Kungiyar Benue youth Initiative sun karrama zabbaben gwamnan kano Karo 2 Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon gwamna Kano karo 2 kuma zabbaben sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau yanzu haka a fadar mundubawa.
Category Archives: Uncategorized
Jihar Kano Ta Sauke Manyan Sakatarori A Kowacce Ma’aikatar Jihar
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje a cigaba da tsaftace ayyukan gwamnati da kara karkashin aikin da ma’aikata, ta sauke dukkanin manyan sakatarori na kowace ma’aikata (Perm Sec) Wannan ya fito daga bakin shugaban ma’aikata na Jihar Kano Auwalu Na’iya, inda zasu mika ragamar aiki ga babban darakta na kowacce ma’aikata dagaContinue reading “Jihar Kano Ta Sauke Manyan Sakatarori A Kowacce Ma’aikatar Jihar”
Labarai Daga Fadar Mundubawa
Maigirma gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tsohon Mataimakin gwamna Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da sauran jami’an gwamnati sun ziyarci Maigirma Zababben sanatan Kano ta tsakiya Distinguish Senator Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano a fadarsa ta mundubawa yanzu haka.
Sanata Ibrahim Shekarau Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Hada Hannu Da Buhari A Cigar Da Najeriya Gaba
Zababben Sanatan Kano ta tsakiya a zaben da ya gabata Sen. Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano ya bukaci wadanda suka fadi zabe su ajiye banbance-banbancensu su hada hannau da shugaba Buhari domin cigar da Najeriya gaba. Sanata Ibrahim Shekarau yace, duk da kalubale da soke-soke da gwamnatin Buhari take samu, wannan bai hana samar daContinue reading “Sanata Ibrahim Shekarau Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Hada Hannu Da Buhari A Cigar Da Najeriya Gaba”
Shedar Karatun HND Da Bsc A Hukumar Ma’aikatan Jihar Kano Daidai Take
Maigirma gwamna Abdullahi Umar Ganduje a bikin zagayowar ranar ma’aikata ta 2019 yace, daga yanzu babu banbanci tsakanin masu rike da takarar shedar karatu ta HND da Bsc a kowane fannin aiki a Jihar Kano. Ko shakka babu, kwakwalwar Maigirma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje nesa take da sauran, ma’aikatan Jihar Kano suna godiya.
MA’AIKATA SUNE GINSHIKIN GUDANAR DA MULKI
Gaisuwa Ta Musamman Gareku Ma’aikata Yau rana ce da aka ware domin duk jinsin ma’aikata. Rana ce ta duniya, wacce manufarta shi ne a nuna muhimmancin gudunmawa da ma’aikata suke bayarwa wajen gudanar da mulki don inganta rayuwar al’umma Ina taya ku murnar shagulgulan zagayowar wannan rana, wacce ta zo daidai da lokacin da majalisarContinue reading “MA’AIKATA SUNE GINSHIKIN GUDANAR DA MULKI”
Kano Zata Hada Hannu Da Kasar Chaina
Gwamnatin Kano karkashin maigirma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sa hannu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da Kasar Chaina inda za ta shigo da manyan motocin zirga-zirga a cikin gari. Wannan ya biyo bayan yadda gwamnatin ke kokarin fito da wata sabuwar hanya ta saukakawa al’ummah a bangaren sufuri, inda a rashin farko zaContinue reading “Kano Zata Hada Hannu Da Kasar Chaina”
Nassarawa da Dala Kuna Birgeni
ALHAMDULILLAH Ina Godiya ga Dan majalisarmu Na Tarayya Hon Nasiru Ali Ahmad bisa Gwangwajemu da Sababbin Mashina a karkashin Jagoranchin Director General dinsa Majidadi Rabiu Baba Nabegu. DG yace kowa sai ya amfana, Jamilu Away Mai Jakai da Nura Kabaransi Gawuna da Jibril Muhammad Na Tara suna cikin Mutum 50 wadanda suka rabauta da MashinaContinue reading “Nassarawa da Dala Kuna Birgeni”
AN SAKA SHEKARAU CIKIN MASU YI WA ZABABBUN GWAMNONI BITA
Kungiyar gwamnonin Najeriya wato ‘Nigeria Governors Forum’ NGF ta shirya taron bita na kwana hudu, daga yau zuwa Laraba, wanda aka tsarawa sabbin gwamnonin da suka ci zabe da wadanda zasu maimaita a Abuja na duk jam’iyyun APC da PDP da APGA. Zababben sanata na Kano ta tsakiya, kuma tsohon gwamna Mallam Ibrahim Shekarau yanaContinue reading “AN SAKA SHEKARAU CIKIN MASU YI WA ZABABBUN GWAMNONI BITA”
ASALIN GURGUNTA ILIMIN JIHAR KANO
Lokacin ina Brigade Special primary school munada Mallamai Kwararru wadanda ba ‘Yan asalin Kano ba, bazan taba mantawa da Form Mistress din mu a Primary 4 ba Malama Mulikat. A Secondary school dinmu ta GSSS Stadium ma muna da Mallamai Yarabawa, Inyamurai da Kabilun Arewa, ina Alfahari da wani Banufen Mallamin mu mai suna MallamContinue reading “ASALIN GURGUNTA ILIMIN JIHAR KANO”
Dokar Hana Zirga-Zirga A Kajuru Jihar Kaduna Yanzu-Yanzu
Sakamakon abin da ya faru a Kasuwar Magani, Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da kakaba dokar hana zirga-zirga awa 24 a Karamar Hukumar Kajuru, har sai abin da hali ya yi
Sannu Da Zuwa Uban Abba
Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya sauka filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake babban birnin taraiya Abuja bayan dawowar sa daga kasa mai tsarki inda ya gabatar da ibadar sa ta Umrah. Gwamna ya samu tarbar Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sanata Barau Jibrin da kuma wasu daga cikinContinue reading “Sannu Da Zuwa Uban Abba”
Nine Na Jawo Rabi’u Kwankwaso Cikin Harkokin Siyasa
Maigirma Kwamishinan raya karkara da birane Musa Iliyasu Kwankwaso yayi ikirarin cewa, shine ya jawo tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso cikin harkokin siyasa. Musa iliyasu Kwankwaso yace, a siyasance ni shugabansa ne, nine kuma na bashi karfin gwuiwa ya tsaya takarar dan majalisar wakilai ta tarayya a lokacin yana aiki a hukumar ruwan sha daContinue reading “Nine Na Jawo Rabi’u Kwankwaso Cikin Harkokin Siyasa”
Kwankwasiyya Ko Abba Zaman Gida?
Wata majiya mai tushe ta tabbatar mana cewa, madugun kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya fara korafi akan yadda hulunan Abba Zaman Gida suke yawo a gari ba tare da alamar kwankwasiyya ba. Nan take madugun yace babu kalmar kwankwasiyya a jikin hulunan, wannan yana nuna an dauko hanyar shafe kalmar ta kwankwasiyya a doron kasa,Continue reading “Kwankwasiyya Ko Abba Zaman Gida?”
KWANKWASIYYA SARAKAN SON ZUCIYA!
Daga Umar Faruq Muhammad Yau duk inda ka karada a social media zakaga Yan Kwankwasiyya suna ta murna da yada Labaran cewa Kotu tace a karbe kujerar Kawu Sumaila ofr saboda bai shiga Primary election ba. Yada wannan labarin bai nuna komai ba sai cikakkiyar son zuciyar Yan Kwankwasiyya. A 2015 kowa yasan Kwankwaso takardarContinue reading “KWANKWASIYYA SARAKAN SON ZUCIYA!”
PDP Ta Janye Zanga-Zanga A Kano
Jam’iyyar PDP ta kasa reshen Jihar Kano ta janye zanga-zanga lumana da tayi shirin gudanarwa Alhamis 18/4/2019 Wannan zanga-zanga, kamar yadda Jam’iyyar tace, ta shirya ta ne domin nuna kyama ga yadda jami’an tsaro suke kamawa da kullewa da musgunawa harma da barazana da rayukan magoya bayanta ba tare da aikata wani laifi ba. WannanContinue reading “PDP Ta Janye Zanga-Zanga A Kano”
Jam’iyyar APC Ta Zabi Sanata Ahmed Lawan Shine Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya bayyana cewa duk da yake Sanata Ali Ndume dan uwan sa ne, dan Jihar sa, ba zai yi wa uwar jam’iyyar APC tawaye ba. Jam’iyyar APC ta zabi Sanata Ahmed Lawan shi ne zai zama shugaban majalisar dattawa, yayin da Sanata Ndume ya ce bai yarda ba, zai tsayaContinue reading “Jam’iyyar APC Ta Zabi Sanata Ahmed Lawan Shine Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa.”
KUN SAN WAYE GEORGE WASH FINGER DA IYABO OLADINI KASALI
Bayan mun fadi a zaben 2011 dandanan aka fara bamu kwarin gwiwar cewa muna zuwa kotu za’a kwace kujerar gwamna daga hannun kwankwaso a bawa malam saluhu Cikin bayanin kwarin gwiwar ne har SHEHU ISA direba yace mun dauko bature mai suna GEORGE WASH FINGER daga America wanda zaiyi aikin gano mutanen da suka yiContinue reading “KUN SAN WAYE GEORGE WASH FINGER DA IYABO OLADINI KASALI”
Justice Mamman Nasir Ya Amsa Kira
Allah yayi wa Galadiman Katsina kuma tsohon ministan shari’a na zamanin Sardauna, Justice Mamman Nasir rasuwa
BAYAN SUN GANA DA BABA
Sai Gabriel Olonisaki Chief Of Defence Staff yake shaidawa yan jarida cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarcesu dasu aikata dukkan wani kalar rashin tausayin da suke dashi a cikin aikin soja ga Barayin dake kashe mutane tare da sacewa a jihar Zamfara…. Tsantsar rashin mutumci nake son ku aikata musu, ko kadan kada ku sauraraContinue reading “BAYAN SUN GANA DA BABA”
Sanata Lawan Da Ndume: Wa Za A Kai Kasa?
Sanata Ahmed Lawan da Ali Ndume dai ba sabbin-yanka-raken shiga Majalisar Dattawa ba ne. Sun jima ana gogawa da su. A baya za a iya cewa ‘yan gida daya ne, wato Jihar Barno. Amma tun bayan kirkiro Jihar Yobe, sai Lawan ya raba hanya da Barno. Ali Ndume ya kuma a Majalisar Tarayya ya naContinue reading “Sanata Lawan Da Ndume: Wa Za A Kai Kasa?”
Sauka Lafiya Maganin Kukanmu
Mai Girma Zababben Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau CON Sardaunan Kano tare da Tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya Lado a Protocol Lounge Aminu Kano Airport. Allah ya kai ku lafiya.
KOTU TA YI WA SANATA SHEKARAU DA AMINU WALI DA INJINIYA MANSUR IZININ TAFIYA UMARA
Kotun tarayya ta mai shari’a Lewis Allogoa da ke sauraron karar da EFCC ta shigar da zababben sanata na Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau da Ambasada Aminu Wali da Injiniya Mansur Ahmed,ta bada izinin ya je ya yi ibadar Umara a cikin wannan watan Ramadana in Allah ya kaimu. A yau a zaman da akaContinue reading “KOTU TA YI WA SANATA SHEKARAU DA AMINU WALI DA INJINIYA MANSUR IZININ TAFIYA UMARA”
Ina Gaskiyar Wannan Labari Na AlkalaminSantsi?
Munci karo da wani rubutu na AlkalaminSantsi inda yake karyata wani rubutu da yake yawo da sunan Sanata Ibrahim Shekarau Mun sami wannan rubutu daga wani shafi na twitter mai dauke da Official TL of Ibrahim Shekarau, ganin wannan labari akan wancan account yabaka karfin gwuiwa cewa daga bakin Sanata Ibrahim Shekarau yake. Matukar baContinue reading “Ina Gaskiyar Wannan Labari Na AlkalaminSantsi?”
Wai Wannan Wasu Su Ke Bi
Wai wannan wasu su ke bi a matsayin jagora, mutuminda yace da mahaifinsa ‘WAWA”. Mutanenda Allah (S.W.A) ya ambata a cikin alkur’ani mai girma. Wallahi dana bishi a matsayin jagora gwara ma nabi wanda ba musulmi ba a matsayin jagora muddin ba zai hana ni addini na ba, dama shi na san ba musulmi baContinue reading “Wai Wannan Wasu Su Ke Bi”
MUNA BUKATAR MAJALISAR DATTIJAI ABIN ALFAHARIN KOWA
A satin da ya gabata takwarorina tsaffi da sabbin sanatoci zababbu, sun ziyarce ni har gida a Kano Wadanda suka ziyarce ni sune: Sanata Danladi Sankara APC Jigawa Sanata Bello Mandiya APC Katsina Sanata Barau I Jibrin APC Kano Sanata Yahaya Abdullahi APC Kebbi Sanata Solomon Adeola APC Lagos Sanata Lekan Mustapha.APC Ogun Sanata DegiContinue reading “MUNA BUKATAR MAJALISAR DATTIJAI ABIN ALFAHARIN KOWA”
Zaben Kano: Mun Gama Shirin Kare Kanmu A Kotu, Cewar INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta reshen Jahar Kano ta kammala shiryawa tsaf don kare kanta a kotu da zarar kotun ta nemi su a kan wani korafi ko wata kara da wani dan takara ko wata jam’iyya ta kai su a zabubbukan Kano da a ka gabatar na 2019. Bayanin hakan ya fito ne dagaContinue reading “Zaben Kano: Mun Gama Shirin Kare Kanmu A Kotu, Cewar INEC”
DAN ADAM SARKIN MANTUWA!
👉 A ranar da aka rantsar da Mal. Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Gwamna a 2003 ya shelantawa Kanawa cewa duk wata Daliba Mace Karatun ta Kyauta ne a Makarantun Jihar Kano, hakanan duk Yara Maza dake Karatu a fannin Kimiya da Fasaha (Science and Technology) suma Gwamnatin ta dauke musu biyan Kudin Makaranta. 2011 KwankwasoContinue reading “DAN ADAM SARKIN MANTUWA!”
Labari da dumi-dumi
Yayin da mako daya ya rage hukumar da ke shirya jarabawar kammala Sakandare ta kasa wato NECO ta rufe karbar kudin rijistan dalibai da za su rubuta jarabawan a wannan shekara ta 2019, gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ba da umarnin fitar da kudi domin biya wa kafatanin daliban jihar da keContinue reading “Labari da dumi-dumi”
NEXT LEVEL YAN PDP NA GASKIYA
Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR Khadimul Islam ya karbi bakuncin ‘yan PDP tsagin Amb Aminu Bashir wali, Sen Bello Hayatu, Hon Salisu Buhari da Alh Yahaya Bagobiri a dakin taro na Africa dake fadar Gwamnatin Kano sunje fadar ne dan taya Gwamna murna da jaddada mubayi’arsu ga Gwamna a yayin maida jawabi GwamnaContinue reading “NEXT LEVEL YAN PDP NA GASKIYA”

You must be logged in to post a comment.