Fitowar Sardauna Bayan Dawowa gida daga Abuja

Sardaunan Kano Sanata Mallam Ibrahim Shekarau CON ya fito daga fadarsa a daidai wannan lokaci domin gaisawa da gudanar da uzire-uziransa na yau da kullum yayin da ya dawo gida Kano kamar yadda ya saba.

Shekarau mutum ne na mutane, shugaba na mutane, mai sauraron mutane da basu hakkinsu daga manya zuwa yara daga cikinsu.

Allah ya kara lafiya dai Sardauna

#SenIbrahimShekarauMedia

Daurin Aure

Salam, Muna Farin cikin Gayyatar Dukkan Masoya Sardaunan Kano, Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau. Daurin Auren Dan Uwa Kuma Abokin Gwagwarmaya, Kuma Coordinator Karamar Hukumar Ungogo Na S4S. Hon Abdullahi Shekaran Kadawa.

Ranar Lahadi 7/7/2019
Da Misalin karfe 10:00 Na Safe.
Wuri Rijiyarlemo Layin Banki.

#SenIbrahimShekarauMedia

KOTUN ZABE TA DAGE ZAMANTA A KANO

Kotun sauraron kararrakin zabe dake zamanta a Kano ta daga shari’ar dake gabanta bisa jayayyar wanda yalashe zaben Gwamna a Kano zuwa Asabar 13 ga watan Yuli na wannan shekarar.

Alkalin Kotun Mai shari’ah Halima Shamaki itace ta dage zaman zuwa wannan rana ta Asabar bayan da ta kammala sauraron lauyoyin bangaren da ake kara.

Tunda farko a zaman daya gabata, kotun ta sanya wannan rana don wadanda ake kara su mayarda martani kan korafe-korafen masu kara, wanda kuma hakan ya kasance a yau.

Bayan kammala sauraron martanin wadanda ake karar ne, mai sharia Halima ta dage zaman zuwa Asabar 13 ga wata don yanke hukuncin shiga shari’at gadan-gadan ko kuma korarta baki daya.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sasantawa tsakanin masu neman kujerar shugaban masu rinjaye na Majalisar Tarayya ta 9

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR kenan bayan kammala sasantawa da aka yi tsakanin masu neman kujerar Shugaban masu rinjaye na Majalisar Tarayya ta 9 Hon Aminu Suleiman Goro da Hon Alhassan Ado Doguwa aka tabbatar da Hon Alhassan a matsayin wanda zaa sanar a zaman Majalisar na yau Alhamis insha Allah.
Ga duk masu daukar siyasar Majalisa da zafi dama ta gaji haka amma idan ana nema amma daga karshe in daya ya samu sai a mara masa baya.

#SenIbrahimShekarauMedia

NA SHIGA OFIS – Sanata Ibrahim Shekarau

Tare da matukar godiya ga Allah.

ALHAMDULILLAH

An rantsar dani a matsayin dan majalisar dattijai da zai wakilci Kano Central.

A ranar Laraba 3 ga Yuli 2019, na samu zarafin shiga ofis da aka tanadar min don gudanar da wannan aikin wakilci cikin nasara da walwala.

Mun gode wa Allah da ya kawo mu wannan matsayi. Ina godiya gareku da duk addu’o’inku da kuma fatan alheri.

Na sha fada, kuma yanzu ma zan maimaita, na karbi amanarku, kuma cikin amincewar Allah zan baku wakilci gwargwadon iko.

Abin da nake nema daga gareku addu’a da karin goyon baya da fatan alheri da duk gudunmawar da zata kaimu ga nasarar niyyarmu.

Nagode, kuma ina godiya

Naku
Sanata Ibrahim Shekarau CON
Sardaunan Kano

LAUYOYI SUN ROKI A SALLAMI SHEKARAU

Lauyoyin da suke tsayawa Sanata Ibrahim Shekarau ( APC-Kano Central) a shari’ar da hukumar EFCC ta shigar kan tuhumar raba kudin zaben shekara ta 2015 da aka yi a gidansa, sun roki a sallame shi kuma a kori karar.

Lauyoyin sun ce sun yi wannan roko tare da dogara da cewa duk hujjojin da EFCC da shaidun da suka gabatar basu zo da na yankan shakku ba. Sun gabatar da hujjoji masu karo da juna.

Jiya Talata 2 ga July 2019 aka sake koma wa kotun domin a saurari roko da duk lauyoyin Ambasada Aminu Wali da Sanata Shekarau da Injiniya Mansur Ahmed suka yi na a sallami karar, tunda EFCC sun ce sun rufe kes dinsu, sun gama bada shaida.

Kowanne bangare sun yi wa kotun mai shari’a Lewis Allagoa jawabin karshe, suna rokon kotu ta karba kuma ta yi watsi da bukatun EFCC wanda suka ce cike suke da tufka da warwara.

Ita kuma EFCC ta roki kotu kada ta amsa rokon Sanata Shekarau da abokan shari’arsa, hasali ma EFCC ta roki a dawo a sake bude shafin da suka rufe na Ambasada Aminu Wali da Injiniya Mansur Ahmed tana mai cewa tana da karin hujjoji da zata gabatar a kansu.

Za a yi hukuncin wannan shari’a gaba dayanta ranar 20 ga Satumba 2019 in Allah ya kaimu

Najeriya ta Rage Kudin Aikin Hajj na Bana

Hukumar aikin hajj ta Nageria ta bada sanarwar rage kudin aikin hajj na bana, inda ta umarci a maidowa duk wanda ya biya kudin a baya a dukkanin jihohin kasar.

Yanzu haka ana sa ran mahajjata zasu sami rangwamen kudaden da yakai kimanin dalar America $165 daidai da Riyals na Saudia 620, wanda kuma yazo daidai da kudin Najeriya N51,170. 45

Sakamakon haka an umarci hukumar alhazai ta jihohi ta gaggauta dawowa da mahajjata rarar kudadensu inda kuma hukumar ta kasa ta kara wa’adin rufe biyan kudin aikin hajjin na bana zuwa 15/7/2019 inji makaddashin sakataran hukumar na kasa Alhaji Ahmad Maigari.

An Cika Hannu Da Wani DPO Na ‘Yan Sanda A Katsina

Daga Jamilu samaila Dandana

Hukumar ‘yan sanda a jihar Katsina ta cika hannu da wani jami’in ta mai mukamin DPO mai suna Garba Talawai, sakamakon mutuwar wata budurwa mai shekaru goma sha shida, mai suna Rabi Abdullahi.

Ita dai wannnan budurwa da ta rasu, rahotanni sun nuna cewa tana aiki ne a gidan Sa’adiyya Danyaya wadda budurwa ce ga DPO Talawai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, Gambo Isah ne ya ambata haka yayin zantawarsa da manema labarai a yau Asabar.

Shedun gani da ido sun ce, an ga gawar Rabi Abdullah ne da misalin karfe sha biyun rana a cikin jeji a ranar Juma’a, yayin da aka shaidawa jami’an ‘yan sanda suka garzaya da gawar asibitin dake a garin Mashi na jihar Katsina.

Bayan kai gawar asibiti malaman lafiya sun ce tun ranar Alhamis DPO Talawai ya kai gawar asibitin na Mashi, a motarsa kirar Toyota Carin.

Tuni jami’an ‘yan sanda suka tusa keyar DPO din tare da budurwarsa domin gudanar da bincike.

Kumbotso Ina Mafita?

Yin rubutu ta kowace fuska domin cin zarafin wani ko bayar da kariya akan rashin gaskiya kuskurene

Kokarin hada wani shugabanni rigima shima kuskure ne faruwar lamarin kuma babu abinda zai haifar illa rabuwar kai wadda mu mabiyya mune a kasa INA fatan shugabanin mu zasuyi duba na tsanaki su fahimci cewa akwai al’umma da suka biyo su wannan tsarin domin imani da yarda akan cewa zaku iya samar musu da mafita

Sun zuba ido sun kuma kasa kunne suna fatan ji da ganin mafitar siyasa daga gareku

Masu girma shugabanin mu Dan Allah Ku daure Ku hada kai a kauda ban bance ban bance a tsakaninku a hadu domin yin tafiya daya domin al’umma

Ina fatan Allah yasa hakkan ya kasance amin

Sulaiman Ibrahim Kura

MUNFI KARFIN WULAKANCI…

Tsagin gidan Malam Ibrahim Shekarau a siyasar karamar hukumar Bichi sune sukafi kowa bayarda Gudun mowa domin ganin ansamu nasara a zaben da yagabata na 2019 ayankin BICHI amma yanzu wasu ko wani mutum yana ganin bamu da sauran amfani shiyasa yake kokarin yasa zababbu suja layi da Jagororinmu kuma Wallahi karyane,

Mu babu wanda ya isa ya wofantar damu a siyasance tunda munsamu tarbiya mai kyau ta hakuri da tawakkali irin na jagoranmu Ibrahim Shekarau

Saboda haka muje zuwa.

Daga El-Mansoor Yusha’u Kyautal

Karyace maras tushe da wasu ke yadawa cewa darakta mai kula da fasahar sadarwar zamani a hukumar zabe ta kasa ya ajiye aikinsa sakamakon takaddamar da akeyi na mallakar rumbun tara bayanai na zamani wato “SERVER”

Hukumar tace Mr Chidi Nwafor yananan akan aikinsa, kwanannan ma shi da wasu jami’an hukumar suka dawo daga kasar South Africa, inda suka halarci taron shekara-shekara wanda ya gudana 18 – 20 ga wannan wata na June.

Hukumar tayi kira ayi watsi da wannan jita-jita wacce bata da tushe balle makama.

ZABEN 2023: Dole Shugabancin Kasa Ya Tsaya A Arewa – Matasan Arewa

Gamayyar Kungiyar cigaban matasan yankin Arewacin Najeriya 19 sun bayyana cewar ya zama wajibi a yankin Arewa ya sake fitar da Shugaban Kasa a shekarar 2023 idan Buhari ya kammala wa’adin mulkin shi.

Matasan na Arewa sun tabbatar da cewa, babu wani tagomashi da ‘yan Arewa suka samu a karkashin shugabancin Buhari illa zubar da jini da talauci gami da garkuwa da mutane, saboda haka a mulkin Buhari Arewa ba ta da wakilcin komai, a domin haka lallai ne mulkin ya tsaya Arewa a shekarar 2023.

Ƙungiyar ta dauki wannan matsaya ne a yayin wata ganawa da Shugaban Ƙungiyar na kasa Alhaji Yerima Shettima ya yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Shugaban matasan Arewan ya kara da cewar ko shakka babu APC za ta mutu kafin shekarar 2023, domin abin da ke rike da APC dama shine Buhari, kuma bukatar Buhari ta cika na yin shugabancin kasa har sau biyu, saboda haka bai da wani buri da jam’iyyar a yanzu, ba zai yi takara a 2023 ba, bisa ga haka ‘Yan Arewa na da damar zaben wanda ya dace kuma wanda zai kai yankin Arewa da kasa gaba.

Dangane da ko waye Matasan na Arewa zasu marawa baya a zaben 2023? Shugaban matasan Arewa na Arewa ya ce a yanzu haka dai basu da wani dan takarar da suke goyon baya har sai idan lokaci ya yi masu neman kujerar sun fara fitowa, amma duk da haka yana tabbatar wa jama’a cewa ko kadan ba za su rungume hannu suna kallon ana cutar da yankin Arewa ba, za suyi gwagwarmaya iyakar karfin su domin ceto yankin Arewa.

Matasan wadanda suka jajantawa jama’ar Arewa dangane da abin da suka kira iftila’i da mulkin Buhari ya jefa su a ciki, kuma ko kadan ba za su yarda da yunkurin da Tinubu ya ke yi na ganin ya zama shugaban kasa ba, dole za suyi tsayuwa irin ta mai daka domin ganin mulki ya cigaba a Arewa a 2023.

Daga Shafin Rariya

Sanata Ibrahim Shekarau ya karbi Lambar Girmamawa

Daga Jibril Muhammad Na Tara

21/06/2019

Mai Girma Goni Muhammad Adam Alkali Garkuwan Gwanayen Alqur’ani na kasa dake Jihar Jos ya karrama Mai Girma Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano bisa gudummawar da yake bawa addinin Islama a koda yaushe .
Allah ya tabbatar da Maigirma Sanata akan Wannan tafarki.

Kakakin Majalisar Sanatoci, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya janye nadin da yayi

Sakamakon nuna rashin jin dadi da Buhari Media Organization da wasu kungiyoyin media na jam’iyyar APC suka nuna wajen nada Dr Festus Adedayo a matsayin mai bada shawara na musamman akan harkokin sadarwa da yada labarai na kakakin majalisar dattijai ta kasa Sanata Ahmad Ibrahim Lawan yayi.

Yanzu haka kakakin majalisar sanatocin Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya janye wannan nadin kuma yana yiwa Dr Festus Adedayo fatan alkhairi a duk inda zai tsinci kansa anan gaba.

Wani dan bindiga ya bude wuta a Kano

Wani dan bindiga ya bude wuta akan wasu mahaya dawaki a unguwar Hausawa dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano inda dayawa daga cikin mahayan suka sami raunika daban-daban.

Wannan ya farune a yayin da mahayan ke hidimar biki a inda sukayi hawa suna zagayawa akan dawaki a unguwar ta Hausawa, shigarsu wani layi keda wuya wannan dan bindiga ya bude musu wuta kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito.

Yanzu haka wadanda suka sami raunikan suna asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano domin karbar magani, yayin da aka tuntubi jami’an ‘yan sanda na Jihar Kano domin jin ta bakinsu, sun tabbatar da maganar amma suka ce, har ya zuwa lokacin rubutu wannan rahoto babu wani cikakken bayani.

Sojojin Najeriya lusarai ne – Buratai

Shugaban sojojin Najeriya Lt Gen Tukur Buratai ya shedawa duniya cewa, hare-haren da ‘yan tada kayar baya ke kaiwa a jihohin kasar a yanzu bazai rasa nasaba da rashin jajircewa da lusarancin sojojin ba.

Masamman wadanda ke filin daga, basa iya aiwatar da aikin dake gabansu na kasancewarsu sojojin masu kare martabar kasarsu Najeriya.

Bunkasa Ilimin ‘ya’ya Mata

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam ya jagoran ci manyan Jami’an Gwamnati zuwa d’akin taro na Ante Chamber dake fadar Gwamnati dan tattauna maqaloli da Matasa tare da had’in guiwar Hukumar Majalisar d’inkin duniya UNICEF ta assa sa dan bunk’asa ilmin y’ay’a mata da kyauta ta rayuwar su. K’ark’ashin jagoran cin Sakatariyar Hilwa Hajiya ladidi sani fagge. Yayin Jawabin ta yabawa Gwamna wajen jajirce wa daya ke wajen inganta rayuwar matasa da ilmantar dasu, tareda Mai Girma Gwamna akwai Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji, Shugaban Ma’aikata Dr Kabiru Shehu, Shugaban jama’iyyar APC Abdullahi Abbas,Perm Sec Usman Bala.

anasa Jawabin Mai Girma Gwamna ya yaba wa wad’annan matasa da janyo hankalin su kan su dage da neman ilmi, k’aurace wa shaye shaye da dukkanin abinda zai gurb’ata rayuwar su.yakuma basu tabbacin sabuwar Ma’aikatar Matasa da wasanni da zai k’irk’iro kwanan nan zata jajirce matuqa wajen kula da Matasa.

Danzainab.
17th June 2019.

Tsaro a Najeriya

Daga Na’Allah Raheemeeb

Maganar gaskiya harkar tsaro a Najeriya itace tafi muhimmanci fiye da komai, saboda idan babu zaman lafiya mulki bazai tafi daidai ba, hasali ma babu wanda zai shiga gidan gwamnati da niyyar ya mulki dabbobi, mutane sune alfaharin mulki, sune ke fitowa su kada kuri’arsu domin mai mulki ya sami kujerar da zai mulkesu lami-lafiya, a halin da muke gani wasa-wasa wankin hula yana neman yakai dare, domin an kasa gano bakin zare da za’a kama a warware wannan mas’ala.

Shugaban kasa Buhari naji yana cewa zai dauki tsauraran matakai a harkar tsaro, inda Gwamnonin Arewacin Najeriya naji sunyi taro domin ganin bayan ta’addanci a Arewacin Najeriya, Gwamnan Kaduna naji ya kirkiri sabuwar ma’aikatar tsaro, haka takwaransa na Jihar Kano shima naji yace zai gina wajen atisaye da horaswa ga sojojin Najeriya a dajin Falgore domin kiyaye harkar tsaro, a baya-bayannan naji Gwamnan Zamfara yace zai fita Kasar Dubai domin ganawa da kwararru akan harkar tsaro domin taimakawa Jiharsa wajen kawo karshen wannan ta’addanci.

Muna jiran muji daga sauran Gwamnonin Arewa irin su Katsina, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Bauchi, Plateau Yobe, Borno, Adamawa, Gombe, Taraba, Niger, Benue da Kogi.

Shin wane irin tanadi kukayiwa harkar tsaro domin cigaban al’ummar wannan yanki dama Kasa baki daya ta hanyar hada karfi da Gwamnatin Tarayya a wannan sabuwar Gwamnati wacce kukayiwa lakabi da MATAKI NA GABA.

BUK tayi bikin yaye dalibai na 35

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam ya jagoran ci tawagar Jami’an Gwamnati zuwa Jami’ar Bayero BUK dan Halartar bikin yaye d’alibai na 35 Convocation, Gwamna yasamu rakiyar Shugaban jam’iyar APC Abdullahi Abbas,tsoffin kwamishinoni da masu baiwa Gwamna shawara , tsohon Mataimakin Gwamna Tijjani Mohammad Gwarzo da sauran masoya.

Danzainab
15th June 2019

Bikin Yaye Jami’an Hukumar Shiga da Fice ta Kasa

Sanata Malam Ibrahim Shekarau yana daga cikin manyan bakin da suka hallacci bikin kaddamar da yaye sabbin ma’aikatan hukuma shiga da fice ta Kasa yau Asabar, 15/6/2019

Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Rasu

Allah ya yiwa tsohon mataimakin gwamnan Bauchi Babayo Gamawa rasuwa, ya rasu a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa Bauchi yana da shekaru 53 a yau Jummah 14/6/2019 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Allah yai masa rahama, yabawa iyalansa da yan uwansa da abokansa hakurin jure rashin sa.

NA KARBI AMANARKU

Assalamu alaikum,

Jama’a barkanmu da Rana

Cikin yardar Allah da ikonsa, yanzu aka rantsar dani a matsayin sanata da zai wakilci Kano Central a jam’iyyar APC. An rantsar dani tare da wasu takwarorina.

Yau ce ranar da na karbi amanarku, a matsayin wakilin bukatunku a majalisar dattijai ta Najeriya. Na amshi nauyin kananan hukumomi 15 na Kano Central.

Wannan rantsuwa ce da nayi domin Allah kuma cikin nufin Allah zan yi bakin kokarina na isar da duk aikenku. Zan sauke nauyinku da sauki da sahalewar Allah.

Ina amfani da wannan dama na yi wa sabon shugaban majalisar dattijai Sanata Dr. Ahmed Lawan da mataimakinsa Sanata Omo Ovie Agege barka da samun wannan matsayi. Allah ne ya baku, mu kuma zamu baku duk goyon baya domin nasarar Najeriyarmu.

Ga jama’ar Kano Central da duk al’ummar Kano, ina sake yin godiya a gareku da nuna min kauna da yarda da kuka yi har Allah ya kawo mu wannan matsayin. Da bazarku muke rawa. Don Allah ku ci gaba da yi mana addu’a da shawari nagari don samun dacewa a yau da gobenmu.

Naku
Sanata Ibrahim Shekarau
(Sardaunan Kano)

Distinguish Senator Ibrahim Shekarau

TAKAITACCAN BAYANIN DA YAYI…

Na shiga majalisar dattawa ne domin na kyautatawa ‘yan Najeriya ba tare da nuna banbancin kabila ko addini ko jam’iyyar siyasa ba.

Don haka yankin mazabata ta fari itace Najeriya, ta biyu itace Najeriya, ta uku itace Najeriya – Distinguish Senator Ibrahim Shekarau

SAKON TAYA MURNA GA MAI GIRMA SARDAUNAN KANO

DAGA #S4S2019

A.madadin jagorori da na wannan tafiya wato Alh. Salisu Indabawa wato Chief of Staff na gidan mai girma za6a66en Senator Kano ta tsakiya Dr. Mallam Ibrahim Shekarau da kuma Alh. Haruna Muhammad Gama ( Garkuwar Sardauna) da dukkannin Exco na #S4S ta jiha karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada, da kuma sauran dukkannin membobinta da sauran Co-ordinators na kananan hukumomi muke amfani da wannan dama domin taya jagoranmu, shugabanmu abin koyi mai girma Sardaunan Kano tsohon Gwamna sau biyu a jere, tsohon Minister na Ilimi kuma yanzu sabon Senator Dr. Mallam Ibrahim Shekarau. Bisa rantsar da shi da a kayi yau Talata 11/6/2019 a matsayin sabon Senator Kano ta tsakiya.

Da fata da kuma addu’ar Allah (S.W.A) yayi riko da hannunsa yayi masa jagora a dukkan al’amuransa. Allah kuma ya bashi ikon sauke wannan nauyi da Allah ya dora masa. Allah yasa yadda ya fara lafiya, Allah yasa ya gama lafiya. Sannan ba zamu gushe ba sai mun mika sakon taya murnar ga dukkannin sauran ragowar Sanatocinmu guda biyu wato Senator Kabiru Ibrahim Gaya da kuma Barau I. Jibrin Maliya da kuma dukkannin sauran yan majalisun wakilai na tarayya suma. Allah yayi riko da hannayensu ya basu ikon sauke nauyin da Allah ya dora musu ga al’umma.

Daga karshe muke addu’ar Allah (S.W.A) ya kara mana lafiya da zaman lafiya a kasarmu da dukkannin sauran kasashen yan’uwa musulmi na duniya. Allah yasa mu cika da imani ya kyautata karshenmu.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S,
11/06/2019.

Jam’iyya ce gaba da kowane zababbe

Shugaban kasa Buhari ya bukaci ‘Yan majalisa su girmama jam’iyya daf da shirye-shiryen kaddamar da majalisar kasa kashi na tara (9)

TAYA MURNA GA SHUGABAN MAJALISAR DOKOKI TA KANO

A yau cikin yardar Allah na samu labarin ‘yan majalisar dokoki n jihar Kano, sun hadu guri guda a zauren majalisa sun zabi Rt. Hon AbdulAziz Garba Gafasa a matsayin shugaban sabuwar majalisar ta tara.

Rt. Hon Gafasa, a lokacin da nake gwamnan jihar Kano, mun yi aiki tare da shi. Na san shi, mutum ne mai kwazo da kishi da amana.

Ina amfani da wannan dama na mika sakon taya murna gare shi da sauran duk ‘yan majalisar Kano da aka rantsar da su a yau. Allah ya sa an shiga a sa’a. Allah ya yi riko da hannunmu duka domin taimakon jihar Kano a kowane mataki.

Nagode
Naku
Ibrahim Shekarau
(Sardaunan Kano)

Mai hali bazai chanja ba

Magana ta gaskiya kamar yadda naji wasu marubuta suna danganta sarautar gargajiya masamman a Jihar Kano da siyasa na amince hakane amma lokaci ake dubawa, a baya kamar yadda akayi bayani tun daga 1955 idan muka duba dole sarakuna su kasance ‘yan siyasa duba da irin hurumin aikinsu masamman na rike madafun iko.

A wancan lokacin, sarakuna keda alhakin shugabantar Native Authority (NA) inda ‘yan sanda, gidan yari, malamai na makarantu, da sauransu ke karkashin ikonsu amma tunda aka fara mulkin dimokaradiyya ta jamhuriya ta farko aka kwace wadannan madafun ikon a hannun sarakuna kuma aka haramta musu shiga sabgar siyasa inda suka zama iyayen kasa kawai, ma’ana kowa nasu ne babu banbanci.

Amma wancan burbushin sarautar da suka dafa na madafun iko a baya, shine yake tasiri wajen tsomala baki a bayan fage duk da sunsan haramun ne a garesu, matsalar shi wannan Sarkin na Kano zakewa da fitowa fili yana yakar gwamnatin da ludayinta ke kan dawo kuma wacce take biyansa da majalisarsa albashi harma da bashi wasu rarar kudade na tafiyar da masarautar.

Shi Sarki fa idan muka duba kamar ma’aikacin gwamnati ne a irin wannan tsarin wanda duk gwamnatin da tazo zata tafi dashi, don haka yazama dole ya sunkuyar da kansa yayi biyayya yayi aiki tare da gwamnatin da take kan gadon mulki, ba kokarin yin aiki da gwamnan da mulkinsa ya shude ba, yin haka nuna kiyayya ne karara ga Gwamnatin da take kan mulki, na tabbatar koma waye bazai dauke kansa ya zuba ido ana takashi ana lakuce masa hanci, ana wofantar dashi ta hanyar kokarin ganin bayansa daga kujerar mulkisa ba.

Kamar yadda marubuta suka tabbatar da rashin adalcin da Kwankwaso yayi na kakabawa al’umma abinda basa bukata bai kamata musaka hannun Ganduje cikin wannan danbarwar ba, duba da cewa, a lokacin bashi da ta cewa a matsayinsa na mataimakin gwamna wanda tsarin mulkin ma bai tantance masa cikakken aikinsa na mataimaki ba, kuskure ne mu sakoshi a matsayin dashi aka nada Sarki Sunusi Lamido Sunusi II.

Shekaru hudu suka shafe tare akan gadon mulki, duk da cewa masarautar tana ta ciwa gwamnan fuska bai daga ido ya duba ba, har bayan shekaru 2 sannan ya shafa kan Sarkin kafin a dawo a daidaita, kasancewar an daidaita wane dalili kuma ya dawo da wancan cin fuska a daidai wannan lokaci?

A fahimtata, tunda wancan daidaitawa da akayi ta fari bata isa masarauta ta daina ciwa gwamna fuska ba, banyi zaton daidaitawar da aka sake yi a halin yanzu zata dakatar da Sarki daga abinda ya sabayi ba, na tabbatar nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa matukar Sarki yana gadon mulki sai ya sake ciwa gwamna Ganduje fuska, kuma zai sake yin kokarin hada kai da Kwankwaso da magoya bayansa domin suga sun cimma burinsu na hana duk wani dan takarar jam’iyyar APC da ta tsayar na gwamna a wannan Jiha ta Kano.

Sanata Ndume yace kuri’a yake son gani a zahiri

Zababban Sanata Ali Muhammad Ndume mai neman takarar kujerar shugaban Sanatoci wato (Senate president) yace, shi kuri’a yake nema ba wai alkawarin goyon baya ba.

Design a site like this with WordPress.com
Get started