EFCC ta fara binciken tsofaffin shugabannin kasar Najeriya

Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa a Najeriya EFCC ta fara binciken tsofaffin shugabannin kasar Najeriya Obasanjo, ‘Yar Adua da Jonathan akan badakalar kudi kimanin dalar America biliyan goma sha shida ($16bn) na samar da hasken wutar lantarki a Najeriya.

#SenIbrahimShekarauMedia

Eid-El-Kabir Tare Da Sanata Ibrahim Shekarau

Lahadi 11/8/2019 Mai girma Sardaunan Kano, Sanata Mallam Ibrahim Shekarau CON ya halarci masallacin eid na kofar mata dake birnin Kano domin yin sallah Eid-El-Kabir.

Allah ya maimata mana ta badin badada, Allah ya kara mana lafiya da zaman lafiya, kwanciyar hankali, ya kara yalwata arzikin mu.

#SenIbrahimShekarauMedia

Najeriya tasha addu’oi a Kasar Saudi Arabia

A yau yayin hawan Arfa a Kasar Saudi Arabia wasu shugabanni da mashahuran malamai sun yi wa Kasar Najeriya addu’oi na masamman domin samun dorewar zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasar arziki.

Muna fatan Allah ya amsa addu’oin kuma suma muna fatan Allah ya karbi aikin hajjin da suka gudanar.

Mun sami wannan labari daga jaridar RARIYA.

#SenIbrahimShekarauMedia

Ina Son Zanyi Yabo Da Jinjina Ga MD Karota Wato Hon Dr Baffa Babba Dan Agundi, A Irin Ceto Da Kuma Dawo Da Martabar Jihar Kano Da Yayi.
Musamman A Ofis Din Sa Na Hukumar Karota,Gaskiya Kayi Abun Da Ya Kamata A Yaba Maka, Saboda Irin Ci Gaban Da Ka Kawo. Allah Ya Tabbatar Da Duga Duganka Akan Hakan.
Sannan Kuma Al’umma Suna Bamu Sakon Godiya Da Yi Maka Addu’ar Gamawa lafiya.
Allah Ya Taimaki Khadimul Islam
Allah Ya Taimaki Dr Baffa Babba
Allah Ya Taimaki Jihar Kano Da Hukumar Karota.
Sako Daga S4S

Quran 2:14

وَإِذَا لَقُوا الَّذِينَ آمَنُوا قَالُوا آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْا إِلَىٰ شَيَاطِينِهِمْ قَالُوا إِنَّا مَعَكُمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِئُونَ

And when they fall in with those who believe, they say: We believe; but when they go apart to their devils they declare: Lo! we are with you; verily we did but mock.

WACCE RAWA KUNGIYAR KWADAGO KE TAKAWA A KANO?

Daga Umar Faruq Muhammad:

Lokacin da Gwamnatin Mal. Ibrahim Shekarau tayiwa Ma’aikatan Jihar Kano karin albashi na #12,500 Minimum wage an cimma matsaya tsakanin Gwamnatin da Kungiyar Kwadago cewa tunda Gwamnatin tana bawa Ma’aikata Kudin Gero da na Rago za’a dena bada kudin hutu (Leave Grant) tunda ga Albashi nan an kyautata shi, a lokacin da akayi wannan karin #6500 ne Minimum wage din.

Kaga dai ba karamin gata akayiwa Ma’aikata ba, ga rubin albashi sannan ga kyautar rabin albashi sau biyu a shekara, janye leave grant bazai cutar da Ma’aikata ba.

Lokacin da Dr. Rabi’u Kwankwaso yadawo a karo na biyu yayi amfani da Majalisar dokoki wajen rushe dokar Ramadhan da Ram bonuses tare da maidata sai anga dama, tunda yayiwa Ma’aikata kudin goron dubu biyar-biyar sau biyu a Mulkin sa har yau Gwamnatin Kano bata kara ganin damar bada bonuses din ba.

Shin wacce Rawa NLC ta Kano ke takawa don dawowa da Ma’aikata kudin su na hutu tunda duk Jihohi na bayarwa?

Magana ta gaskiya in NLC basu nemo wannan hakkin ba basu sauke nauyin dake kansu ba, da ace ana biyan bonuses din can da babu laifi in Kwadago ta tsuke bakinta.

#SenIbrahimShekarauMedia

Yaushe sabon albashin ma’aikata zai fara aiki?

Sanin kowa ne a ranar 18/4/2019 maigirma shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya rattaba hannu akan sabon tsarin albashin ma’aikata wanda akace zai fara daga wannan rana da shugaban kasar yasa hannu yau fiye da watanni uku kenan.

Shi wannan tsarin albashin an tsuguna an tashi tsakanin kungiyoyin kwadago da jami’an gwamnati har tsayin kusan shekaru uku, ana neman yadda gwamnati zata amince dashi, inda daga karshe aka cimma daidaito.

Bayan da shugaban kasa Buhari yasa hannu, ya amince a biya mafi kankantartar sabon albashin na dubu talatin (#30,000) ne, sai farashin kayayyaki a kasuwanni daban-daban kama daga masu saidai kayan masarufi dana gini da sufuri da sutura da abinci da dai sauransu sukayi tashin gwauron zabi.

A gefe guda kuma, su ma’aikatan har zuwa yanzu basuji komai a asusun ajiyar kudin albashin nasu ba, kamar yadda labari yake ishemu cewa, har ya zuwa yanzu ana ta takaddama game da yadda gwamnati zata iya biyan albashin, ma’ana har yanzu akwai sauran rina a kaba, duk da gwamnati tace, sabon albashin ya fara daga lokacin da shugaban kasa ya rattaba hannu, shi kansa taruwar bashin ariyas akan gwamnatin wata barazanace ga ma’aikatan, domin idan lokaci yayi nisa, zai kawo takaddama tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati wajen biyan bashin da ya taru a kansu.

Haka kuma farashin kasuwanni zuwa yanzu, yana kara gurgunta al’amuran tattalin arzikin aljihun ma’aikatan, inda ma’aikatan ke dandanar azabar rashin karin albashin, har ma sun gwammace an tsaya kamar yadda ake a baya, kafin ayyana karin sabon albashin da sa hannun shugaban kasa Buhari yayi.

Muna kira ga gwamnati ta tausayawa ma’aikata da iyalansu, kasancewarsu kashin bayan tafiyar da gwamnati kuma masu habaka tattalin arzikin kasa, saboda duk lokaci da ma’aikaci ya sami kudi bashi da burin ajiyewa a asusun ajiya, illa dai ya shiga kasuwa ya sayi abubuwan da yake da bukata, ma’aikaci ne yake baza kudi a hannun jama’a a kasuwanni, yin hakan shine karuwar tattalin arziki da walwalar jama’a.

#SenIbrahimShekarauMedia

CNG: Ba ruwan mu da shirin yin fito-na-fito da hukumomin.

Jimlar hadakar kungiyoyin Arewa da aka fi sani da The Coalition of Northern Groups (CNG) sun gana da manema labarai ranar Lahadi 4/8/2019 inda suka sanar musu cewa, anja hankalinsu domin yin wani gangami da wata kungiya ta tsara gudanarwa daga Litinin 5/8/2019, (CNG) ta fada da kakkausan harshe cewa, ta tsame hannunta daga kiraye-kirayen yin gangamin fito-na-fito da gwamnati.

Kungiyar ta fadi haka ta bakin kakakinta Abdul-Azeez Suleiman, yace, “ba mu gamsu da wannan yunkurin kawo tarzoma wanda wasu daga waje ke kokarin haifarwa a Najeriya ba, muna sane da irin burinsu na tarwatsa kasashen Africa, misali a Libya, Syria, Sudan da Yemen, ba zamu shiga abinda zai kawo wa kasarmu da al’ummar mu koma baya da yin da na sani ba.”

“Abinda kungiyoyin mu na Arewa zasu iya shiga, shine abinda zai kawo mana cigaba, mutunci, girmamawa da zama a bisa teburin shawara idan muna da wani sabani da hukumomi domin warwarewa cikin ruwan sanyi.”

“Don hakan muna shaida muku ba zamu shiga wata boyayyiyar manufa tare da mutanen da tuntuni suke kokarin ganin bayan Arewa ba.”

#SenIbrahimShekarauMedia

DSS: Mun kama Omoyele Sowore domin kokarin hargitsa Najeriya

Jami’an tsaron sirri na farin kaya (DSS) sunce, sun bankado wani sirrin hadin baki tsakanin kasashen ketare da mai fafutikar chanja gwamnatin Najeriya ko ta halin yaya Omoyele Sowore domin kawo hargitsi a kasar.

A dakacemu…

#SenIbrahimShekarauMedia

SHIRIN TALABIJIN NA RAHMA SHIRIN REDIYO NA RAHMA

Gidan talabijin Na RAHMA a shirin MIKIYA zan gabatar da tattaunawa ta musamman akan matakin da gwamnatocin jihohin North West suke dauka akan matsalar tsaro, haka za a yi magana akan shigowar Farfesa Attahiru Jega cikin siyasar jam’iyyar PRP da ma’aikatun da ake sa rai za a tura ministocin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya aika wa Majalisar dattijai kuma aka tantance su.

ZA A YI TATTAUNAWAR KARFE 7 da kuma karfe 10 Na dare a ranar Lahadi 04 August 2019. Ana kama tashar RAHMA TV a StarTimes 178

A shirin zaman yan Marina a tashar Rediyon FM RAHAMA 97.3. Zan yi awa guda live” akan yadda aka raba shugabannin kwamitoci a Majalisar dattijai da tarayya da yadda jihar Kano ta rabauta da ministoci biyu da aikin da ke gabansu na raya Kasa

ZA A YI TATTAUNAWAR KARFE 10 Na safe a ranar Litinin 05 August 2019 a mita 97.3 zangon FM.
Nagode
Dan uwanku Bello Muhammad Sharada

#SenIbrahimShekarauMedia

Jami’an tsaro sun gargadi iyaye su kula da yaransu karsu shiga zanga-zangar kawo fitina

Wata kungiya mai suna #RevolutionNow wacce wani dan jarida kuma dan siyasa mai suna Omoyele Sowore ke jagoranta, domin kokarin tirsasa chanja gwamnatin Najeriya.

Helkwatar yan sanda karkashin babban sifeton yan sanda na kasa Muhammad Adamu tace, wannan kungiyar haramtacciyace kuma cin amanar kasa ne tare da kokarin kawo hargitsi a kasar da ake mulkin dimokaradiyya wacce keda lokacin zaben shugaba da chanja shugaban bisa doka a matakin zango-zango.

Duk wani kokarin tirsasa chanjin gwamnati ta wata hanya ba wannan ba, haramun ne, cin amanar kasa ne, ta’addanci ne, tayar da hankalin al’ummar kasa ne, sakamakon haka jami’an yan sanda sunce, bazasu lankwashe hannayensu wajen zuba ido hakan ta faru ba.

Wannan kungiyar, ta shirya zanga-zanga a fadin Najeriya ranar Litinin 5/8/2019 domin su tirsasa chanja Gwamnatin Najeriya, don haka jami’an yan sanda suna kira ga al’umma su kaucewa wannan zanga-zanga haka kuma iyaye kar su bari ayi amfani da yayansu a wannan rana domin kawo hargitsi a kasa.

Jami’an yan sandan sunce, zasu fito domin kare mutuncin kasa da rayukan al’umma da dukiyoyinsu, don haka duk mai shirin fitowa domin yin wannan zanga-zanga ya kuka da kansa, Idan kunne yaji, jiki ya tsira.

#SenIbrahimShekarauMedia

Ayi siyasa ba da gaba ba

Hoto mai magana yayin da aka shiga kotun korafin zaben gwamna a Kano

Shin ko menene ra’ayinka akan wadannan hotuna da kake gani?

#SenIbrahimShekarauMedia

Falalar Goman Farko Na Watan Zul Hijja

A yau juma’a daya ga watan Musulunci mai Alfarma wato watan Zul Hijja na shekara ta 1440.

Ga wasu daga cikin falalar wannan wata da kuma abubuwan da ake bukatar Musulmi mu yi don samun ribar wannan watan:

* Allah yayi rantsuwa da wannan ranaku a cikin alqur’ani maigirma

‎الفجر وليال عشر

Jamhurun malamai sun fassara wannan ranaku da goman farko na Zul Hijjah Alhafiz Ibn Kasir cikin tafsirinsa yace “wannan shine magana mafi inganci”

* Idan watan Zul Hijjah ya tsaya babu kyau ga wanda keda niyan layya yayi aski ko yankan faratu annabi ya hani da hakan. Duba cikin sahihu muslim1977

* Jigajigan rukunan musulunci ana samunsu ne cikin Zul Hijjah
~Tauhidi yadda alhazai suke talbiya
~Sallah ta idul adha
~Azumi ta yadda wanda bai samu hadaya ba zai yi azumi uku a aikin hajji bakwai inya dawo gida
~Sadaka tayadda wanda yayi tamattu’i ko kirani zai hadaya a rabawa miskinai da mabukata
~Aikin hajji da wannan babu wani watan da ake samun wannan aiyukan gaba ki daya sai cikin Zul Hijjah.
Duba cikin fathul-bari juzu’i na 2 shafi na 460
* Aikin hajji na kankama ne cikin goman farko tun daga ranar takwas zuwa ranar sha uku ga wata
* Ranar Allah yafi yanta bayi daga wuta cikin goman farko ne wato ranar Arfa.
* Cikin goman farko Allah ya umarci alhazai su ambace shi a Masha’arur-haram wato ranar goma ga wata

* Azumin ranar Arfa na cikin goman farko ne wanda ake ranar tar ga wata ga wanda keda ikon yi kuma bai samu zuwa aikin hajji ba Azumin na kankare zunubai.

* Cikin goman farko ake kabarbari sabanin sauran watanni kana ma الله اكب الله اكبر لا اله الا الله الله اكبر الله اكبر و لله الحمد
Abu Huraira da Abdullahi Ibn Umar suna fita kasuwa cikin goman farko suna kabarbari mutane suna kabbara da kabarbarinsu. duba cikin fathul bari juzu’i na 1 shafi na 458 cikin hadisin Abdullahi bn Umar yace Manzon Allah s.a.w yace
‎ما من ايام اعظم عند الله و لا احب اليه من العمل فيهن من العشر فأكثيرو فيهن من التهليل واتكبير واتحميد
Ma’ana Manzon Allah s.a.w yace Babu wata rana da aiki na gari yafi daukaka da soyuwa ga Allah fiye da kwanaki goma na farkon Zul hijjah saboda haka ku yawaita wadannan kalmomin
La’ilaha illalah Allahu akbar walillahil hamd

* Hafsa bint Umar radiyallahu anha tace
‎اربع لم يكن يدعهن انبي صل الله عليه وسلام صيام عشوراء والعشر و ثل ثة ايام من كل شهر والركعتين قبل الغداة
Ma’ana abubuwa hudu Manzon Allah s.a.w baya taba barinsu
~Azumin Ashura daya ga watan Muharrah
~Azumin goman farko na Zul Hijjah
~Azumin kwanaki uku a kowane wata
~Raka’a biyu kafin sallar asubahi
Musnad Imamu Ahmad Ibn Hambal hadisi na 25,920

* Cikin wannan wata ne aka cika mana addini wato ranar Arfa kamar yanda Buhari ya ruwaito 4606

* Fiyayyen addua itace adduar ranar Arfa tara ga watan Zul Hijjah

* Watan Zul Hijjah shine cikamakin watanni sanannu wanda Allah yace الحج اشهر معلومات

* Kuma cikin watan Zul Hijja ne Allah ke alfahari da bayinsa da suka halarci Arafa
Allah yasa mu dace Amin

Sen Ibrahim Shekarau
(Sardaunan Kano)

#SenIbrahimShekarauMedia

FRSC: Bamu da ikon karbewa driver takardun mota

Hukumar kare hadurra ta kasa wato Federal Road Safety Commission (FRSC) tace, babu wani jami’inta dake da ikon karbewa driver takardun motar sa, abinda kawai zasu iya karbewa driver shine license na tuki yayin da driver ya karya dokar tuki saboda shine mallakin gwamnatin tarayya.

Kwamandan rundunar ta Ilorin Zakari Muhammed shine ya bayyana haka yayin gabatar da wata lacca a wani taro na masu ruwa da tsaki.

Shima jami’in kula da shari’a na hukumar, Kayode Ajibike yace, jami’ansu na da hurumin janye motar duk wani driver daga kan titi zuwa ga hukumar yan sanda matukar ya aikata laifi, ya dada da cewa, duk wanda yasan bai aikata laifin da hukumar ke tuhumarsa da aikatawa ba, to yana da damar kalubalantarsu.

#SenIbrahimShekarauMedia

Gwamnatin Tarayya zata samar da tashar sauke kaya a Kano

Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen tabbatar da tashar sauke kaya wacce bata shafi ruwan teku ba.

Wannan cibiya da aka fi sani da Dala Inland Dry Port, idan aka tabbatar da ita za ta habaka tattalin arzikin yankin Arewa maso Yamma dama kasa bakidaya.

Babban Darakta mai kula da hukumar samar da jujjuya ayyukan cigaba na Gwamnatin Tarayya (ICRC) Engineer Chidi Izuwah Snr, yayi tattaki zuwa Kano domin duba yadda za’a ci gaba da wannan aiki a Unguwar Zawaciki ta Karamar Hukumar Kumbotso.

Daraktan ya tabbatar da cewa, zai yi duk abinda zai iya domin ganin cigaban aikin tare da magance duk wani abu da zai dakatar ko kawo matsala gareshi, haka kuma ya bayyana cewa wannan aikin zai samar da ayyukan yi ga matasa, sannan kuma zai kawo hanyoyin kasuwanci su habaka inda kai tsaye za’a shigo da kayayyaki daga kasashen waje haka kuma zai bada damar fitar da kayayyakin da muka noma zuwa kasashen waje.

Yayi kira ga Gwamnatin jihar Kano ta samar da hanyoyin mota, wutar lantarki da ruwa a inda za’a gudanar da aikin kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

A jawabinsa na maida martani Shugaban wannan tasha ta Dala Inland Dry Port Alhaji Ahmad Rabi’u yace, yayi farin ciki ganin za’a ci gaba da wannan aikin da aka faro shekaru ashirin baya, yace tuni Gwamnatin Jihar Kano ta sa aikin titinan da zata gina a wannan waje a cikin kasafin kudi na bana, wato 2019.

#SenIbrahimShekarauMedia

Ban taba tunanin zan zama Minista ba a rayuwata

Shehin malami Isa Ali Pantami yace bai taba tunanin zama minista ba a rayuwarsa, kamar yadda malamin ya fada cewa, yayi imanin duk abinda Allah madaukakin Sarki ya kaddarawa bawansa sai yasameshi, saboda ban taba kamun kafa a wajen wani domin samun mukamin minista ba.

#SenIbrahimShekarauMedia

An raka wakilin masarautar Takai domin fara aiki.

Sarkin Rano Dr Tafida Abubakar Ila Autan Bawo ya nada wakilai a Kura, Garun Malam, Bebeji da Takai a sakamakon dakatar da hakiman wadannan yankuna da akayi a baya-bayannan.

Gashinan inda aka raka wakilin Takai a wannan rana ta Laraba 31/7/2019. Allah yayi riko da hannayesu, ya rabasu da yan gangan da ganganci, ya basu ikon sauke nauyin alummar su.

SAKON TAYA MURNA GA SENATOR KANO CENTRAL DR. IBRAHIM SHEKARAU DAGA #S4S TA JIHA.

A madadin jagororin #S4S na Jiha Alh. Salisu Indabawa da Alh. Haruna Muhammad Gama (Garkuwar Sardauna) da shugabanninta na Jiha dana kananan hukumomi da sauran membobinta karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada muke amfani da wannan dama domin mika sakon taya murna ga jagorammu kuma Sanatan Kano ta tsakiya mai girma Sardaunan Kano Dr. Mallam Ibrahim Shekarau bisa nada shi da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan yayi domin jagorantar Committee of Establishment and Public Service.

Allah Ubangiji (S.W.A) yayi jagoranci ya sanya alheri yayi riko da hannayensa. Allah Ubangiji yasa a gama lafiya ya kuma kauda dukkan abin ki.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S
30/7/2019.

SHUGABANCIN KWAMITIN MAJALISAR DATTIJAI

Shugaban Majalisar dattijai na tarayyar Najeriya Sanata Dr Ahmed Lawn ya bayyana sunan Mallam Ibrahim Shekarau a matsayin shugaban kwamitin harkokin hukumomin gwamnati da dukkan ma’aikata na tarayya.

Sunan kwamitin: Establishment and Public Service.

An fadi wannan suna ne cikin sunayen da aka gabatar a yau da rana bayan kammala tantance ministocin kasar da sahalewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada su ba tare da wata tangarda ba.

Majalisar dattijai ta kafa kwamitoci guda 69.
Kwamitin da aka sanya amanarsa a hannun Sanata Ibrahim Shekarau shi ne yake da alhakin kula da tafiyar da duk hukumomin gwamnati da ma’aikatunsu da duk ma’aikatan gwamnatin tarayya. Babban kwamiti ne komai da ruwanka, wanda zai lura da kafa duk wata sabuwar hukuma da sake fasalin tsohuwa.

A wajen saka Sanata Ibrahim Shekarau kan wannan jagoranci Majalisar dattijai ta yi la’akari da kwarewarsa da gogayyarsa da sanin makamar aikin harkar gwamnati da kuma amanarsa da zai rike ta ma’aikatan Najeriya a majalisa.

#SenIbrahimShekarauMedia

SAKON TA’AZIYYA DAGA #S4S TA JIHA.

A Madadin jagororin tafiyar #S4S da kuma shugabanninta na jiha karkashin jagorancin Abdullahi Ahmad Tadada muke amfani da wannan dama domin yiwa daya daga cikin shugabannninta na jiha mataimakin Secretary wato Na’Allah Raheemeeb bisa rasuwar yayarsa wadda Allah ya yiwa rasuwa. Da fatan Allah ubangiji (S.W.A) ya jikanta ya gafarta mata ya yafe mata kurakuranta ya haskaka kabarinta ya sadata da Manzon tsira (S.A.W). Allah ya bawa iyalanta da yan’uwanta hakurin wannan rashi.

Allah ya jikan dukkannin iyayenmu da sauran yan’uwa musulmi da suka rigamu gidan gaskiya tin daga lokacin Annabi Adamu (A.S) zuwa yau din nan. Idan tamu tazo yasa mu cika da kalmar shahada.

Announcer:-

Basheer Basardaune,
State P.R.O #S4S,
27/7/2019.

Sakon Jummah Daga Sen Ibrahim Shekarau Media

Ya Allah! Ka lullubemu da rahamarKa, Ka bamu nasara da kariya da tsarkin zuciya daga duhun zargin da bamu da tabbas.

Ya Mai rahama akan bayinSa da suka bada gaskiya.

Barkanmu da wannan rana ta Jummah.

#SenIbrahimShekarauMedia

KANO TA TSAKIYA: LAYA TAYI KYAN RUFI

Daga Umar Faruq Muhammad:

Kasa da watanni biyu da fara zaman Majalisa ta 9 alamu na nuna Yan tsakiyar Kano sunyi nasarar tura wakili.

A iya zaman da Majalisar Dattawa tayi anji amon Sabon Sanata wajen bada gudunmuwa kan batutuwan da kai tsaye talakawan Nijeriya zasu amfana.

Wani abu da ya burge ni da wannan wakilci na Sardauna shine ya yarda shi dan aiken Jama’ar Kano ta tsakiya ne ba kansa yaje wakilta ba.

Idan ka Kalli Hoton da Sanata Shekarau ke zaune a office zakaga takardu a gaban sa, dayawan Takardun Al’umma ne suka rubuta shawarwari game da bukatun wadanda yake wakilta, daga ciki akwai wacce wani Mallami na yabani nikuma na mikata ga Babban Sakataren Sanata Sardauna Alh. Abdullahi L. Yola.

Wannan ya tabbatar mana cewa Sardaunan Kano zaiyi wakilcin da yasha bamban dana wancanen ka.

AlhamdulilLah, Kanawan tsakiya bamuyi asarar kuri’a ba.

#SenIbrahimShekarauMedia

Majalisar Wakilai tayi kira da a sake kidaya jama’ar Najeriya

Majalisar wakilai ta Najeriya tayi kira ga hukumar kidaya su hanzarta sake kidaya al’ummar Najeriya.

Wannan ya biyo bayan kudirin da dan Majalisar Wakilai na Tarayya Afolabi Olalekan (APC, Osun) ya gabatar domin sanin yawan al’ummar, duba da talaucin dake addabar kasar kuma ga yawan jama’a na karuwa, kamar yadda yace, Najeriya ce kasa ta 152 cikin kasashen duniya 188 kamar yadda hukumar (UNHI) ta bayyana wajen talauci 2019.

Itama takwararta, hukumar (UNDP) tayi hasashen nan da shekara ta 2050 yawan jama’ar ta Najeriya zai iya kaiwa miliyan dari hudu 400m.

Dan majalisar tarayya Olalekan yace, a yanzu haka dan Najeriya yana rayuwa ne akan kudin da bai wuce $1.90 a kowace rana ba, don haka yayi kira ga Gwamnatin Tarayya ta hanzarta kididdige yawan al’ummar ta akai-akai domin shawo kan wannan matsala.

##SenIbrahimShekarauMedia

SANATA SHEKARAU YA NEMI BAHASI KAN AMFANI DA HARSUNAN GIDA

A karo na biyu cikin sati guda a tsayawarsa gaban Majalisar dattijai, Sanatan Kano ta Tsakiya Mallam Ibrahim Shekarau, ya nemi tsohon ministan kimiyya da fasaha, Cif Ogbonnaya Onu, ya yi bayani kan matakin da zai dauka domin amfani da harsunan gida wajen bada ilmi na kimiyya da fasaha Idan an nada shi minista.

Mallam Shekarau ya yi wannan tambayar ne yau gab da la’asar a lokacin da Majalisar dattijai take aikin tantance sunayen ministocin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya aike mata. Ogbonnaya Onu wanda shi ne na shida a jerin ya bayyana a yau.

Sanata Shekarau ya ce, Idan har ana son bada ilmi mai fa’ida da ratsa kwakwalwa sai an rika amfani da harsunan gida a wajen koyar da darussan kimiyya a makarantu tun daga tushe irin yadda ake yi a Faransa da Jamus da Italiya da Sin da kasashen Larabawa. Anan ne ya nemi jin yaya Onu zai yi a kan wannan shiri.

A lokacin da yake amsa tambayoyin sanatoci Onu ya ce wannan abu ne mai muhimmancin gaske, akwai kwamiti a matakin kasa na ministoci da suka shafi ma’aikatar ilimi da ma’aikatar Science, Technology and Innovation. Ya ce, dorawa kawai za a yi.

A Talatar makon jiya ma a zaman Majalisar dattijai Sanata Shekarau ya mike tsaye domin goyon bayan moshin da dan Majalisar dattijai Sanata Eyakenyi Akon Etim (PDP A/ Ibom South) da takwarorinsa su 34 ya gabatar. Sanata Shekarau ya yi tsokaci akan wajabtawa malaman makaranta amfani da kwamfuta.

#SenIbrahimShekarauMedia

Ba zamu yadda da janye tallafin mai ba – Majalisar Dattawa

Majalisar dattawan Najeriya sunce, ba zasu amince da janye tallafin man-fetir ba, saboda janyewar zata kara tsadar man da kuma jefa al’umma cikin matsananciyar wahala

Maimakon haka, majalisar zata bincika kamfanonin da aka basu lasisin gina matatun man-fetir har guda arba’in da uku (43) amma basu fara aiki ba, su gaggauta fara aikin kamar yadda Aliko Dangote ya fara.

#SenIbrahimShekarauMedia

Ba zamu tantance masu laifukan cin hanci da rashawa ba

Majalisar dattawa tace ba zata tantance sunayen ministocin da shugaba Buhari ya aika mata ba, matukar muka samesu da laifukan cin hanci da rashawa.

#SenIbrahimShekarauMedia

Majalisar dattawa ta Najeriya ta dakatar da tafiya hutu

Sakamakon sunayen ministoci da fadar shugaban kasa Buhari ta tura wa majalisar dattawa a wannan rana ta Talata 23/7/2019 domin tantancewa.

Majalisar ta dakatar da tafiya hutu da zatayi 26/7/2019 domin hanzarta dubawa da fara tantance mutanen da shugaban kasa ya tura domin su zama ministoci.

#SenIbrahimShekarauMedia

BAMBANCIN A BAYYANE YAKE

Daga Jibril Muhammad Na Tara

Waya taba ganin masu taimakawa Kwankwaso a Majalisa ?

Ga masu taimakawa Sardaunan Kano tuni kowa ya kama aiki.

#SenIbrahimShekarauMedia

Sen Ibrahim Shekarau Yakai Ziyara Hukumomin TETFUND da NUC

Litinin 22/7/2019

Daga Jibrin Muhammad Na Tara:

Mai Girma Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano a National University Commission (NUC)

Sen. Malam Dr. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano ya kaiwa Sakataren NUC Prof. Abubakar Adamu da Sakataren TETFUND Prof Solomon Elias Bogoro da Proprietar BAZE University Abuja Dr Datti Baba Ahmad Ziyara sun tattauna batutuwa masu matukar mahimmanci akan cigaban Ilimi a kasa .
Allah ya taimaki Tsohon Malamin Makaranta Tsohon Ministan Ilimi

#SenIbrahimShekarauMedia

Sardaunan Kano Mutumin Kirki

Saboda kyan halayensa da dabi’unsa yasa a majalisar dattawan ma rububinsa a keyi. Shi yasa muke da yakinin da izinin Allah (S.W.T) zai baka mulkin kasar nan baba Sardauna. Dan haka ne hausawa ke cewa halin mutum jarinsa.

Sako Daga #S4S,

#SenIbrahimShekarauMedia

Design a site like this with WordPress.com
Get started