
Yayin sauraron korafin zabe a Abuja inda Atiku Abubakar ke kalubalantar lashe zaben shugaban kasa da shugaba Buhari yayi a zaben da ya gabata.
Atiku Abubakar ya gabatar da shaidu a karon farko, wadanda zasu shaidawa kotu cewa ko shakka babu shine ya lashe zaben, nan take aka gabatar da shaida na farko mai suna Buba Galadima.
Yayi bayanin dangantakarsa da Buhari tun 1960 inda ya bayyanashi da mutumin kirki, jajirtacce kuma mai gaskiya, amma yabar tafiyarsa ne sakamakon ya kasa aiwatar da alkawuran zaben da aka zabeshi domin ya aiwatar.
Yayin da lauyoyi suka tambayeshi ko yana sane da ‘yarsa tana cikin gwamnatin? Ya amsa da cewa, ya sani, amma ‘yar tasa tafi kowane jami’in gwamnatin ta Buhari ilimi kuma har yanzu shima dan jam’iyyar ta APC ne kuma babu wanda ya isa ya koreshi tunda dashi aka kafata.
Shaida na gaba ya bayyana cewa, shi ma’aikacin da hukumar ta dauka domun gudanar da zaben ne, ya tabbatar da sunyi aiki da card reader kuma sun tura da sakamakon kai tsaye zuwa runbun tara bayanai na INEC inda sukayi amfani da wata lamba ta sirri da hukumar ta basu domin tura sakamakon zaben.
Da lauyoyi suka tambayeshi ko zai fadawa kotu wannan lambar ta sirri da aka basu domin tura sakamakon zaben? Sai yakada baki yace, ya manta lambar.
Sai shaida na gaba, inda ya tabbatarwa da kotu cewa a inda aka turashi yayi aikin zabe, ba’ayi zaben ba, amma sai gashi an bayyana sakamakon zaben a yayin bayyana sakamakon zabe na jihar,
Da lauyoyi suka tambayeshi ko shi da kansa ya sami uzirin jefa tasa kuri’ar? Nan take ya amsa da cewa yayi nasa zaben.
Sai shaida na gaba, inda shima yace sun tura da sakamakon zabe cikin runbun tara bayanai na hukumar zaben ta hanyar card reader.
Da lauyoyi suka tambayeshi wace rana akayi zaben shugaban kasa? Nan take yace bazai iya tunawa ba.
Lauyoyi da shaidu da alkalai aci gaba da gashi, suya sai ranar sallah.
You must be logged in to post a comment.