Daga Datti Assalafiy
Masoyina Maigirma Sardaunan Kano, Sanatan Kano ta tsakiya Malam Dr Ibrahim Shekarau (Khadimul Islam)

Idan kana neman ‘dan siyasa a Nigeria da ya taimaki addinin Musulunci a fili da boye ka samu Sardaunan Kano to magana ya kare.
Idan kana neman ‘dan siyasar da yayi sanadin musuluntar da dubbannin maguzawa zuwa cikin addinin Musulunci ka samu Maigirma Sardaunan Kano magana ya kare.
Idan kana neman ‘dan siyasa mai kishin addinin Musulunci, wanda yayi ta fashi fadi har gwamnatin Nigeria ta tabbatar da jami’an tsaro na Musulunci wato rundinar Hisbah a bisa doka to shine Malam Ibrahim Shekarau.
Idan kana neman ‘dan siyasa da ya gina masallatai a arewacin Nigeria da kudanci wanda bai san adadinsu ba ka samu Maigirma Sardaunan Kano magana ya kare.
Idan kana neman kwararren dan siyasa da bai yarda da bangar siyasa ba, ka samu Maigirma Sardaunan Kano magana ya kare.
Idan kana neman ‘dan siyasa da ya gina al’umma, wanda abin hannunsa bai dameshi ba, na talakawansa ne, ka samu Sardaunan Kano magana ya kare.
Idan kana neman ‘dan siyasa da ya san darajar mutane, ya san darajar talakawanshi, yake halartan daurin aurensu da yin ta’aziyya ga talakawanshi idan ka samu Sardaunan Kano magana ya kare.
Idan kana neman ‘dan siyasa da yake katse dukkan aikin da yakeyi koda a gaban shugaban Kasa yake, da zaran lokacin Sallah yayi fita yake ya tafi Masallaci ka samu Maigirma Sardaunan Kano to magana ya kare.
Idan kana neman ‘dan siyasa daga arewa, wanda ya amsa sunan Malamin makarantan boko, ya san sirrin karatun boko, ya taka babban matsayi a karantarwa har ya zama Ministan ilmi ka samu Sardaunan Kano magana ya kare.
Idan kana neman ‘dan siyasa da ya karanta addinin Musulunci karatu na gaske, ya rubuta litattafai na addinin Musulunci ka samu Maigirma Sardaunan Kano magana ta kare.
Idan kana neman ‘dan siyasar da a duk lokacin da ya gabatar da sallah na farillah sai ya tashi yayi wa’azi irin na addinin musulunci, ya tunatar da mutane Allah (SWT) da Manzo (SAW) ka samu Sardaunan Kano to magana ya kare.
Shine Sanatan da a ranar da aka sanar da sakamako yaci zaben Sanata, masoyansa suka cika gidansa, aka sa min a waya ina sauraransu suna ta karatun Qur’ani don bayyana godiyarsu ga Allah Madaukakin Sarki, wanda wannan itace irin tarbiyyan da Maigirma Sardauna ya baiwa magoya bayanshi.
Me yasa Datti Assalafiy yake goyon bayan siyasar gidan Sardaunan Kano?
Idan kana neman dalilan to ga su can a sama, duk wanda yake da ja a kan haka to ina kalubalantarsa da kwararan hujjoji.
Shine ‘dan siyasar da a duk lokacin da na yi waya dashi, ko wani ya hadani dashi mukayi waya, ba zamu kare wayar ba sai ya saka min albarka saboda shima ‘dan albarka ne.
Maigirma Sardauna ja gaba muna binka a baya, don munsan ba zaka kaimu zuwa ga tafarkin halaka ba, sai dai hanyar tsira a duniyarmu da kuma lahirar mu.
Hoto na farko, Sardaunan Kano Khadimul Islam Malam Ibrahim Shekarau (Hafizahullah)
Hoto na biyu, Lambar yabo ne wanda dakarun social media na gidan Sardaunan Kano suka karramani dashi saboda Allah.
Yaa Allah Ka taimaki Salihin bawanKa Malam Ibrahim Shekarau, Ka daukaka mana darajarshi, Ka bashi nasara akan dukkan kyawawan manufofinshi Amin.
#SenIbrahimShekarauMedia
You must be logged in to post a comment.