Sen Ibrahim Shekarau ya halarci bikin rantsuwa

Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano.

Ya halarci rantsar da Hon Alhassan Ado Doguwa mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa da Hon Ali Datti Yako wakilin Bebeji da Kiru.

Wanda aka sake zaben su a ranar Asabar, 25/1/2020

Allah ya yi mu su jagora.
Muna taya su murna.

Sako Daga S4S

Godiya ga Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Dr Ahmad Ibrahim Lawan

A madadin shugabani da magoya bayan kungiyar Shekarau 4 Senator (S4S)

Muna mika sakon godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Dr Ahmad Ibrahim Lawan, tare da jagoran mu, Sanata Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano.

Bisa nada;
1. Hon Bashir Hayatu Jantile,
2. Khalid Ibrahim Shekarau

A matsayin mataimaka na Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya. Allah ya kara daukaka da sutura, ya yi mu su jagora.

Sako Daga S4S

Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai ci, Ibrahim Shekarau ya yi martani a kan rikicin da ke tsakanin masarauta da gwamnatin jihar Kano. Ya ce yana iya bakin kokarinsa ta karkashin kasa don ganin an samu jituwa tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sarki Muhammad Sanusi II. A wata hira da ya yi da shafin BBC Hausa, Shekarau wanda ke wakiltan Kano ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, ya ce ba zai yiwu ya fito bainar jama’a da sunan yin tsokaci kan lamarin ba alhalin ya kasance an majalisar sarki kuma jigo a gwamnatin jihar Kano.

Shekarau ya jadadda cewa za su ci gaba da aiki ta karkashin kasa don cimma masalaha a tsakanin shugabannin biyu. Wannan shine karo na farko da sanatan ke magana tun bayan fara samun rashin jituwa a tsakanin shugabannin biyu yayin da ya cika shekarara 10 da samun sararutar Sardaunan Kano, wadda marigayi Sarki Ado Bayero ya nada shi.

Ya ce: “Ita masalaha kamar ciwo ce, rana daya sai ciwo ya shige ka amma sai ka shekara, shekaru ma kana shan magani ba ka warke ba.”

Ya kuma bayyana cewa yana sane da kima da martabar masarauta, kana kuma ya san kima da martabar gwamnatin Kano don haka za su ci gaba da yunkurin ganin an sasanta. A baya mun ji cewa wata babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 27 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron karar da dattijan jihar Kano suka shigar ta neman a dakatar da sabuwar dokar kirkirar sabbin masarautu guda hudu a Kano. Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa dattijan Kano su 19 a karkashin jagorancin Alhaji Bashir Usman Tofa sun shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar sabuwar dokar da ta bawa gwamnatin Kano damar kirkirar sabbin masarautu. Wadanda sunansu ya bayyana a karar da dattijan suka shigar sune kamar haka; shugaban majalisar dokokin jihar Kano, alkalin alkalai na jihar Kano, Tafida Abubakar Ila (sarkin Rano), Ibrahim Abdulkadir Gaya (sarkin Gaya), Dakta Ibrahim Abubakar II (sarkin Karaye), Aminu Ado Bayero (sarkin Bichi), fadar Kano da sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

#SenIbrahimShekarauMedia

KWANKWASON KARFE

Daga Umar Faruq Muhammad:

Idan zakayi awo da Ma’auni na Jarumta zaka ga sakamako cewa Musa Ilyasu Kwankwaso shine Kwankwason Karfe, Madugun zare Idanu kuwa sai dai ka kirashi Kwankwason Roba.

Shugaban Karamar Hukumar Madobi kawai yataba rikewa a Mukamin Zartarwa, sai Kwamishinan Kananan Hukumomi dayayi a zamanin Sardaunan Kano dakuma lokacin Khadimul Islama, amma duk sanda zabe yazo sai ya kasa ya tsare ya tumurmusa motsin Madugu.

Ko sanda Madugu ke Gwamna da kyar yake samun Nasara akan Musa Ilyasu.

Yauma dai gashi nan a Re-Run din da akeyi Musa din ya kachalchala Madugun.

Musa Ilyasu kaine KWANKWASON KARFE.

#SenIbrahimShekarauMedia

Kasance da Hon (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso Lahadi 26/1/2020

Masha Allah, yau Lahadi 26/1/2020 kasance da maigirma Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso kwamishina ma’aikatar raya karkar da cigaban Al’ummah yau a gidajan rediyon 1- Rahama karfe 9:00 zuwa 10:00 2- Guarantee karfe 10:00 zuwa 11:00 na daran yau, ku biyomu.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau akan hanyarsa zuwa Kano

Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Da Arch Aminu Abubakar Dabo, A Hanyar Su Da Dawo Jihar Kano. Allah Ya Sauke ku lafiya. Sako Daga S4S

Senator Shekarau arrived Abuja this morning

His Excellency Senator Shekarau arrived Abuja this morning.

You are highly welcome sir and wish the trip was a successful one to you and the whole nation

#S4S

Sen Ibrahim Shekarau na gayyatar magoya baya zuwa daurin auren Sani Bin Umar

A madadin maigirma Sen Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, ni Abdullahi Ahmad Tadada, shugaban kungiyar (S4S) ina farin cikin gayyatar dukkanin magoya bayan Sardaunan Kano, zuwa wajen daurin auren hadimin sa kuma Sakataren Kungiyar SHEKARAU4SENATOR (S4S) Sani Bin Umar.

Karkashin Jagorancin Sen Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, wanda za ayi kamar haka:-

Rana:- Lahadi 26/01/2020.

Wuri:- Kawon Alh. Sani layin Baburawa.

Lokaci:- 11:00am na safe.

Allah ya bada ikon zuwa ameen.

#SenIbrahimShekarauMedia

DAGA LANDAN ASABAR, 18 JUNAIRU 2020.

Manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya 47 Daga cikin shugabannin gudanarwa da manyan jami’ai sun shirya domin fara Jarrabawar Karin matsayi Na Shekarar 2019 a Babban Ofishin Najeriya dake Landan.

Jarrabawar na gudana a cibiyoyi guda huɗu a duk faɗin duniya .
An fara shi cikin dukkanin cibiyoyin guda huɗu lokaci guda duk da bambancin lokaci,
Cibiyoyin sune New York da misalin karfe 10 na safe, Cibiyoyin dake Arewa da Kudancin Amurka, Amurka. Nairobi, Kenya ga Afirka da misalin karfe 5 na yamma, Cibiyoyin dake New Delhi, Indiya da waɗanda dake Asiya da ƙarfe 830 na safe, da Landon, UK da ƙarfe 3 na yamma ga waɗanda ke aiki a cikin ƙasashen Turai.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, shugaban kwamitin Public Service and Establishment a Majalisar Dattawa Mai Girma Sanatan Kano ta tsakiya Dakta Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya ja hankalinsu da su kasance jakadu na Gari a koyaushe
Sannan ya yi addu’ar Allah ya bada Sakamako Madaukakiya.

Malam Ibrahim Shekarau ya samu rakiyar wasu daga cikin Sanatoci a Majalisar Dattawa da Hon. Engr Bala Sani daga Majalisar wakilai da membobin hukumar Ma’aikatan Gwamnatin tarayya da kuma Sakataren dindindin na hukumar Mista Abel Olumuyiwa.
#S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Kakakin Majalisar Kasar Gambia Ta Karrama Sen Ibrahim Shekarau

Kakakin Majalisar Kasar Gambia Mariam Jack Denton Ta Karrama Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano. A Ziyarar Ban Kwana Da Sukayi A Karshen Ziyarar Da Suke A Kasar Gambia. Allah Ya Kara Daukaka.

#SenIbrahimShekarauMedia

A ci gaba da ziyarar kasar Gambiya

A Rana Ta Uku, Kuma Ta Karshe A Ziyarar Da Kwamatin Majalisar Dattawa Dana Wakilai Na Majalisun Najeriya, Karkashin Jagoranci Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, Yake Jagoran ta.
1.Sun Ziyarchi Ofishin Jakadancin Najeriya Dake Banjul Kasar Gambia.
2.Sun Tattauna Da Clerk Na Majalisar Kasar Gambia Momodon A. SIZE
3.Wannan Sun Ziyarchi Gidanjen Tarihi Na Kasar Gambia.
Daga Karshe Muna Rokon Allah Ya Yi Jagora. Ya Tabbatar Da Alheri A Wannan Tafiya.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau Mikiya Mai Hangen Nesa

A ci gaba da kawo muku abubuwan da Mai girma Sen Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya bujuro dasu, za mu ci gaba kamar haka;

a) Daukar ma’aikata masu taimaka ma sa a ofishin sa na Sanata.

b) Shirin sa na hada hannu da shugabannin kananan hukumomin Kano ta Taskiya domin kawo ayyukan da za su tallafawa al’umma na shiyyar sa da yake wakilta a can kasa.

A yanzu haka zai ci gaba da zama da masu ruwa da tsaki kamar yadda ya fara zama da shugabannin kananan hukumomin Kano Central, shugabannin shiyyoyi, shugabannin jam’iyya, Coordinators, Hakimai, Malamai, ‘Yan kasuwa da sauran fanni-fanni na al’umma, Mata da Maza.

c) Akwai wani kudiri shima da su ka hada hannu da sauran sanatocin jihar ta Kano, Sen Barau Jibrin da Sen Kabiru Gaya, wanda su ke so a magance, ayi bincike, kuma a hukunta wadanda suka sace kananan yara a Kano.Yanzu haka, maganar tana gaban kwamatin sauraron korafe-korafe na majalisar dattijai.

Zamu ci gaba da kawo muku ayyukan alkhairi da su ke kan layi nan gaba.

Idan mukabi a sannu, Sen Ibrahim Shekarau zai sakko da tsari har kasa insha Allah.

Sako daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau daga kasar Gambiya a ci gaba da ziyarar aiki

A Rana Ta Biyu, A Ziyarar Aiki Da Wakilan Majalisar Dattawa Da Na Majalisar Wakilai Suke Yi A Banjul Kasar Gambiya. Karkashin Jagorancin Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano.
1.Kwamatin Sun Tattauna Da Mataimakin Shugaban Majalisar Kasar Gambia, Momodon L. L. Sanneh
2.Haka Kuma Sun Gana Da Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Kasar Gambia, Kebba k. Barrow
3.Sannan Sun Zauna Da Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Kasar Gambia.

4.Daga Bisani Anyi Zaman Karawa Juna Sani Da Dukkan Ma’aikatan Majalisar.
Allah Ya Taimaki Mai Girma Sardaunan Kano.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

An sake dage yanke hukuncin zaben gwamna na Kano

Daga Abdullahi Ahmad Tadada:

Kamar Yadda Muka Sani Cewa A Yau, An Koma Zaman Kotun Koli Akan Zaben 2019 Da Akayi wa Mai Girma Gwamna Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam Da Mataimakinsa Dr Nasiru Yusif Gawuna Dukkan su Na Jam’iyyar A. P. C. Wanda Kuma Allah ya Basu Nasara.
Daga Bisani Jam’iyar Adawa Ta PDP. Da Dan Takarar Ta Abba Kabir Yusif, Suka Tafi Kotu Domin Kalubalatar Zaben. Kotun Farko Ta Tabbatar Da Uban Abba Ne Yaci Zabe.

Haka Kuma Suka Tafi Kotu Ta Biyu, A Garin Kaduna Ita Ma Ta Gamsu Da Zaben Da Akayiwa Baban Abba. Sai Suka Tafi Kotun Karshe Ta Koli wacce Ake Cewa Daga Ita Sai Allah Ya Isa. Wanda Ita kuma Ta Sanya Ranar Litinin 20th January, 2020, Zata Yanke Hukuncin Zaben. Wanda Da Yardar Allah Ita Zata Amince Da Hukuncin Wadacan Kotunan Guda Biyu. Wato Zata Tabbatar wa Da Mai Girma Gwamna Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam OFR, Da Dr Nasiru Yusif Gawuna Ci Gaba Da Aiyyukan Alheri Da Suke Yiwa Jihar Kano.

Daga Karshe Muna Rokon Ya Saka wa Mai Girma Gwamna Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam Da Mataimakinsa Dr Nasiru Yusif Gawuna. Tare Da Dukkan Jamian Gwamnatinsa, Irin su Hon Shehu Muhammad Na’allah Kura, Hon Dr Musa Iliyasu Kwankwaso, Hon Baffa Takai, Hon Ghali Sadiq, Engr Mustapha Gwarzo Da Sauran Wadanda Ba Zasu Fadu ba.

Jinjina Ga Shugaban Jam’iyar A. P. C Dan Sarki Jikan Sarki, Alh Abs
Abdullahi Abbas Da Shugaban Kwamatin Yakin Neman Zabe Hon Nasiru Aliko Koki. Allah Ya Saka Da Mafificin Alheri.

Muna Kara Jadadda Goyon Bayanmu Ga Mai Girma Sardaunan Kano Kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau, Jagora Nagari Abin Koyi. Allah Ya Kara lafiya Da Daukaka.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Hukumar ‘yan Sanda sun shirya tsaf wajen tun karar zaben 25 ga wannan wata

Asabar 25, Janairu ce ranar da hukumar zabe ta sa domin a sake gudanar da zabukan da kotu ta bada umarni, hukumar zabe karkashin kwamishinan zabe na INEC a Kano Professor Risqua Shehu ya gana da masu ruwa da tsarki na jam’iyyun da zasu shiga zaben.

Yaja hankalin masu ruwa da tsarki cewa zasu gudanar da zabe bisa doka da ka’ida kuma sahihi wanda ba za’a sami kura-kurai ba, don haka ya hada kai da jami’an tsaro domin samun nasara.

Haka kuma ba za’a tura NYSC a Bebeji ba, sakamakon shawarar da muka samu daga jami’an tsaron inji Risqua, haka kuma ba zamuyi kasa a gwuiwa ba wajen soke zaben da duk aka sami hargitsi, ko aka yiwa masu zabe barazana da rayukansu ko dukiyoyinsu.

A bayanin Kwamishinan yan sanda na Jihar ta kano, Ahmad Sani yace, a shirye hukumar sa take wajen kawo zaman lafiya, amma yaja hankalin duk masu son tada tarzoma, su kwana da shirin zasu fuskanci hukunci da doka ta tanada akan su daidai da abinda suka aikata.

Daga karshe, suma masu ruwa da tsarki na jam’iyyun sun ja hankalin hukumar zaben da su guji goyon bayan wata jam’iyya, su tsaya a matsayinsu na ‘yan baruwanmu su gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanadar musu.

Haka kuma sunja hankalin kwamishinan ‘yan sanda da ya dauki mataki akan duk wadanda ke shiga kafafen yada labarai yana yin furuci na kokarin tada tarzoma.

Kamar yadda hukumar zaben ta jihar Kano ta tabbatar za’a gudanar da zaben ne ranar Asabar 25 ga wata janairu 2020 a gurare kamar haka:
(Kiru/Bebeji da Tudun Wada/Doguwa)sai kuma polling units 2 a Kumbotso mazabar dan majalisar tarayya sai kuma wasu 4 daga cikin mazabun ‘yan majalisar Jiha wadanda suka hada da; Bunkure, Madobi, Minjibir and Rogo.

#SenIbrahimShekarauMedia

Hukumar ‘yan Sanda sun shirya tsaf wajen tun karar zaben 25 ga wannan wata

Asabar 25, Janairu ce ranar da hukumar zabe ta sa domin a sake gudanar da zabukan da kotu ta bada umarni, hukumar zabe karkashin kwamishinan zabe na INEC a Kano Professor Risqua Shehu ya gana da masu ruwa da tsarki na jam’iyyun da zasu shiga zaben.

Yaja hankalin masu ruwa da tsarki cewa zasu gudanar da zabe bisa doka da ka’ida kuma sahihi wanda ba za’a sami kura-kurai ba, don haka ya hada kai da jami’an tsaro domin samun nasara.

Haka kuma ba za’a tura NYSC a Bebeji ba, sakamakon shawarar da muka samu daga jami’an tsaron inji Risqua, haka kuma ba zamuyi kasa a gwuiwa ba wajen soke zaben da duk aka sami hargitsi, ko aka yiwa masu zabe barazana da rayukansu ko dukiyoyinsu.

A bayanin Kwamishinan yan sanda na Jihar ta kano, Ahmad Sani yace, a shirye hukumar sa take wajen kawo zaman lafiya, amma yaja hankalin duk masu son tada tarzoma, su kwana da shirin zasu fuskanci hukunci da doka ta tanada akan su daidai da abinda suka aikata.

Daga karshe, suma masu ruwa da tsarki na jam’iyyun sun ja hankalin hukumar zaben da su guji goyon bayan wata jam’iyya, su tsaya a matsayinsu na ‘yan baruwanmu su gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanadar musu.

Haka kuma sunja hankalin kwamishinan ‘yan sanda da ya dauki mataki akan duk wadanda ke shiga kafafen yada labarai yana yin furuci na kokarin tada tarzoma.

Kamar yadda hukumar zaben ta jihar Kano ta tabbatar za’a gudanar da zaben ne ranar Asabar 25 ga wata janairu 2020 a gurare kamar haka:
(Kiru/Bebeji da Tudun Wada/Doguwa)sai kuma polling units 2 a Kumbotso mazabar dan majalisar tarayya sai kuma wasu 4 daga cikin mazabun ‘yan majalisar Jiha wadanda suka hada da; Bunkure, Madobi, Minjibir and Rogo.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sakon taya murna daga S4S

Shugababnin kungiyar #S4S ta jiha karksahin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada muke mika sakon taya murna ga daya daga cikin hadiman mai girma Sardaunan Kano Sanatan Kano ta tsakiya wato Engr. Bello Sani Gwarzo bisa rabauta da yayi ta kujerar Executive Director na Hadejia Jama’are. Allah Ubangiji (S.W.A) ya sanya alheri ya taya riko ya kauda dukkannin abin ki yayi jagora.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S,
13/01/2020.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau a hirar sa da gidan radio Najeriya na Kaduna

Daga Abdullahi Ahmad Tadada:

A yau Asabat 11 ga Janairu 2020 da misalin karfe goma na safe zuwa sha biyu na rana, tare da Zonal Director na FRCN Mallam Buhari Awwalu

Sanata Mallam Ibrahim Shekarau ya fadi muhimman abubuwa guda goma.

GA SU A JERE:

Na daya: Abubuwa biyu ne zasu gyara harkar zabe a kasar nan. A yi aiki tukuru na fadakar da mutane wajen muhimmancin karbar rijista da shiga zabe da kuma aikin fito da duk wadanda suka yi rajista su zo su sauke nauyin. A samar da isassun jami’an tsaro.

Na biyu: Wasu zababbu suna da karancin fahimtar aikin da ke kansu, haka wasu sauran jama’ar gari sun jahilci nauyin wakilcin da suka tura wakilansu.

Na uku: A yau muna bukatar kwararru da managarta masu tsananin kishi a cikin sabgar siyasa, wadanda za su biya mana bukatunmu.

Na hudu: Ba shakka membobin majalisar kasa ana basu kudaden gudanarwa na yau da kullum kamar yadda ake warewa bangaren zartaswa.

Na biyar: Aikin mazabun ‘yan majalisa ko na tarayya ko na dattijai yana da amfani sosai, zamu bada gudunmawa sosai domin a inganta shi, a kaucewa korafin da ake yi akansa.

Na shida: Nayi darasin duk bukatun Kano Central Senatorial District a tsawon wata hudu kuma nayi nisa a tattaunawa da duk jama’armu domin mu hada karfi wajen samun nasarar wannan nauyi da aka dora mana.

Na bakwai: Babban abin da zamu maida hankali akansa shi ne gina dan adam mai tarbiyya da samar da ingantaccen ilimi da dora matasa a turbar rayuwarsu ta gobe da zata gina kasa.

Na takwas: Ko aikin daidaita hakkin ‘yan fansho da sauran bukatunsu tare da duk wanda abin ya shafa muka yi nasarar warware wa ya ishemu aikin alheri da alfahari a zamanmu na majalisa.

Na Tara: A matsayinsa na sanatan Kano Central zai tsaya ya bi kadin duk bukatun yankinsa da hakkoki na jiha da tarayya, tare da abokan aiki da shawara.

Na Goma: Mun shata wa kanmu wasu manufofi da zasu kaimu ga nasarar majalisa ta Tara. Daga cikinsu har da yin kokari matuka gaya a samu jituwa a tsakanin majalisa da bangaren zartaswa domin a yi wa Najeriya aiki.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

KWANKWASO YA MURKUSHE KUDIN ‘YAN FANSHO BILIYAN TARA

Daga Bello Muhammad Sharada:

A cikin hira da ake yi da Sanata Mallam Shekarau a yanzu ta gidan rediyon tarayya na Kaduna, ya yi bayani cewa a cikin shekara guda da barinsa daga kujerar gwamnan Kano, tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya murkushe kudaden da aka tara na ‘yan fansho har naira biliyan tara.

YA CE masu hakki ne ya kamata su binciki inda kayansu yake.

#SenIbrahimShekarauMedia

Ga Kadan Daga Kudurorin Da Sanata Ibrahim Shekarau Ya Gabatar

Kamar Yadda Al’umma Suka Zabi Mai Girma Sardaunan Kano Kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau.
Ga Kadan Daga Kudurorin Da Ya Gabatar Kamar Haka.
Bayan An Rantsar Da Yan Majalisa, Sun Zabi Shugabanin su.Sannan Sun Tantance Ministochin.
Ga Kadan Daga cikin Kudurorin.
1.Mal Dr Ibrahim Shekarau, Ya Kai Kuduri Akan Koyawa Malamai Da Dalibai Ilimin Kwamfiyuta(Computer) Na Primary Da Secondary.Tare Da Sanya Computer A Makarantun, Domin Dalibai Su Koyi Yadda Zasu Iya Zana Jarrabawar CBT, Tun Daga Matakin Primary Zuwa Secondary.
Wannan Kudurin Ya samu Karbuwa, Domin Samun Nasarar Jarrabawar Shiga Jami’oin, Wanda Hukumar JAMB, Ta Sanya Ya Zama Dole, Ga Duk Mai son Shiga Jami’a.
2.Kuduri Na Biyu, Shine Akan Karin VAT, Wanda Mai Girma Sardaunan Kano, Ya Nemi Da Majalisa Ta Rage Wannan Kudi A Kasafin Kudin Da Zasu Mikawa Gwamnati, Mai Girma Sanata Ya Ja Hankalin Yan Uwansa, Yan Majalisa Akan Ayi Duba Ga Halin Da Tattalin Arziki Yake A Hannun Mutane.
Daga Karshe Muna Kara Kira Yan Uwa Cewa Kadan Daga cikin Kudurorin Da Zamu Fara Kawo wa. A Biyo Dan Jin Wasu.
Sako Daga S4S.

#SenIbrahimShekarauMedia

Za mu kawo muku ayyukan ci gaba da Sen Ibrahim Shekarau zai kawo na ci gaba

Daga Abdullahi Ahmad Tadada:

A Yau Da Yardar Allah Zamu Kawo Muku Irin Ci Gaban Da Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, Zai Kawo wa Kasa, Jihar Kano Da Kuma Sanatorial Dinsa. Kasance Da Taskar S4S.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

KANO CENTRAL: Sabon Tsari

Daga Umar Faruq Muhammad:

Bayan ganawa da Shugabannin Mulki da Shugabannin Jam’iyyar APC na Kananan Hukumomin Kano ta tsakiya, a Jiya da Shekaran jiya Sanata Mal. Shekarau Sardaunan Kano yakara ganawa da Shugabannin Jam’iyyar da Kodinotocin sa na wadannan kananan Hukumomin.

Wannan yana nuna Sardaunan Kano ba da ka yake wakilcin mu, wakilci ne mai cike da ingantaccen tsari.

Tunda aka halicci Kano ta tsakiya bata taba yin gamo da Sanata mai gudanar da Wakilci bisa nutsuwa da tuntubar wakilan Al’umar Tsakiyar ba sai a wannan Karon.

Sardaunan Kano ya gamsu shi sanatan Tsakiyar Kano ne ba sanatan Arewa ba, shiyasa ma bai dorawa kansa Gantalin Jihohi ba a irin salon wancanen ka na Inuwar Giginya.

In sha Allahu Kanawan tsakiyar Kano zasuga Wakilci irin wanda suke bukata.

#SenIbrahimShekarauMedia

Kano Ta Tsakiya Sun Zabi Jajircen Sanata kuma Tsayayyen Namiji

Daga Abdullahi Ahmad Tadada:

Aiyyukan Da Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano,Yayi A Lokacin Da Ya Zama Ministan Ilimi Najeriya.
Abun Da Yasa Zamu Kawo muku Kadan Daga Cikin Aiyyukan Alheri Da Yayi Shine, Domin Sanin Cewa Al*Ummar Kano Ta Tsakiya Sun Zabi Jajirce, kuma Tsayayye Namiji, wakili Nagari.
Ga Kadan Daga cikin Aiyyukan.
1.A Satin Farko Daya Zama Ministan Ya Warware Ya Jin Aikin Da Aka Dade Anayi Tsakanin Ma’aikatan Polytechnic Da Na College Ilimin Najeriya.
2.Samar Da Kwamatin Gudanarwar A Jami’oin Da Aka Kafa Guda Goma Sha Daya. Wato Governing Council, wanda a lokacin Akai Wata Uku Ba’a Yi, Sai lokacin Da Ya Zama Minista. Misalin Federal University Dutse.
3.Mayar Da Federal College Of Education Zuwa University of Education, Misalin FCE Kano, FCE Zaria, FCE Akure Da Kuma Alva Ikoku.
4.Samar Da Hukumar NBAIS Wato National Board Arabic And Islamic Studies.
5.Samar Da Jami’oin Guda Tara. Misalin Ritman University Akwa Ibom.
6.Samar Da Sakamakon Da Zai Bawa Yan Arewa Damar Shiga Unity School. Sabanin Baya.
7.Samar Da Kudade Domin Tattance Bukatun Jami’oin, Domin Warware Matsalolin Jami’oin. Wato( Needs Assessment).
8.Biyan Bashin Tallafin Dalibai Wato Federal Scholarships.
9.Samar Da Tallafi Ga Dukkan Dalibin Da Zai Karanci Ilimin Koyarwa.
10.Samar Da Guraben Aiki Ga Dukkan Dalibin Da Yayi Kokari Ta Hanyar Samun Sakamako Mai Kyau. (Good Result).
Kadan Daga Aiyyukan Da Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Kuma Sardaunan Kano Mal Dr Ibrahim Shekarau Yayi A Ministan Wata Goma Da Yayi, Dan Haka Muka Kawo Abubuwa Goma.
Allah Ya Kara Masa lafiya Da Daukaka. Sannan Muna Nan Zamu Kawo Muku wanda Zaiyi A Matsayin Sa Na Zababben Sanatan Kano Ta Tsakiya.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Sakon taya murna ga Hon. Mahmud Madakin Gini

A madadin jagororin #S4S Alh. Salisu Indabawa da kuma Alh. Haruna Muhammad Gama (Garkuwar Sardauna) da kuma shugabanninta na jiha dana kananan hukumomi karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada muke amfani da wannan dama domin mika sakon taya murna ga Alh. Mahmuda Madakin Gini bisa nada shi S.A na Commerce da mai girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi.

Hakika wannan nadi anyi shi bisa chanchanta kuma an ajiye kwarya a gurbinta. Saboda haka ne muke addu’a da fatan Allah (S.W.A) ya sanya alheri ya taya shi riko. Allah ya kau da dukkannin wani abin ki. Allah kuma yayi riko da hannayensa yasa a gama lafiya. Allah yasa daga wannan kuma sai babbar kujera.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S,
05/01/2020.

#SenIbrahimShekarauMedia

MASANIN QABLI DA BA’ADI SHIKE LIMANCI

Daga Umar Faruq Muhammad:

Bayan ganawa da zababbun Shugabannin kananan Hukumomi na Kano Central wanda Sanatan Tsakiyar Kano yayi a ranar Alhamis, yau Litinin Sanatan yagana da Shugabannin Jam’iyyar APC na Kano ta tsakiya.

Duk fa wannan salo ne da Sanatan yakebi don gano bakin zaren ta yadda zaiyi amfani dashi don dinke duk wata baraka game da Wakilcin da Talakawan Tsakiyar Kano suka tura shi.

Kai da ganin wadannan Shirye-shiryen kasan Masanin hanya aka bawa tukin Motar.

Allah yasa laya tayi kyan rufi Sardauna.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau ya karbi bakuncin Hon Kwamishina Shehu Na’Allah Kura

Daga Abdullahi Ahmad Tadada: 6/1/2020

A Wannan Dare Mai Girma Kwamishinan Kudi Da Tattalin Arziki Na Jihar Kano Hon Shehu Muhammad Na’allah Kura. Ya Kaiwa Jagoranmu, Mai Girma Sardaunan Kano Kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau,Ziyarar Girmamawa. Tare Da Sanya Masa Albarka A Wannan Matsayi Da Mai Girma Gwamna Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam Ya Bashi Na Kwamishinan Kudi Da Tattalin Arziki.
Daga Karshe Mai Girma Sardaunan Kano Yayi Masa Adduar Samun Jagorancin Allah Akan Aikin Da Aka Dora Masa. Ka Tabbata Dan Halak Na Sardauna.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Bayan Daure Dauren Aure Da Ya Halarta…

Daga Abdullahi Ahmad Tadada: 5/1/2020

A Yau Mai Girma Sardaunan Kano Kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau, Bayan Daure Dauren Aure Da Ya Halarta. Sannan Ya Wuce Gidan Alh Aminu Alhassan Dantata, Inda Ya Yi Masa Jajen Gobarar Da Yayi A Gidan sa Dake Jihar Katsina. Inda Akayi Adduoin Ga Angwaye Na Allah Ya Sanya Musu Albarka Da Alheri. Haka kuma Anyi Addu’a Ga Gobarar Da Alh Aminu Alhassan Dantata, Allah Ya Mayar Masa Da Alheri, Ya Kiyaye Afkuwar Haka A Nan Gaba.
Allah Ya Taimaki Sardaunan Kano.
Allah Ya Kara Masa lafiya Da Daukaka.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Akwai mutukar kauna dayawa a tsakaninmu

Daga Nasir Harun Alfalaky Alkanawy:

Akwai mutukar kauna dayawa a tsakaninmu kuma Alhamdulillah domin Allah wannan kauna take shi yasa kullum Allah yake mana fiye da tunanin yan kwanta kwanta duk kuwa da irin mugun kai kawon su. Sardaunan Kano Allah ya kara mana kaunar juna domin zatinsa ya kara lafiya yaja kwana Baba ya kare karemu sharrin yayan Agwagwa.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau ya gana da shugabannin kananan hukumomi 15 na Kano Central

Daga Abdullahi Ahmad Tadada:

A Daren Jiya Alhamis, Mai Girma Sanatan Kano Ta Tsakiya Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano. Ya Gana Da Kwamishinan Kananan Hukumomi Na Jihar Kano Hon Murtala Sulen Garo, Da Shugaban ALGON Na Jihar Kano Hon Lamin Sani Kawaji Tare Da Dukkan Shugabanin Kananan Hukumomin Kano Ta Tsakiya, Da Kuma Wakilcin Wasu Daga Shugabanin,Wanda Mataimakansu Suka Wakilcesu.Da Shugaban Kwamatin Koli Na Gidan Mai Girma Sardauna Dr Umar Musa Mustapha Mai Munsileta, Sakataren Kwamatin Koli Hon Auwalu Dan Zabuwa Da Kuma Senior Legislative Aide Hon Nasiru S/Dinki.
Kuma An Tattauna Muhimman Abubuwa Da Ci Gaban Wannan Sanatorial Da Mal Yake Wakilta. Allah Ya Karawa Sardauna lafiya Da Taimaka Masa A Wannan Majalisa.
Daga Karshe Muna Yiwa Yan Uwa Barka Da Juma’a.
Sako Daga S4S

#SenIbrahimShekarauMedia

Ga Gwarzan Shekara Ta

Daga Abdullahi Ahmad Tadada:

Na Zabi Mal Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya. A Matsayin GWARZON SHEKARAR 2019.

#SenIbrahimShekarauMedia

Design a site like this with WordPress.com
Get started