialist Hospital (Asibitin Nassarawa) yana zaga dakuna yana duba marasa lafiya.

Photo :- Abadulkarim Badamasi

Shekarau 4 Senator S4S ta yi rawar gani

SHEKARAU 4 SENATOR (S4S)

A Madadin shugabani da magoya bayan Kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S)

Muna mika sakon godiyar mu ga Allah da kuma shugabanin Kungiyar Shekarau 4 Senator S4S na mazabar Tudun Wazirchi, bisa siyan tankin ruwa, da suka yi, dan ci gaban al’umar mazabar.

Allah ya saka muku da alheri, ya kara daukaka da sutura.
Allah ya taimaki mai girma Sardaunan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau.

Sako daga S4S

A madadin Sen Ibrahim Shekarau S4S na mika sakon ta’aziyya

A madadin jagororin kungiyar SHEKARAU4SENATOR (S4S) karkashin Alh. Salisu Indabawa da kuma Alh. Haruna Muhammad Gama (Garkuwar Sardaunan Kano) da kuma shugaban ta na jiha Abdullahi Ahmad tare da dukkannin membobin ta.

Mu na amfani da wannan dama domin mika sakon ta’aziyyar mu ga Engr. kuma SA na mai girma gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a kan kasuwanci Mamuda Sani Madakin Gini bisa rasuwar mahaifiyar sa.

Allah Ubangiji (S.W.A) ya jikan ta ya gafarta mata ya yafe mata kusakuran ta ya sada ta da Manzon tsira (S.A.W). Ya jikan iyayen mu da dukkannin yan’uwa musulmi da suka riga mu gidan gaskiya tin daga lokacin Annabi Adamu (A.S) zuwa yau din nan.

Mu kuma idan tamu tazo yasa mu cika da imani.

Sako Daga

SHEKARAU4SENATOR (S4S)
02/02/2020.

Sen Ibrahim Shekarau ya jagoranci taya Ganduje murna

SHEKARAU 4 SENATOR S4S
A yammacin wannan rana ta Asabar 1/2/2020 Mai Girma Sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya shugabanci taron taya Mai Girma zababben Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam, murnar samun nasarar da yayi a kotun koli.

Allah ya kara lafiya da daukaka Mai Girma Sardaunan Kano.

Sako Daga S4S

KOWA DA RABON DA ALLAH YA RUBUTA MASA

Daga Umar Faruq Muhammad:

A shekarar 2002/03 damu akayi Gwagwarmayar nemawa Mal. Shekarau Gwamna, bayan yawon Kamfen mune muka kasa muka tsare Akwatinan zabe.

Da Allah yabada Nasara Mallamin ya nada wadanda Allah ya tsaga da rabon su manyan Mukamai, a ciki harda Kwamishina Kafi Gwamna dakuma Fulagan Gwamnatin.

A damar da Mutanen can suka samu sun gina kansu sun gina ‘YA’YANSU, sun tura ‘Ya’yansu karatu kasashen waje, sun kuma kafa Kamfanonin neman Masarufi.

Bayan faduwar Gwamnatin a 2011 dayawan su komawa gefe sukayi suka rufe bakunan su, mudin da bamu ci Kwabo a Gwamnatin ba mune muka dage a Facebook muna kona datar mu muna kare Gwamnatin dasuka tsotse romon dimukuradiyyar ta.

2014 kaddara ta maida mu PDP, Shekarau yasamu kyakykyawar karba har ya rabauta da kujerar Minister, Mutanen dasuka mori Gwamnatin dai sune suka kara morar wannan romon na PDP.

Rabon sune Allah yarubuta musu,.

Akan me zaku damu kanku idan Dan cikin Jagoran daya zama silar Arzikin wadancan shima yau rabo yaratso ta kansa?

Dama ai haka Rayuwar take, In an jika hagu sai a jika hannun dama.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sakon taya murna ga Sen Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano

SHEKARAU 4 SENATOR (S4S)

A madadin shugabanni da magoya bayan Kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S)

Muna taya mai girma Sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, murnar cika shekara goma da nada shi a matsayin Sardaunan Kano na farko a jihar Kano.

Allah ya kara jagora da daukaka.

Haka kuma, muna kara rokon Allah ya gafartawa marigayi mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Dr Ado Bayero, yasa yana Aljannatul Firdausi makormasa, ya jikan dukkan musulmi baki daya.

Idan ba’a manta ba a ranar 22/1/2010 marigayi mai martaba sarkin Kano Alh Dr Ado Bayero ya nada Mal Dr Ibrahim Shekarau a sarautar Sardaunan Kano.

Allah ya kara masa lafiya da sutura. Barka da Juma’a.

Sako Daga (S4S)

Sen Ibrahim Shekarau ya karbi bakuncin dattijan siyasar Kano

Yau Alhamis 30/1/2020

Mai girma sanatan Kano ta tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, ya karbi bakuncin mai baiwa Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam shawara akan harkokin komai da ruwanka (Special Adviser on Special Duties) Alh Hamza Usman Darma tare da daya daga cikin manyan ‘yan siyasar Jihar Kano Alh Dauda Raula.

Wanda suka ziyarce shi a ofishin sa na majalisa.
Allah ya kara zumunci da daukaka.

SHEKARAU 4 SENATOR (S4S)

Sen Ibrahim Shekarau yayin tattaunawa da ‘Yan kwamitin sa

Mai Girma Sanatan Kano ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, tare da ‘yan kwamatin sa na Majalisar Dattawa, suke tattance sunayen da Mai Girma Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ya gabatarwa da Majalisa na Ma’aikatan Majalisar.

Wato National Assembly Service Commission.
Allah ya taimaki Mai Girma Sardaunan Kano.

Sako Daga S4S

Design a site like this with WordPress.com
Get started