Gaskiyar magana dole a yabawa Hon Nasiru Ali Ahmad domin shine na farko daya saukewa masu tiri-tiri da takarar sa kabakin arziki Musa Dambele Nazer Danhalak da sauran yan gwagwarmaya ina taya murna. DG Rabi’u Baba Nabegu kaima Allah ya saka da alkhairi domin wannan duk kokarin ka ne.
Category Archives: Uncategorized
Najeriya Ta Dakatar Da Hakar Gwal A Zamfara
Gwamnatin Najeyiya ta dakatar da ‘yan kasashen waje masu hakar gwal a Jihar Zamfara da kewayen ta. Kamar yadda mukaddashin babban sifetan ‘yan sanda na kasar Mohammed Adamu ya bayyana cewa anyi haka ne domin a sami damar dakile masu tada kayar baya tare da yin garkuwa da mutane a Jihar.
Daurin Aure Cikin Hotuna
A wannan rana ta Lahadi 7/4/2019 daya daga cikin ‘yan gwagwarmaya a fadar mundubawa Mallam Haroun Shekaran Gama ya sake angwancewa kari akan angwancewarsa ta fari, yanzu haka Mallam Haroun Shekaran Gama ya zarce sa’ansa. Muna addu’a Allah yasa albarka cikin iyalinsa ya bashi ikon sauke nauyin da ya karu akansa na yin adalci aContinue reading “Daurin Aure Cikin Hotuna”
ZAMU SAKA SHEKARAU A MANYAN DATTIJAN MAJALISARMU
Inji Sanata Ahmed Lawan Dan takarar shugabancin majalisar dattijai Sanata Ahmed Lawan (APC-Yobe) ya bayyana cewa akwai wasu zababbun mutane da a koda yaushe majalisar dattijai ta kasa ta ke kaddara su a matsayin manyan dattijanta. Ya ce, zababben Sanata na Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau, zai kasance daya daga cikinsu a wannan majalisa taContinue reading “ZAMU SAKA SHEKARAU A MANYAN DATTIJAN MAJALISARMU”
Mutum Bashi Da Tabbas
Nasan wani bawan Allah wanda yake zaune bashi da aikin yi,hakan ne yasa kullum matar sa sai ta fita unguwa domin ta samu abinda zata ci idan ta fita sai dare take dawowa. Shi kuma yakan je majalissar abokai domin ya samu abinda zai kai bakin sa Ana haka ne aka fadawa wani dan siyasaContinue reading “Mutum Bashi Da Tabbas”
Masu Tafiya A Hanyar Hadejia Wajen ‘Yan Kaba Ayi Hattara
Wani ganganci sai bakin mutum Yayin da wata trailer dauke da mai tafadi mai yana zuba a kan hadeja road kusa da Benni international school. Madadin a nesanceta amma al’ummar mu sai ma kara kusantarta suke. Allah ya kyauta ya kiyaye tashin wuta. Daga Abubakar Datti Dakata
Kamar Yadda Aka Saba Kowace Jummah
Mai Girma Zababben Sanatan Kano ta Tsakiya Dr Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano Ya halarci Sallar Juma’ah a Masallachin Yandutse dake Bompai anyi Zaman Fada kamar inda aka Saba. Jibril Muhammad Na Tara
Tayaya Mai Mulki Zai Gane Yayi Kuskure?
Sau da dama zaka sha mamaki idan kaga yadda ake mu’amalantar masu mulki. Sai kayi mamaki tayaya mai mulki zai gane yayi kuskure, alhali mafiya yawancin mutane in suka je wajensa basa gaya masa hakikanin al’amari. Hatta wasu Malamai da suke sukar shugabanni kan yadda suke tafiyar da Gwamnati, idan suka samu damar yin idoContinue reading “Tayaya Mai Mulki Zai Gane Yayi Kuskure?”
TIRKA-TIRKAR SIYASAR KUMBOTSO !
Banso cewa komai ba amma dai lamarin yakai matsayin da zamu iya magana kasancewar mu Ahalil zikiri akan wannan batu, abu mafi muni a cikin wannan magana shine mafi yawancin masu magana akai basu da wani tabbaci akan lamarin iya kacinsu bazai wuce samun bayani daga wani bangare ko dai masu suka ko kuma masuContinue reading “TIRKA-TIRKAR SIYASAR KUMBOTSO !”
Tafaru Ta Kare
Ta Faru Ta Kare, Ranar Da Ake Jira Domin Banbace Makaryata Da Masu Gaskiya Tazo. Dr Abdullahi Umar Ganduje Da Dr Nasiru Yusuf Gawuna Da Zababun Yan Majalisar Dokoki Na Kano Na Jam’iyar APC. Sun Karbi Shaidar Cin Zaben Su Daga Wajen Hukumar Zabe Ta INEC.Allah Ya Sa A Fara Lafiya, Yasa A Gama lafiya.Continue reading “Tafaru Ta Kare”
KULLUKUM RA’IN…
Daga Umar Faruq Muhammad. Daga 2015 har zuwa 2023 Shugaba Muhammadu Buhari ne babban wanda za’a yiwa tambaya akan al’amuran dasuka faru a Nijeriya. PMB shine ‘First citizen’ a Nijeriya, don haka shine wanda yafi kowa cancantar daukar nauyin abubuwan dake faruwa a Nijeriya. Shin Shugaba PMB yana kwana da abubuwan dake faruwa a ZamfaraContinue reading “KULLUKUM RA’IN…”
Allura Zata Tono Garma
Kalubalantar nasarar da Maigirma Gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben da ya gabata wanda PDP ke shirin yi a kotu, shine kuma zai tozarta Jam’iyyar ta PDP a Jihar Kano baki daya. Domin allura zata tono garma, masamman kujerun majalisar Jiha da PDP suka samu za’a bankado kullin da ke cikin wannanContinue reading “Allura Zata Tono Garma”
TUN DAGA JAHAR GOMBE YAZO FADAR MUNDUBAWA…
Wannan Bawan Allah dake hannun hagun Mai girma Sardaunan Kano, wani Masoyinsa ne daga Jihar Gombe. Sunansa Ismail Garba lokaci bayan lokaci yakan taso yazo domin ya gaida Mai girma Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau. Haka idan wani abu na farin ciki yafaru da Sardaunan zai taso domin taya murna ga Sardaunan na Kano. YanzuContinue reading “TUN DAGA JAHAR GOMBE YAZO FADAR MUNDUBAWA…”
Bazan Yada Karya Ba
Nidai Banga Wanda Zaisani Na Yada Karya Ba Bayan Nasan Illar Haka Cikin Addini Na Daga Sani Kabir Kwankwasiyya Wani Matashi Dan Kwankwasiyya Yace Shi Ba Jahili Bane Dan Haka Baiga Wanda Zai sashi Yada Karya Ko Kage Dan Kare Manufarsa Ta Siyasa Ba Bayan Yasan Kabarin Mu Ba Daya Bane Matashin Yace An sasuContinue reading “Bazan Yada Karya Ba”
RATAYE NAJEEB AKAYI
Daga Kamal A Baba Mahaifin Najeeb. Bansan me nayi muku ba, kuka rataye wannan yaro najeeb Kamal A Baba an kashe shi har lahira. Bayan an tashe su daga Makaranta, naje na ɗauko su, da shi da “yan uwansa, Nauwar da Nabeel, na kawo su Gida, jiya Alhamis babu makarantar Islamiyya sai Najeeb yace AbbaContinue reading “RATAYE NAJEEB AKAYI”
IDAN NASAMI DAMA SAI NAYI RASHIN MUTUNCI!!
Daga: SANI ROGON AIKAWA DALA. (Kalaman wani yaro da naji da kunnena) Jiya Talata ina tsaye Daidai jakara Bola zan hau babur Din Adaidaita sahu, sai wani yazo saura mutum daya, amman Da wani yaro agaba yazauna gefen babur din hannunsa rike da kullun buhun Leda dakuma wani kwano, ban vata lokaciba na hau saiContinue reading “IDAN NASAMI DAMA SAI NAYI RASHIN MUTUNCI!!”
Adalci ‘Yan PDP
Daga El-Mansoor Yusha’u Kyauta PDP takama Sokoto anyi Adalci. PDP takama Bauchi anyi adalci. PDP takama adamawa anyi adalci. PDP takama Taraba Anyi adalci. PDP takama benue anyi Adalci. APC takama Kano Amma Anyi zalunci. To Anki Ayi Adalcin Duk Abinda zakuyi Kun dade Bakuyi ba Ganduje ne Gwamna Cikin yardar Allah.
Mun Shirya Tsaf!
Daga Baballe Kabiru Isyaku Mun shirya tsaf! Mu na da hujjoji kwarara da su ke tabbatar da cewa gwamna Ganduje shi ne ya lashe wannan zabe”. Wasu lauyoyi yan asalin Jahar Kano fiye da su dari uku [300] sun yi alkawarin kare gwamnan Jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a gaban kuliya kyauta ba tareContinue reading “Mun Shirya Tsaf!”
Ana Wata Ga Wata
Daga Hussaini Alhassan H.A A Gobe Alhamis 28/03/19 kotun daukaka Kara dake Kaduna zata fara sauraron daukaka Karar da PDP reshen jihar Kano tayi dangane da karar da Hon. Alh. Ibrahim Ali Amin Little ya shigar akan yadda aka fitar da Engr. Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP. A bayaContinue reading “Ana Wata Ga Wata”
YADDA DILLIN TAKANYI DILLIN HAKA MA DILKIN TA KANYI DILLIN
Daga Haroun Shekaran Gama Wallahi da na saurari maganganun kwankwaso sai na tausaya masa bisa yadda naji muryarsa tana rawa da shasshekar kuka bisa yadda kokawa da cewar wai an zalunce shi. Ina gama saurararshi sai na fashe da dariya,nace mai guma cuta an guma masa duba da irin zalunci da rashin imanin da yaContinue reading “YADDA DILLIN TAKANYI DILLIN HAKA MA DILKIN TA KANYI DILLIN”
MASAURATAR KANO TA SAMU MATSALA KENAN ??
Bayan bayyan sakamakon zaben Gwamna a Jahar Kano, Masoya da Magoya bayan Gwamna Ganduje da jam’iyyar APC, sunje har gidan gwamnati domin murnar lashe zabe. Ana tsaka da murna Hoton SARKIN KANO dake like tare da na Gwamna a jikin bangon babban dakin TARO na gidan gwamnati (Coronation Hall), ya hadu da wasu fusatattun MatasaContinue reading “MASAURATAR KANO TA SAMU MATSALA KENAN ??”
Sakamakon Karshe Na Gwamnan Kano
ZAGAYEN FARKO RANAR 9 MARCH 2019 PDP Abba K Yusuf 1,014, 474 APC Abdullahi U Ganduje 987, 819 ZAGAYE NA BIYU RANAR 23 MARCH 2019 APC Abdullahi Ganduje 45, 876 PDP Abba K Yusuf 10, 239 JUMLAR SAKAMAKON ZABUKAN APC 1,033,695 PDP 1,024,738 BANBANCI APC da PDP 8,982
Zaben Cike Gurbi A Kano A Mahangar Yan Sanda
DIG Micheal Ogbizi a hirarsa da ya yi da gidan Talabijin na Channels yau 23 ga Watan Maris, 2019 da karfe 3:27 zuwa 3:36 na yamma. Ya ce “A mazabar Gama (karamar hukumar Nassarawa) jama’a sun fito da yawan gaske wajen yin wannan zabe. Kuma an yi zabe cikin kwanciyar hankali.” “A wasu wurare kadanContinue reading “Zaben Cike Gurbi A Kano A Mahangar Yan Sanda”
Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Koka
Mazugal A Karamar Hukumar Dala
Ya isa shaida cewa, zaben da ake sake maimatawa yau a Jihar Kano yana tafiya lami-lafiya. Mazugal ta Karamar Hukumar Dala ba’a barsu a baya ba wajen fitowa da kada kuri’unsu. Allah ya sa a gama lafiya kamar yadda aka fara lafiya
Belli Ta Karamar Hukumar Rogo
Rashin kammaluwar zabe yau zai kammala a zaben da ake sake fafatawa a wasu akwatuna dake Belli ta Karamar Hukumar Rogo. Masu zabe sunyi fitar kwari domin zabawa kansu abinda ya dace, kuma wannan ya isa shaida cewa, ana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
GAMA Cikin Karamar Hukumar Nassarawa A Yau
Daga dukkanin alamu, komai yana tafiya daidai kuma cikin kwanciyar hankali a mazabar Gama. Masu jefa kuri’a sun fito suna sauke nauyin da ya doru a kansu. Daga yanzu an shiga “MATAKI NA GABA” a Jihar Kano
UMARNIN AJIYE JAR HULA: Da walakin Goro a miya
Daga Umar Faruq Muhammad Kowa yasan yadda Kwankwaso yabawa Jar hula Muhimmanci hatta sallar Juma’ah da Eid baya halartar su da wata hula ba Ja ba. Lokacin da za’ayi zaben Gaya da Garko Kwankwaso ya Umarci mabiyan sa na 44 LGs sunje sun mamaye tashoshin Zabe da JAJAYEN HULUNA, suka hana kowa dangwala kuri’a saiContinue reading “UMARNIN AJIYE JAR HULA: Da walakin Goro a miya”
Abba Zaman Gida
Daga Na’Allah Raheemeeb
Ali Nuhu: ‘Abin da ya sa na shiga harkokin siyasa gadan-gadan’
Shahararren dan wasan Hausa Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa ba sabon abu ne ‘yan fim su shiga harkokin siyasa ba, kamar yadda yanzu ‘yan wasan Hausa suke yi. Dan wasan ya bayyana mana hakan ne a wata hirar musamman da muka yi da shi a Kano ranar Laraba. Ya ce an saba ganinContinue reading “Ali Nuhu: ‘Abin da ya sa na shiga harkokin siyasa gadan-gadan’”

You must be logged in to post a comment.