
Mun sami labarin kotun sauraron koke-koken zabe na gwamna a Jihar Kano ta tsayar da ranar Laraba domin yanke hukunci.
#SenIbrahimShekarauMedia
s4s.home.blog

Mun sami labarin kotun sauraron koke-koken zabe na gwamna a Jihar Kano ta tsayar da ranar Laraba domin yanke hukunci.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Datti Assalafiy:

Dakarun Sojin Nigeria sun samu nasaran katse mummunan harin ta’addanci wanda annoba ‘yan ta’addan Boko Haram suka kaddamar a sassa dabam na jihar Borno tun daga jiya juma’a a tsakanin garuruwan Gajiram, Banki da Jiddari Polo
Adadi mai yawa na ‘yan ta’addan Boko Haram sun bakunci lahira babu shiri, wanda zuwa yanzu ba’a kai ga tattara mushen gawarwakinsu ba

Na fitar muku da wasu hotuna da zasu iya bayyana saboda ka’idojin facebook, Boko Haram sun hadu da mummunan kisan wulakanci, hakika wannan karon ba ta zo wa ‘yan ta’addan da sa’a ba
Jinjina ga sojojin kundunbala, aci gaba da gashi tunda ba zasu tuba ba!
Muna rokon Allah Ya tabbatar da cikakken nasara ga sojojin Kasarmu Nigeria akan yakin da suke tsakaninsu da Boko Haram
#SenIbrahimShekarauMedia

Kungiyar Shekaru4Senator S4S karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada tana mika sakon taya murna ga daya daga cikin ‘ya’yanta Hassan Sani Gidan Fulani murnar fita daga cikin gwagware inda ya angwance a wannan rana ta Lahadi 29/9/2019.

Muna addu’a a garesu shi da amaryarsa, Allah ya sa albarka a cikin auran, yabada zaman lafiya, ya hire masa yadda zai kula da gidansa.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Sulaiman Muhammad Yakasai

Malam Ibrahim Shekarau mutum ne wanda ya taso a gidan tarbiyya shiyasa idan ka zauna dashi zaka koyi abubuwa da yawan gaske. Hakan ne yasa zaka ga yawancin magoya bayansa su ma sun koyi wasu daga cikin kyawawan halayensa.
A zaben 2011 lokacin da Malam Ibrahim Shekarau yake takarar shugaban kasa akwai wani babban malami da ya fito yace bazasu goyi takarar Shekarau ba, dalilinsa shine yace ” Malam Shekarau yan izala kadai ya taimakawa a gwamnatinsa kuma yan izala suna kafirta su, dan haka dasu zabe shi gara su zabi arne” duk da yake akwai hujjoji da zaa iya nunawa wajen qalubalantar wannan Malami , amma Malam Shekarau ya hana duk wani magoyin bayansa mayarwa da wannan Malami martani dalilin da ya bayar shine ” yace dan Adam ajizine Malam yana iya yin dai dai yana iya yin ba dai dai ba, maganarsa bazata hana hukuncin Ubangiji ba”
Da ace jagorori zasu yi koyi da irin wannan halaye da ba’a samu rashin tarbiyyar da ake samu yanzu ba duk inda wani yake nuna kiyayya a gareka bazai hana hukuncin da Allah yayi a gareka ba.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Sani Haruna Gilashi

Al-‘umar Kasar nan Suna Cigaba da Nuna Al-‘hininsu Da Bacin Rai Dangane da Cin Mutuncin Da Mabiya Kwankwasiyya Suka yiwa Malamin Adinin muslunci Kuma Minister Shaik Isa Ali pantami
A filin Sauka Da tashin Jiragen Sama Na Mal.Aminu Kano.
Yanzu haka jama’a Naci Gaba da Allah wadarai da Wannan Al-amari Inda wasu daga cikin Mabiya kwankwasiyyar Suke ficewa da Kungiyar yayin da Suke Cewa kungiyar tana Barazana ga tarbiyar matasa.
Allah ka Dauramu Akan Dai-dai.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Haroun Shekaran Gama:

Nifa tun ranar da mutanen banzan nan suka jibge ni a Durba hotel ana gobe Inconclusive na kara tabbatar da cewa basu da mutunci kuma basu gaji mutunci ba.
Mutanen nan basu kalli daraja ta ta malamin makaranta ba, basu kalla darajar gemu na ba, basu kalli darajar zamantakewa ba, basu kalli cewar idan kaine yau gobe ba kai bane.
Abinda zai baka mamaki shine wallahi harda wani babba a cikinsu wanda nake tunanin ko gani yayi ana duka na zaiyi iya yinsa wajen ganin ya kwace ni, amma abin mamaki wallahi shine ma ya debo yaran suna bi daki daki suna neman inda nake basu san na lafe a wani waje ba.
In takaice muku sai da ta kai hatta masu gadin Hotel din sai da suka hausu da duka wai sai sun fito dani sun kashe ni.
Wani yaro da na ganshi da wata tsitaka yana kokarin soka min na daga cikin mutanen da BILLAHIL AZIM bazan taba yafe musu ba, kuma matukar Kere na yawo Zabo ma yawo zamu hadu kuma daukar fansa babu fashi.
Hausawa suka ce fashi barnar aiki, kowa ya gaji bai saba ba.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Umar Faruq Muhammad:

Jiya wasu Gafalallu daga mabiya Aqidar Kwankwasiyya sun tozarta Jihar Kano a Idon duniya yayin rakiyar Daliban dazasu fitar kasar Hindu.
Duniya tasan Kano cibiya ce ta Mutunta Ilmin Addini da Ma’abota Addini, amma Jiya Kwankwasiyya sun zubar mana da wannan kima tamu ta hanyar cin zarafin Minista Mal.. Famtami saboda yafadi Gaskiya a wani Karatun sa, gaskiyar dasuka fifita Jagoran su akan su karbeta.
Matsalar da Kwankwaso yashigo da ita a Siyasar Kano da Nijeriya shine, indai baka hada ra’ayin siyasa dashi ba ko kuma baka goyon bayan sa to Kai Makiyi ne, shikuwa Makiyi ba cin zarafi ba ai har jinin sa ana iya zubarwa.
A wurin Kwankwasawa irin su Daurawa ne kawai Mallamai masu Daraja, tunda basuyi suka akan kalaman Madugu da suke cike da Kuskure ba a addinance.
Hakika masu wannan Akida cikin Kwankwasiyya sune MATSALAR SIYASAR KANO, sune suke maida sabanin siyasa zuwa Kiyayya.
Ba duk aka taru aka zama daya ba, akwai tsirarun Kwankwasawa da basa tare da wannan mummunan ra’ayin, ina rokon Allah yaraba Nagari da Mugu!
SenIbrahimShekarauMedia
Daga Jamilu Away Mai Jakai:

A fahimtar Madugun Kwankwasiyya Ba’a Aikin Alkhairi Sai Lokacin Zaman Banza.
Shi Kuma Mallam Ibrahim Shekarau Fahimtarsa Shine Lokacin Dakake Da Aiki Lokacin NE Yafi Dacewa Kamaida Hankali Wajen Aikin Alkhairi Saboda Yafi Falala Da Lada
Dan haka yake zuwa gidan Mutuwa, Daurin Aure, duba Marasa lafiya
Yana Gwamna da kuma yanxu dayake matsayin Sanata.
Allah yasaka masa da gidan Aljanna

Munga shima azahirin Kwankwaso lokacin yana Gwamna da sanda yake Sanata babu ruwan-sa da zuwa Daurin Aure, Ta’aziyya, ko duba Marasa Lafiya.
Da mukai magana yan darikar kwankwasiyya suka ce yana da aikinyi shiyasa baya zuwa
Yanxu babu aikinyi yadawo zuwa ta’aziyya.
Muna rokon Allah yadauwamar masa da rashin aikinyi kodan yaci gaba da aikin alkhairi har karshen rayiwarsa.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Umar Faruq Muhammad:

Jiya a hirar Madugun Kwankwasiyya yayi abinda yasaba na zagin Farfesoshin dasuka Jagoranci zaben 2019 tare da jaddada musu sunan rashin daraja saboda zargin su dacewa sun sauya alkaluman zabe, yakuma ce bai taba rantsar da wani a hatamtacciyar Kujera ba.
Farfesa Sani Lawal Malumfashi shine ya Jagoranci Hukumar zabe ta Kano a lokacin Kwankwaso, tun kafin zaben Kwankwaso yashiga Rediyo yace yayi Mafarki Kazar sa ta kyankyashe Kwayaye 44 babu baragurbi, da akazo zaben babu kunya babu tsoron Allah Wannan Farfesan ya shelantawa duniya cewa APC Kwankwasiyya ta cinye Ciyamomi 44 da Kansiloli 488.
Duk raunin Jam’iyyar Hamayya karya ne ayi sahihin zabe ace bata samu ko kujera daya ba.
A ganina in ana neman Farfesa maras Daraja a harkar zabe to daga Malumfashi sai ashafa Fatiha.
Wannan itace hakikanin Darajar Kwankwasiyya.
#SenIbrahimShekarauMedia

Kotunan sauraron kararrakin zaben gwamnonin jihohin Kano, Sokoto, Plateau da Bauchi ake jira domin yanke hukunci kowa yasan matsayinsa.
Daga nan zuwa sabon wata mai kamawa ne al’ummar jihohin Kano da Sokoto da Plateau da Bauchi suke jiran kotunan zabe domin yanke hukunci, domin kowa yasan takamaimai wanda yayi nasara a zaben gwamnonin da hukumar zabe ta ayyana wadanda ke kai a halin yanzu, inda abokin karawarsu suka kalubalanci zabukan da aka yi musu a kotunan kararrakin zabe na jihohinsu.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Umar Faruq Muhammad:

Duk lokacin da Mutum ya tunkari wani Al’amari to Juriya da Dauriya suna daga cikin sinadaran kaiwa ga Nasara.
Fafutukar Tsohon Mallamin Makaranta Mal. Ibrahim Shekarau ta neman Gwamnan Kano a 2003 ta koyarda wannan darasin.
Mallamin ya Jure, Mallamin ya daure, an fada ya toshe kunnen sa, an aikata Batanci ya kauda Idon sa.
Bana Mantawa a wani taron Jam’iyyar APP a gidan Zaituna na Kings Garden, Jiga-jigan APP da masu neman takara sun taru anyi Jawabai, lokacin da aka gabatar da Mal. Shekarau zaiyi nasa jawabin sai Mutane suka dinga tashi suna fita daga gidan, kai har jifa da ledar pure water sai da akayi kan MUMBARIN jawabin.
Duk wadannan abubuwan basu sare gwiwar Mallamin ba, ya cigaba da shiga taruka tare da shiga Unguwanni yakin neman zabe, a iya kyautata zaton sa yasan Allah ne meyi, kuma shi aka nufa da bukatar, shiyasa ma taken tafiyar yazama DOGARO GA ALLAH JARI, kuma a karshe ANCI RIBAR JARIN.
#SenIbrahimShekarauMedia

Salam, A Madadin Shugabanin Da Magoya Bayan Kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S), Muna Mika Sakon Taaziyar mu Ga Hon Sha’aban Ibrahim Sharada. Bisa Rasuwar Mahaifin sa Mal Ibrahim Sharada.Muna Rokon Allah Ya Gafarta Masa. Yasa Aljannatul Firdausi Makormasa. Iyalan sa Allah Ya Basu Hakurin Jure Rashin.Allah Ya Jikan Dukkan Musulmi Baki Daya.
Nagode
Abdullahi Ahmad Tadada
Shugaban S4S
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Umar Faruq Muhammad:

Duk sanda kaji wannan kalmar cikin Yan siyasa kai tsaye zuciyar ka Sardaunan Kano zata kawo.
Kirarin sa ne, taken sa ne tun sanda yafito takara 2003.
Ya fuskanci tsangwama daga Gwamnatin lokacin a matsayin sa na Babban Ma’aikacin Gwamnatin, bashi da karfin tattalin Arzikin kashewa a hidimar siyasa, amma Tauhidin sa ya yarda Allah ne mai bayarwa, a haka yafito takara a Babbar Jam’iyyar hamayya ta ANPP duk da yasan akwai Attajiran Yan takara cikin Jam’iyyar.
Dogaron sa ga Allah shine nasarar sa, har gobe akan haka siyasar Sardauna take, shiyasa bai damu da hayaniya ko karfa-karfa ba.
Wannan hoton yakin neman zabe ne a kakar zaben 2003.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Mu’awiya Habib

MANYA-MANYAN KYAWAWAN HALAYEN MUSULMIN LAGOS
KULA DA TSAFTACE WURIN SALLAH DA WURIN ALWALA DA MAKEWAYI BABU YADDA ZAKAGA YANA KO GIZO-GIZO A SAMAN MASALLATANSU, SANNAN SUNA AIKI TUKURU DUK WATA SAI AN TSAFTACE SAMA DA KASA DA BANGON MASALLATAN, WANDA WANNAN AIKINE NA MASU ZUWA SALLAH WURIN, BABU MAI KUDI BABU TALAKA KOWA SAI YAZO ANYI DASHI,
SANNAN MASALLACHIN YANA DA MAI SHARARSA DA WANKE MAKEWAYI KULLUM,
SANNAN MAGARIBA ZUWA ISHA LOKACINE NA KARATUTTUKAN LITTAFAN ADDINI,

WALLAHI WANI LOKACI NAZO KANO NA KALLI MANYA-MANYAN MASALLATAI DA DATTI DA YANAR GIZO-GIZO, NA KANYI MAMAKI,
YANZU MASALLACHIN MURTALA DA MASALACHIN JUMA’A NA FAGGE IDAN NAGA YANAR GIZO-GIZO A SAMA WLH SAI MAMAKI YA KAMANI, INAMA MASU SALLAH A WURIN SUYI KAMAR YADDA AKEYI A LAGOS.
MUMA ALLAH YASA MASALLATAN KANO MUYI KOYI DASU AMIN.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Umar Faruq Muhammad:

An dauki wannan hoton a dakin karatu na DIALOGUE COMPUTER INSTITUTE, Gwamnatin Mal. Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) ce ta dauki nauyin Dubunnan Matasa domin basu horo akan sana’ar dake alaka da sarrafa Na’ura mai kwakwalwa.
Farfesa Abdallah Uba Adamu da Ado Ahmad Gidan Dabino ne suka Jagoranci shirin.
Bayan kudin Registration da Gwamnatin tabiya Alh. Mahadi mamallakin Makarantar duk sati ana bawa kowanne Dalibi #2800 kudin Mota, bayan Refreshment da ake bayarwa kullum.
Bayan mun kammala anbawa kowa kayan aiki da kudaden kama shago.
Farar rigar dake saman kayana itace Uniform din dalibai, KNSG aka rubuta asaman Aljihun, saboda kudin Gwamnatin Kano akayi amfani dashi ba kudin Shekarau ba.
Kudin mu ne, hakki ne Gwamnatin ta sauke, shiyasa ma batayi yamididi da aikin ba.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Umar Faruq Muhammad

A satin da yagabata Hon. Sha’aban Sharada ya Jagoranci Tawagar Dattawan APC na Municipal zuwa ziyara fadar Sanata Ibrahim Shekarau.
Yayin Ziyarar tawagar ta gabatarwa Sardauna Mutanen dasuka ce sun zauna sun tattauna da jiga-jigan Karamar Hukumar sun zabe su a Matsayin Dattawan dazasu kula da Jam’iyyar a Municipal.
Wannan Jawabin Sardauna ya kalla yakuma yi amfani da Zahirin abinda akaje masa dashi ya yabawa kokarin su.
Kamar yadda muka sani akwai rikici tsakanin Sha’aban dasu Mukhtarri Ishaq Yakasai, daga baya Sardauna ya fahimci wancan Tsarin tsari ne na tsagin su Sha’aban.
Nayi wannan rubutun don Jan hankalin Sardaunawa kar su biyewa masu sukar Sardauna irin su Dan Bilki akan wancan jawabin nasa, dama su masu neman kuka ne aka jefe su kwallon Dabino.
Kowa yasan su Baffa Babba Dan Agundi da Mukhtar Ishaq Mutanen Sardauna ne, dasu da su Sha’aban duk daya ne wajen Sardauna, fatan damuke su taru su hada kansu su manta da sabanin da yafaru kafin zabe.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Bangis Yakawada:

Hukumar Kwastam a Najeriya tace, duk wanda yayi satar hanyar shigowa da shinkafa ‘yar waje cikin Najeriya zai kwashe shekaru uku (3) a kurkuku akan kowane buhu daya (1) na shinkafa da ya shigowa dashi.
#SenIbrahimShekarauMedia

Mai girma gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taya mai girma Shugaban Kasa Buhari murna sakamakon nasarar da ya sake samu a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da ya gabata, wanda kuma jam’iyyar adawa ta kalubalanta.
Wannan ya nuna irin yadda aka gudanar da zaben akan bin doka, tsafta da kwanciyar hankali, kamar yadda Dr Abdullahi Umar Ganduje yace, ta bakin kakakin sa na yada labarai Abba Anwar ya sanar da manema labarai.
Ganduje yace, wannan yar manuniyace, yadda gwamnatin ta jam’iyyar APC ta yi abin kirki ga al’umma wanda kuma za taci gaba da aiwatarwa anan gaba.
#SenIbrahimShekarauMedia
Daga Datti Assalafiy:

Na kalli hotunan da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka fitar har ma da bidiyo a harin da suka yi jiya, amma ban zan saka bidiyon da hotunan anan ba saboda yayi muni, sun tafi da motoci da kayan yaki masu yawan gaske, sun salwantar da rayukan jarumai.
Baba Buhari muna jin takaicin yadda ake zaginka saboda soyayyar da muke maka don Allah, hakika akwai fargaba a Kasar YERWA.
Bama zargin kowa, amma sanannen al’amari ne ana cin amana game da yaki da wadannan annoba ‘yan ta’adda, muna da boyayyen bincike da muka rubuta muka ajiye akan cin amanar da ake yi, wanda zan iya yin rantsuwa da Allah an mayar da wannan ta’addancin hanyar neman kudi, ba’a so ya kare.
Muna rokon Allah Ya haskakawa shugaba Buhari abinda maciya amana suke boye masa. Amin.
#SenIbrahimShekarauMedia

MANZON ALLAH tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yace: “Bazaku shiga aljannah ba sai kun yi imani, kuma ba za kuyi imani ba sai kun so juna.” Shin ba na nuna muku wani abu da in kun yi shi za ku so juna ba? “Ku YADA SALLAMA TSAKANINKU.” Yan uwa, mukasance masu yada sallama a cikin al’umma.
Barkan mu da Jummah.
#SenIbrahimShekarauMedia

Shugabar mata ta kasa da shugabannin mata na shiyyoyi da jihohi da na babban birnin tarayya Abuja na jam’iyyar APC sun kai wa shugaba Buhari ziyara.
Shugaba Buhari ya fada musu cewa, idan suka duba tun daga hawansa kujerar mulki ya dauki mace a matsayin mai kula da dukiyar kasar har zuwa yanzu mace ce kejan akalar tafiyar da kudaden Najeriya a gwamnatinsa.
Wannan ya biyo bayan yadda ko a gidajen aure ake dankawa mace kudade domin tafiyar da gidan.
#SenIbrahimShekarauMedia

Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da kudi kimanin dalar Amurika biliyan biyar da digo uku ($5.3bn) domin karasa shimfida hanyar jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano.
Ministan sufuri Rotimi Amaechi ne ya bayyana haka, Ministan ya bayyana haka ne ta bakin mai taimaka masa a fannin labarai Israel Ibeleme.
#SenIbrahimShekarauMedia

A yau Laraba 11/9/2019 kotun sauraren karar zaben shugaban kasa ta yanke hukunci tsakanin dan takarar shugaban kasa a shekarar 2019 Atiku Abubakar/PDP da Shugaban kasa Buhari/ INEC.
Inda jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar ke kalubalantar hukumar zabe mai zaman kanta INEC da shugaba Buhari bisa ayyana shugaba Buhari da lashe wannan zaben.
Bayan sauraron kowane bangare na masu kara da masu kariya, kotun sauraron karar ta bayyana wannan rana ta Laraba 11/9/2019 domin yanke hukunci bisa laka’ari da hujjojin da kowane bangare ya gabatar.
Yanzu haka, bayan shafe awanni bakwai (7) tana zayyano dalili daban-daban, daga karshe kotun ta yi watsi da karar da Atiku da jam’iyyar sa ta PDP suka shigar a gabanta.
#SenIbrahimShekarauMedia

Gwamnatin Tarayya zata fara zaftare kudadenta da ta ba Jihohi rance domin kashe gararin biyan albashi da hakkokin ma’aikata da gwamnatocin jihohin suka gagara biya mai suna (bailout loan)
Ministan kudi Zainab Ahmed ta bayyana cewa kudaden da suka kama Naira biliyan dari shida da sha hudu (#614bn) za’a fara zaftaresu daga gwamnatocin jihohin da suka ci wannan bashi a cikin kudaden da gwamnatin tarayya ke basu daga watan satumba na wannan shekara 2019
Za kuma a maida su asusun babban bankin kasa wato CBN
#SenIbrahimShekarauMedia

Idan Allah ya kaimu gobe Laraba 11/9/2019 kotun sauraron karar shugaban kasa zata yanke hukunci tsakanin Atiku da jam’iyyar sa ta PDP suka kai shugaba Buhari da hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC domin zargin hada baki wajen ayyana Buhari da lashe zaben.
Sanarwar ta fito daga bakin kakakin yada labarai ta kotun Sa’adiyya Kachalla inda ta bayyana a yau Talata 10/9/3019, idan aka yanke wannan hukunci zai bada dama ga wanda bai amince ba ya daukaka kara zuwa ga kotun koli.
#SenIbrahimShekarauMedia

Kotun sauraren kararrakin zaben Gwamna a Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasiru El-Rufa’i a matsayin halartaccan wanda ya lashe zaben.
El-Rufa’i yayi kira da a zauna lafiya kuma a hada kai domin cigar da Jihar ta Kaduna gaba.
#SenIbrahimShekarauMedia

Zanyi amfani da wannan dama wajen taya ‘yanuwa abokan gwagwarmaya a fadar mundubawa murnar samum scholarship domin tafiya karatu kasar Benin (Cotonou) ta karkashin ofishin sanatan Kano ta tsakiya.
Muneer A Sadi
Muktar B. Kawu
Abba A. Abdullahi
Muna tayaku murna
#SenIbrahimShekarauMedia

Wanda Allah SWT ya azurta, yayi bukata daidai da arzikinsa, wanda kuma bai wadata da arziki ba, shima yayi bukata daidai da abinda Allah SWT ya hore masa, Allah baya dorawa rai sai abinda ta mallaka, duk wani tsanani yana tare da sauki.
Quran: Surah 65 Verse 7
#SenIbrahimShekarauMedia

Najeriya ta bi sauran kasashen duniya wajen shelanta ranar 16 ga watan Satumba na kowace shekara a matsayin ranar alamar kasancewa dan kasa.
Sakataran Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya aikewa da shugaban hukumar kula da tantance yan kasa (NIMC) Aliyu Aziz domin ware wannan rana tare da bin sahun kasashen duniya wajen tantance al’ummar kowace kasa a duniya saboda yin kididdiga da tsare-tsaren cigaban kasa da kuma na tattalin arziki.
#SenIbrahimShekarauMedia

Ba zan daina amfani da MTN ba.
Haka nan SHOPRITE kuwa sai in ba ni da kudi.
DSTV kuwa ba kama kafar yaro!!!
Ashe kuna son goyon bayanmu kuke hana FULANI yin kiwo a yankunanku?
Kuna son mu taya ku kuke murna da wani wawan gwamna ya ruguje mana masallaci?
Ko sati ba’a yi ba.
Yau kuma gashi kun hadu da fushin fusatattu irinku.
Wlh ko a jikina wai an yakushi kakkausa.
Dama babu ta inda Allah baya yin sakayya.
kukan kurciya…
#SenIbrahimShekarauMedia
You must be logged in to post a comment.