SHARHI NA MUSAMMAN
DAGA Bashir Abdullahi El-bash:

-Nasarar Gwamna Ganduje A Kotu, Nasarar Dimokaraɗiyya Ce, Inji Shugaba Buhari
-Ta Tabbata Gaskiya Ta Yi Halinta, Kotu Ta Tabbatarwa Jama’ar Jihar Kano Abin Da Su Ka Zaɓa Da Hannayensu, Inji Gwamna Ganduje
-Ɗaukaka Ƙara Da PDP Da Abba Gida-Gida Da Kwankwasiyya Su Ka Yi, Tamkar Ɓata Kuɗi Da Lokacinsu Za Suyi, Cewar Tsohon Kwamishina, Muhammad Garba.
Yau Talata, 8 ga watan Octoba, 2019.
Ranar Laraba, 2 ga watan Octoba, 2019, rana ce wacce ta kasance ta farin ciki da murna ba ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kaɗai ba, har da ɗaukacin al’umma masoya da kuma masu yi wa Jihar Kano fatan alkhairi.
Tun bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 23 ga watan Maris, 2019, al’ummar Jihar Kano su ka samu nutsuwa da kwanciyar hankali, saboda sun gamsu zaɓen ya gudana cikin nasara da lumana.
A wannan rana, al’umma sun gudanar da bukukuwa da shagulgulan murnar wannan nasara da mai girma gwamna ya samu a dukkan loko da saƙo na ƙananan hukumomin Jihar Kano (44) kowa ya ji a ransa cewar wannan nasara tasa ce.
Amma abin mamaki, sai ga jam’iyyar (PDP) da ɗan takararta na gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) da kuma rusasshiyar ƙungiyar nan ta Kwankwasiyya sun yanke shawarar ƙalubalantar wannan nasarar da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna
Abba Kabir, bisa jagorancin mai gidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso, sun tattara hujjojin da ba su inganta ba sun miƙawa manyan lauyoyinsu, waɗanda su da kansu sun riga sun san cewar sun ɗauki dakon shari’ar da ba nasara za su samo ba.
Bayan shafe tsawon watanni uku lauyoyi su na fafutukar sauya haƙiƙanin al’amuran da su ka faru tare da gabatar da hujjoji masu rikitarwa waɗanda ba su inganta ba.
Lauyoyin mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da na hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), haɗe da na jam’iyyar (APC), cikin nutsuwa da bin ƙa’ida sun kare shari’ar tare da gabatar da sahihan hujjojin da su ka rusa dukkan zarge-zarge marasa hujja da masu ƙara su ka gabatar a gaban kotun.
Kamar yadda aka tsammata, a ranar yanke hukuncin ƙarshe, mai shari’ar da ta jagorancin zaman yanke hukuncin, mai shari’a Halima Shamaki, bayan shafe tsawon awanni uku ta na gabatar da bayanai, daga ƙarshe ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar (PDP) ta shigar ta na ƙalubalantar nasarar da gwamna Ganduje ya samu a zaɓen 9 da 23 ga watan Maris ɗin shekarar (2019).
Kotun ɗaukaka ƙarar ta bayyana rashin hujjoji gamsassu daga masu ƙara (PDP) a matsayin dalilan da su ka sanya ta yi watsi da ƙarar da su ka shigar su na ƙalubalantar nasarar ta gwamna Ganduje a zaɓen gwamna na shekarar (2019).
Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma ƙara da bayanin cewa soke sakamakon zaɓukan Mazaɓar Gama da na wasu Mazaɓu da aka yi su ka kuma haifar da sake maimaita zaɓen cike giɓi, ba wai batu ba ne na doka kawai, zaɓen ya zama karɓaɓɓe.
Mai shari’a Shamaki ta kuma ƙara da cewa, “Bambancin shi ne akwai ƙuri’un da ake nema a mazaɓar gama guda (128,000) idan aka haɗa su da ƙuri’u (26,000) na ɗan takarar jam’iyyar (PDP) Abba Kabir Yusuf. Dan haka akwai buƙatar a gudanar da wannan zaɓe zagaye na biyu na ranar 23 ga watan Maris, 2019 domin kammala zaɓe gaba ɗaya.
Sai kuma mai shari’a Shamaki ta ƙara da shaida cewa, matakin da hukumar zaɓe ta (INEC) ta ɗauka na bayyana zaɓen 9 ga maris a matsayin wanda bai kammala ba, da kuma sake shirya zaɓen cike giɓi da ta yi, ya yi daidai matakin ya na kan turbar doka da ƙa’ida cikin kundin tsarin mulkin ƙasa da tanade-tanaden dokokin zaɓe.

Sannan kuma ta ƙara da tabbatar da cewa masu ƙara ba su iya gabatar da hujjoji gamsassu ba.
Daga nan kuma mai shari’a Halima Shamaki ta ƙara da cewa matakin sake zaɓe ba wai na iya hukumar zaɓe ta (INEC) ba ne, hatta su kansu jam’iyyun siyasa ciki har da jam’iyyar da ta kawo ƙarar, duk sun gamsu da matakin gudanar da zaɓen na cike giɓin.
Tun bayan da labari ya bazu cewar kotu ta yi watsi da wannan shari’a, al’ummar Jihar Kano su ka bazama kan tituna cikin shauƙi da murnar wannan nasara, wanda hakan ke nuni da kotu ta tabbatar da abin da su ka riga su ka sani, hukunci na gaskya.
Wannan shi ne yadda gwamna Ganduje, cikin shara ɗaya ya binne Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar (PDP) da ƙungiyar Kwankwasiyya a kabarin da ke cikin maƙabartar siyasa, abin da ba su taɓa tunanin fuskanta ba.
Cikin jawabinsa jim kaɗan da bayyana sakamakon hukuncin kotun, gwamna Ganduje ya bayyana cewa “gaskiya ce ta yi halinta”
“A lokacin da aka gudanar da wannan zaɓe mun samu nasara, amma jam’iyyar adawa ta (PDP) ta ƙalubalanci wannan nasara da mu ka samu zuwa kotun shari’un ƙararrakin zaɓe. Sai dai kuma, yanzu ta bayyana a fili ga kowa nasarar tamu ce, kotun ta tabbatar da hakan”.
Daga nan kuma sai gwamna Ganduje, ya ba da tabbacin samar da adalci ba tare da nuna wariya ko wani bambancin ga kowa ba. Kamar inda ya ke cewa:
“Ni gwamna ne na kowa ba tare da nuna bambanci ba, kamar yadda hakan ke ƙunshe cikin manyan manufofin jam’iyyarmu ta (APC)”. Inji Gwamna Ganduje.
Sai kuma ya cigaba da ba da tabbacin yin tafiya da kowa cikin buɗaɗɗiyar gwamnati kamar yadda ya faro a zangon mulkinsa na farko, “zan cigaba da yin aiki tuƙuru cikin juriya da sadaukarwa domin kyautata rayuwar al’ummata a wannan Jiha tamu abar alfaharinmu”. Inji Gwamna Ganduje.
A ƙarshe kuma sai gwamna Ganduje ya sake jaddada saƙon godiyarsa ga al’ummar Jihar Kano da su ka sake zaɓarsa a zangon mulki na biyu, sannan kuma su ka cigaba da yi masa addu’a kan ƙalubalantar nasararsa da ƴan adawa su ka yi a kotu, har zuwa wannan lokaci da Allah ya ba shi wannan nasara a kotun.
“Yau rana ce ta murna da farin ciki, ya yin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta tabbatar mana da nasarar da Allah ya ba mu a sanadiyyar zaɓen da al’umma su ka yi mana tun a baya”. Inji Gwamna Ganduje.
“Wannan nasara ce ga dimokaraɗiyya’ -Inji Shugaban Nageriya, Muhammadu Buhari.
A saƙon taya murna da ya aike, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana nasarar gwamna Ganduje a matsayin nasara ga dimokaraɗiyya.
Shugaban na Nageriya, ya bayyana yadda shari’ar ta gudana a matsayin nasara ga dimokaraɗiyya. Tare da godewa al’ummar Jihar Kano kan yadda su ka martaba zaman lafiya, su ka bi hanyoyin shari’a kamar yadda doka ta tanadar a dimokaraɗiyya.
Dangane da abubuwan da su ka faru a daga zaɓe da kuma hukuncin kotu, shugaba Muhammadu Buhari ya hori gwamna Ganduje kan cigaba da samar da haɗin kai a Jihar Kano domin tunkarar cimma ƙudurorin jam’iyyar (APC) na kyautata rayuwa da samar da walwala ga al’umma. Shugaba Buhari ya faɗi haka ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban jami’insa na musamman kan harkokin watsa labarai, Mallam Garba Shehu.

“Kada ku ɓata ƙarfi da kuɗaɗenku, shawarar Muhammad Garba ga jam’iyyar (PDP).
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai, Mallam Muhammad Garba, ya shawarci jam’iyyar (PDP) da ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir Yusuf da su rungumi ƙaddara su janye ƙudurinsu na sake ɗaukaka ƙara a kotu ta gaba
Muhammad Garba da ya ke jawabi la’akari da zaman lafiya da kuma cigaba gami da yadda yadda siyasar Jihar Kano ta kai matakin cikar nagarta, ya buƙaci Abba Kabir yusuf da ya rungumi shan kaye cikin girma da daraja.
Ya bayyana cewa, la’akari da yadda kotun ta gudanar da saurare game da yanke hukunci kan shari’ar, (PDP) ba ta iya gabatar da hujjoji gamsassu kan zargin da ta ke yi ba.
Muhammad Garba ya kuma nazarci cewa, jam’iyyar (PDP) da ɗan takararta, babu wata shari’a da za su ɗaukaka ƙara akai duba da yadda su ka gabatarwa da kotun farko raunanan hujjojin da ba su inganta ba kan zargin ba daidai ba da su ke tunanin an yi a ya yin zaɓen gwamna.
Daga nan kuma sai tsohon kwamishinan ya buƙaci al’ummar Jihar Kano musamman ma magoya bayan jam’iyyar (APC) da su cigaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da lumana, ka da su yarda su sanya kansu cikin duk wata tarzoma domin jami’an tsaro ba za su lamuci karya doka da rusa zaman lafiya a Jihar Kano ba.
Bikin cikar Nageriya shekaru (59) da samun ƴancin kai, gwamna Ganduje ya buƙaci kauda bambance-bambancen da ke tsakani domin ciyar da ƙasa gaba.
Gabanin shagulgulan murnar samun nasara a kotu, albarkacin cikar Nageriya shekaru (59) da karɓar ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka na Ingila, gwamna Ganduje ya buƙaci dukkan ƙabilun da ke Jihar Kano da su kauda bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin ɗorewar zaman lafiya da kuma haɗin kai da Jihar gaba.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a filin wasa na tunawa da marigayi Janar Sani Abacha da ke Ƙofar Mata, tare da jan hankali kan batun haɗin kan ƙasa a madadin rarrabuwa.
“Bambance-Bambancen da ke tsakaninmu ta fuskar al’adu da kamance, ka da ya zama abin da zai haifar mana da rarrabuwa, mu fahimci bambance-bambancen domin mu zauna lafiya cikin girmama juna”.
Gwamna Ganduje wanda mataimakinsa, Dakta Nasiru Yuauf Gawuna ya wakilta, ya bayyana taken taron na bana da “zaman lafiya kan haɗin kai da gina ƙasa” duba da matsalolin hantara da ƙyamar juna gami da nuna bambance-bambancen yanki da shiyya da rashin zaman lafiya a tsakankanin al’ummun yankunan wannan ƙasa.
Sannan kuma gwamna Ganduje ya yi tsokaci kan batun cigaba da wayar da kan matasa dangane da kyawawan halaye da ɗabi’u kan batun zaman lafiya da haɗin kai domin samar da cigaba mai ma’ana a Jiha da kuma ƙasa gaba ɗaya. Kamar inda ya ke cewa:
“Matasanmu jari ne mai girma a tattare da mu, mun yi imani cewa ƙaddararsu ba wai ta na nufin matsayinsu kenan ba a rayuwa, a matsayinmu na iyaye ko gwamnati, ko al’umma, ba za mu zuba ido mu ƙyale su kara zube ba, za mu cigaba yi musu uzuri da ƙoƙarin ganin sun fita daga cikin mawuyacin halin da su ke ciki domin samun kykkyawar rayuwa”.
Wannan gwamnatin tamu, ta tallafawa matasa sama da mutum (200,000) a zangon mulkin farko, kuma za mu cigaba da ganin mun daƙile matsalolin da matasanmu su ke fuskanta a wannan Jiha.
Gwamna Ganduje ya kuma cigaba da cewa, a cikin shekaru huɗu da su ka gabata, gwamnatinsa ta samu nasarar cimma managartan nasarori a fannin ilimi da na lafiya da na tsaro da na noma da kuma manyan ayyukan raya Jiha da samar da ayyukan yi. Kuma a yanzu ma a wannan zango na biyu za ta ɗora daga inda ta tsaya ne domin cigaba da samar da ƙarin ɗumbin nasarori.
“Mun yi dogaro da cewa hanya mafi a’ala ta samar da ilimi ga waɗanda su ka cancanta ita ce ta ba da ilimi kyauta, kuma mun bayyana ƙudurinmu na fara bayar da ilimi kyauta tun saga firamare har zuwa babbar sakandire, kuma kowa ya gani a cikin watan da ya gabata mun fara aiwatarwa.
“Ina mai farin cikin tabbatar muku cewa, za mu cigaba da kyautata makarantunmu na gwamnati tare da tabbatar da cewar yaranmu sun samu horo mai inganci. Za kuma mu cigaba da horar da malaman hanyoyi da dabarun koyarwa irin na zamani domin samun kykkyawan sakamako cikin ajujuwa.
A fannin ƙoƙarin gwamnati wajen inganta sashen lafiya kuwa, gwamna Ganduje ya bayyana cewa fannin lafiya a Jihar Kano ya karɓi manyan nasarori a cikin shekaru huɗu da su ka gabata, inda gwamnati ta kammala aikin ginin asibitin Mallam Isyaka Rabi’u da Kuma Muhammad Buhari Specialist Hospital gami da sabuntawa da kuma ɗaga darajar wasu asibitocin tare kuma da samar musu da kayan aiki irin na zamani da kuma samar ƙarin cibiyoyin lafiya sama da guda (300) a sassa daban-daban na Jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya kuma ƙara da cewa akwai tsare-tsare na cigaba da samar da ayyukan raya jiha a dukkan birane da karkara inda za a cigaba da samar da tituna da gadojin sama da na ƙasa domin kyautata harkokin sufuri ga al’umma da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jiha.
Sauran fannonin da gwamnatin gwamna Ganduje ta samu nasarar cimma managartan nasarori har da batun samar da wadataccen abinci a Jiha da kuma daƙile matsalar rikicin fulani makiyaya da manoma matsalar da ke barazana ga harkar tsaro da batun zaman lafiyar ƙasa. daƙile matsalar rikicin fulani makiyaya da manoma, matsalar da ke barazana ga harkar tsaro da batun zaman lafiyar ƙasa.
#SenIbrahimShekarauMedia
You must be logged in to post a comment.