
#S4S2019
Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa Prince Uche Secondus yace Shugaban Kasa Buhari yana tunzura jami’an tsaro domin yin kwacen mulkin Kasar da taimakonsu, yace bai taba ganin Shugaban da yayi umarni a kashe Al’ummar kasa ba sai Buhari.
Zabe ba harka ce ta jami’an sojoji ba, don haka bai kamata ace soja ya shiga harkar zabe ba bayan ga ‘yan sanda, a cewar sa Shugaba Buhari ya daura yaki ne da ‘yan Najeriya tunda yayi umarni a kashe su.
Daga Na’Allah Raheemeeb
